Skip to content
Home » Sanaoin Mata wanda zasu iya yi a Gida domin su samu kudi

Sanaoin Mata wanda zasu iya yi a Gida domin su samu kudi

Sanao’in mata suna da yawa wanda zaki ga mafi yawancin mata masu kokari sukan rike su domin su samu abun dogaro da kai, Domin ana so mace ko tana gida ta ringa yin sana’a domin hakan zai sa ta taimakawa mai gidanta da kuma yaranta.

ko a zamanin da mace na taka rawa a wajen sana’oin gargajiya balle yanzu da zamani ya zo hakan bai sauyaba dai.

To acikin wannan post din zamu duba wasu sana’oi kanana da mace zata iya yi amma kafin nan bari muga mi ake nufi da sana’a kanta?

Snaoin mata

Mi ake Nufi da Sana’a?

Sana’a tana nufin samun wata hanya da kudin shiga zasu rika zoma mutum ta yadda zata kama ma mashi ko kuma ta dauke mashi nauyin duk wasu harkokin rayuwarsa.

A dalilin zuwan cigaban kimiyya da fasaha abubuwa da yawa na rayuwar dan adam sun sauya musamman a karnin internet mutane suna samun kudi da Internet sosai.

Wanda a da babu yiwuwar hakan, duk da haka kuma sanadiyyar internet din dai ana amfani da ita don habbaka kasuwanci.

Dalilin faruwar hakan ya ta’allaka musamman dalilin zuwan Wayoyi irinsu android, wanda akwai sana’oi da yawa da ake yi da waya ita kanta.

Mi yakamata in duba kafin in fara Sana’a?

Kafin ki fara sana’a akwai muhimman abubuwan da yaka kamta ki duba wanda zaki fara tambayr kanki kmara haka:

 • Shin idan ina da miji zai banni ?
 • Suwnene cistomomi na?
 • Bayan ya barni mi zan fara saidawa wanda mutane suk so?
 • Ina karatu ko wani abu da zai hanani walwala a sana’ar?
 • Jarin nawa nike so?
 • Ya na tsara nan da wata daya, biyu ko ma shekara game da sana’ar

Bayan kin samu amsar kina iya karawa da wasu yadda kika ga ya dace domin kafin fara kowane kasuwanci ko kuma sana’a ana bukatar tunani.

To bari muga sana’oin da ko a gida kina iya yinsu kamar yadda taken post din ya nuna.

Sana’oin mata da zaki iya yi a Gida

Ga su kamar haka zani fara lissafa maki su kafin mu tafi akan bayaninsu.

 • Dinki
 • Saka
 • Saro Kaya daga Waje da saidawa

 

Dinki

Sna’ar Dinki wata sana’a ce wadda ake samuin kudi da ita sosai, wadda maza da mata duka suna iya yinta koma kowa na samu.

Sna'ar Dinki

Abun lura ga dinmki shine kowa dole yasa kaya ajikinsa,  kuma kayan nan ana yawan son masu kyau musamman lokacin Bukukuwa, suna ko kuma shagulgula kamar na sallah.

A dalilin haka ne idan kika fara dinki indai kin iya style mai kyau ga yanuwanki mata zaki iya tashio da kusan dubu dari  biyu karanci a shekara.

Abubuwan da kike bukata domin fara Dinki

 • Keken dinki
 • Almakashi
 • Zaruruwa
 • Jarin sayen kananun abubuwa kamar su allura

Saka

Sana’ar saka ana samu da ita kuma tana daya daga cikin sana’oin hannu  wanda an dade ana yin su a kasar hausa sai dai yanzu abun ya canza.

Saboda a da komai da bahaushe yake sawa saka shi ake yi kamar su hula, atamfofi da sauransu to amma yanzu mata da ance sana’a ta kayan sanyi tafi ziomasu a rai.

To kayan sanyo iya saka su yana da matukar amfani kuma kasuwar su n ja mussamman a lokacin sanyi.

Amma a shawarata kina iya hadawa da sakar abubuwa irinsu kafet ko kuma irinsu hula kamar su kube da sauransu yadda ba lokacin sanyi kawai kasuwar ke ja ba da wani lokaci yayi ta kwanta.

Kayan da ake saka da su

 • Injin saka
 • Zaruruwa
 • Allurai
 • Almakasi
 • Jarin da zaki sayi wasu kayan da ake bukata

 

Saro kaya daga waje da Saidawa gida

sana'ar saro kaya daga waje

Mata a wannan zamanin sun gane wannan sana’ar ta saro kaya daga waje musamman suna sayen kaya daga china su saida a nan gida wanda mun koya ta a baya.

Yawanci yadda abun yake shine suna suna sayen kayan online sai a kawo masu post office su amsa.

Bayan haka sai su dora ribar su bayan an kawo masu a nan gida nigeria kina iya karanta cikakken bayanin a link na rubutu kamar haka.

Karanta: Yadda zaka sayi kaya daga China a kawo ma su har Gida

Abubuwa biyar 5 da ya kamata ka sani kafin sayen kaya online

Wannan sana’ar ko shakka babu tana da riba sosai domin, sun san yadda suka saya ga yadda zasu saida kuma yawancin kayan waje suna jama mutane musamman mata hankali sosai.

Abubuwan da kike Bukata

 • Waya ko kuma computer
 • Sa data da hada group na kafafen sada zamunta wanda zaki tara customin online dinki
 • Jari na sayen kayan

 

Kammalawa

Ta a nanne muka zo karshen wannan post din, dan abunda zan kara shine cewa kafin ki fara sana’a kisan ya take ki iya ta.

Sannan kuma ki dage da hakuri da ita da kuma kokarin kyautatama customomi saboda shi wanda yake sayayya wajenka yana son kyautatawa.

Bayan haka in kina da tamabaya ko kuma karin bayani kiyia a comment dake kasa ga masu son tunatartwa akwai karaurawa kasa sai su dannan da mun dora sabo inshallah zasu gani a wayar su.

karanta:

Yadda zaka habaka kanka ta fuskar karatu da bincike a koda yaushe ta hanyar amfani a yanar gizo

Kasuwanci: Hanyoyin Samun kudi masu saukin ga Dalibai

Abubuwa 12 dake sa mace ta zama Tauraruwar girki

Mungode.