Skip to content
Home » Sana’ar Dinki da yadda zaka fara ta

Sana’ar Dinki da yadda zaka fara ta

Sana’ar Dinki tana daga cikin sana’oi’n hannu na zamani wanda ake samun kudi da sy sosai musamman a nan kasar hausa idan akace lokacin bukukuwan sallah sun matso lokacin kowa yana bukatar yaga ya fitoi da kaya masu a jikinsa.

To bama wai kawai a ce a lkasar hausa ana samu da ita ba kawai a’a sana’a ce da duka duniya ana samun kudi da ida kwarai da gaske saboda abunda zaka kula da shi shine kowane mutum dole ne dai ya sanya tufafi a jikisa babu mai iya yawo hakanan to bari mu tafi akan ma’anar sana’ar dinki kafin muyi bayanin yadda ake fara ta.

Menene Sana’ar Dinki da Kuma Ma’anar sana’ar Dinki?

yadda ake fara sana'ar dinki

Abunda ake nufi da dinki ana nufin amfani da zare da allura wajen dinkawa ko kuma hade wani abu yadda zai bada wani abu mai amfani, a kuma fannin sana’a.

Sana’ar Dinki na wata sana’a ce da mutane ke yi wanda suke dinka tufafin da mutane suke sawa, yawanci mutum zai kaima wanda ake cema tela shine wanda ya dauki sana’ar dinki a matsayin hanyar samun kudin shi, mutum zai kaima shi yadi, shadda ko kuma wata atamfa ya dinka masa zuwa wani lokaci ya amsa bayan ya biya shi kudi.

Tun kafin zuwan zamani bahaushe yana yin wannan sana’a daga cikin sana’oin gargajiya wadda yawanci ana daukar ta a matsayin gado wato da ya gada daga baban sa.

Shin ana samun kudi da ita?

Ana samun kudi kau sosai da wannan sana’a ta dinki saboda akwai misalai da dama da zan iya baka in da da hali akwai mutanen da lallai da wannan sana’ar suka dogara sosai har suna iya cida iyalansu ba tare da wata kargada ba sun samu rufin asiri.

Wasu kuma ma wuce na c ida iyalai sun zama miloniyas da sun tara dukiya mai tarin yawa sosai, kai in takaice maka labari dai wannan sana’a ce da zaka ga kana da suka fara ta suka bude shago zaka ji mutum ya cemaka ay wannan azumin kusan da dubu dari biyu ya tashi to ka gani tsakanin azumi zuwa sallah mutum ya samu haka ai lafiya lau .

Musamman a wannan zamanin da zaka ga styles na dinki kala-kala daban daban wanda kullun kara gyara al’adun hausawa suke da haska su kowa yana sha’awar ya dauki wanka kamar yadda matasa ke cewa wanka iya -wanka.

Karanta: Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a

Yadda zan Fara Diniki?

To bayan matashiya akan wannan sana’ar bari mu tafi kai tsaye yadda zaka fara taka, yadda zaka fara kuma shine ka sani kana da bukatar manyan abubuwa guda biyu wanda zan yi maka bayaninsu dakamar haka.

 • Jarin sayen kayan aiki
 • Koyon sana’ar

Jarin sayen kayan aiki

Kamar yadda  ka sani Abu mai amfani kowace irin sana’a a fadin duniya tana da bukatar farwa da jari ko yaya yake kafin fara samun kudi da ita ya danganta karami ne ko babba, amma dai kamar yadda a al’ada yawancin wanda zai fara wata sana’a zaka ga da karamin jari zai fara.

karanta: Kasuwanci: Yadda ake fara kasuwanci da karamin jari

To da karamin jari ma kana iya farawa, kawai dai abubuwan da kake bukata sune ya kasance ka sayi duk wani karamin kayan ma’aikaci ko kuma babba yadda da ka fara aiki kawai cigaba zakayi kuma zan lissafa maka kayan da kake bukata na aiki manya da kanana kusan yawancinsu koma dukansu wanda zasu taimaka maka a wajen kasuwancin ka.

