You are currently viewing Ma’anar Sana’a  da kuma Amfaninta

Ma’anar Sana’a da kuma Amfaninta

Sana’a wani abu ne wanda dan adam ya dade yana yi a tsawon rayuwarsa don samun abunda zai iya dogara da shi, a wannan post din zaniyi bayani akan mi ake nufi sana’a, ma’anar sana’a da kuma amfanin sana’a,  da kuma irin rawar da sana’oi suke takawa a rayuwar dan adam.

Ma’anar sana’a?

Ma'anar Sana'a

Sana’a tana nufin iya wasu abubuwa wanda zasu taka rawa a rayuwar wasu ta yadda shi me yin abun zai karu da su ta hanyar amsar kudi.

Kuma tana nufin samun ilimin yadda ake hada abu ko kuma kirkira abu ta yadda za’a saida mutane masu bukatara abun kamar iya kosai a ringa saida shi misali.

Misalin sana’a shine kamar mai sa’anar kafinta ko mai walda da sauransu wannan duka misalin sana’oi ne wanda ake ake yi.

To a yadda zamani yake yawan canzawa sana’a ta rabu zuwa gida biyu akwai ta gargajiya akwai kuma ta zamani wadda duka mutane suke yi.

Rbe-Reben sana’a

Sana’a ta dai rabu zuwa gida biyu ne akwai sana’oin gargiya akwai kuma sana’oin zamani 

Sana’oin gargajiya

Wadannan sana’oin sun shafi fannin sana’oin da hausawa suke yi tun kafin zuwan zamani wanada aka gada daga kaka da kakanni.

Kuma wadannan irin sana’oin sun danganta akwa sana’oin m,ata wanda mata suke yi kawai akwai kuma sana’oin maza.  yawancinsu na hannu ne.

Sna’oin gargajiya mafi yawa daga cikin su har yanzu ba’a bar yin wasu ba saboda mahimmancinsu a rayuwar dan adam

misalan sana’oin gargajiya sun hada gasu kamara haka:

  • Noma
  • kiwo
  • Rini
  • Jima
  • Saka da sauransu

Sanaoin Zamani

A dayan bangaren kuma akwai sana’oin zamani wanda suka sha banban da na gargajiya wanda muka yi bayani a sama su kuma ga abunda suke nufi.

Sana’oin zamani suna nufin sabbin sana’oi wanada zamani ya zo da su, musamman a irin wannan zamani da muke ciki na cigaban kimiyya da fasaha.

Sanadiyyar cigaba da aka samu na zamani yanzu har abun ya kai ga har a wayar hannu

ana yi wanda yawancinsu sun shafi samun kudi ne ta Hanyar amfani da Internet. to irin wadannan sana’oin da wadanda ba a online ake samun kudi da su ba duk su ake cema sana’oin zamani wanda a da cen kaka da kakanni basu yisu ba kwata kwata.

Misalan irin wadannan sana’aoin zamani ga su kamar haka a lissafe.

da sauran masu kama da suy.

Amfanin Sana’a

Amfanin sana'a

Samun abun yi yana Mahimmanci sosai ga rayuwar dan adam saboda rashin yin sana’a yana jawo abubuwa kala daban daban wanda ba’a so kuma.

Wasu daga cikin muhimman amfanin sana’a sun hada da

  • Dogaro da kai
  • Samun Natsuwa a Rayuwar
  • Samun Zaman Lafiya a zamantakewar aure
  • Kare mutum daga aikin ta’asa da kuma ashsha

Abubuwan da take Bukata kafin farawa

Akwai muhimman abubuwa daban daban da ake bukata kafin a fara ko wace irin sana’a kamar yadda shima kasuwanci haka yake a dayan bangaren.

Wasu daga cikin su sun hada da Iyawa abunda ake son ahyi kafin farawa, Jari sai kuma kyautata ita kamata sana’ar yadda zata samu karbuwa daga wajen mutane masu bukatar abun.

Yadda ake Bunkasa ta

Akwai hanyoyi da dama da ake bi wajen bunkasa amma ga wasu kadan daga cikinsu nana wanda zanyi bayaninsu domin saukin fahimta.

Zuba hannun jari

Abu na farko wanda yake taimakama yan kasuwa a harkokin su shine zuba hannun jari wanda idan mutane da yawa zasu hadu su zuba maka jari a ciukin kasuwancinka to zakaga indai ana sayen abun ana samun alheri.

Kuma yanayin riba yafi lunkawa kuma wannan shine ake cema samun dama wanda duk kusan  yawancin masu kudin duniya da kake ganinsu ta wannan hanyar ce Allah yake kara taimaka masu za’a zuba masu jari suyi ta kokarin rike ta da mahimmaci.

Idan aka zuba jari wanda ake cema share ana raba riba dai dai kwalgwadon kason kowa kuma irin wannan nauin kasuwancin yafi na mutum daya wanda zakaga yanayi shikadai tilo.

Bincike

Bincike kusan dole na ga wanda yake son ya cigaba da harkarsa ta kasuwanci sabaoda ta wannan hanyar ce zaka san wani abu ne sabo ya bullo kai kuma ina zaka fuskanta da shi a harkar.

Rashin hakan yana sa yan kasuwa kai har ma da manyan kamfanoni durkushew kamar bari in baka misali nokia na daya daga cikin abunda ya durkusar da su daga zama na daya a fannin waya shine da android tazo suka ki gyara harkar kasuwarsu.

Tafiya akan Buri

Idan kana yin kowane irin abu ne a duniya ba wai sai fannin neman kudi ba kawai ya kamata ka yi kokari kaga ka tabbatar da cewa kana tafiya akan wani buri wanda kake son cimmawa.

Ma’ana ya kasance kana son ka zama kaza wanda yake taimakama alumma ta fannin kasuwancin shi da abu kaza, to kaga a haka kamar ka samu fitla wadda take haska maka gabanka ne.

 

 

 

 

 

 

 

Author Profile

Ibrahim Buhari
Ibrahim Buhari