kayan sana'ar dinki

Kayan da ake bukata manya da kanana
 • Keken dinki
 • zaruruwa
 • Allurai
 • Almakashi
 • Reza
 • Man keken dinki
 • Tape
 • Sauran engina kamar na ziza ga idan da damar hakan

Wadannan abubuwan dana ambata a sama sune kake da bukata ka nemi kusan kashi 90 daga cikin dari nasu in son samu nayi ma ka neme su dukan su yadda da ka fara aiki shikenan inshallahu, sai kuma mu tafi abu mai mahimmanci na biyu wanda shine koyo.

Koyon sana’ar

Sana’oin hannu kusan dukansu komshakka babu kana da bukatar ka koye su indai kana son kayi zarra saboda ay yo idan ma baka iya ba to mi zaka yima mutane ne ay saidai kawai kallo, amma iyawa yana taimakawa a san da mutum sosai kuma sai ka samu inda zaka koya domin a koya maka.

Akwai wurare da dama da zaka je ka koyi wannan sana’a wadanda suka hada da kamar wajajen horaswa na sana’oin zamani na garinku ko kuma ka samu yan kudin ka kalilan ka je wajen mai shago ka biya shi ka ce mashi ya koya maka inshallahu zai koya maka yadda zakaiya sosai suma ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da kake bukata wanjen koyen ka je da su.

Abubuwan da kake bukata
 • Karangar nama saboda koyon yanka
 • Yan kyallaye yadda in ka fara ityawa zaka dan dinka
 • Kayan aiki kamar yadda na mabata.

Ababen da muka ambata a sama sukuma sune zasutaimaka maka wajen cimma gurinka na koyon wannan sana’ar ta dinki wanda zaka da su wajen masu koyama ka, a wannan wenbsite inshallahu bada dadewa ba zamu fara yin wani tsari na koyar maku da sana’ar dinki.

Daga nan kuma sai abubuwan da yakamat ka sa a ranka lokacin koyo/

Yadda zaka kasance a koyo

A lokacin da kaje da kayan aikin ka domin koyon wannan sana’ar tofa ka sa ma ranka cewara zaka tsaya ka nastsu ka fahimci yadda ake yanka ka tabbata a lokacin da akae koya maka yankan ka iya domin da shi ne zaka iya sarrafa sana’ar kana yin desioghn kala-akala da zaka ja hankalin masu kawo maka aikin dinkin.

Sai kuma abu na biyu bayan ka dawo gida ka cigaba da kokarin yawan maimata abun da aka koya maka kana kara yinsa a aikace yadda ba zakayi saurin mantawa ba.

Daga nan kuma kamar yadda na saba fada a wannan website sana’a kowace kala ce tana da bukatar mutum ya sa ma ransa hakuri dole sai da hakuri ake iya cimma buri duk wanda bashi da hakuri to baya iya komai idan kayi hakuri shekara daya zuwa biyu ka kware sosai musamman in kana danaci.

Karanta: Kasuwanci: Hanyoyin Samun kudi masu saukin ga Dalibai

Kammalawa

Kamar dai yadda na gabatar maka da bayani a sama sana’ar dinki sana’a ce da ake samun kudi da ita sosai gaskiya kuma daman a fannin kasuwanci yawancin abunda yafi albarka ko a musulunce shine sana’oin hannu wanda yake ci daga gumin hannayensa guda biyu.

To sai ka daura damara a tashi a ga an cimma buri ta hanyar jajircewa da kuma hakuri, bayan haka idan akwai tambaya kar ka ji komai aje a comment section wanda ke kasa zan amsa maka inshallahu, acigaba da kasancewa da mu a koda yaushe don sammun abubuwa na sana’aoi kasuwanci dama sauransu.

Karanta:

Hanyoyi 5 da Ake Samun Kudi da su a YouTube

Koyon Internet da Abubuwan da Suka Shafe ta

Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a

Maganin Ulcer da tayi Yawa(chronic) har abada