You are currently viewing Hanyoyi 5 da Ake Samun Kudi da su a YouTube

Hanyoyi 5 da Ake Samun Kudi da su a YouTube

Samun kudi a YouTube abu ne wanda mutane da yawa sukeyi sanadiyyar yadda youTube a wannan zamanin yake kara samun biliyoyin mutanen da suke ziyartar sa domin kallon bidiyoyi daban daban akan fannoni kala -kala.

A dalilin haka kamar yadda a baya mukayi bayani akan yadda ake samun kudi da wayar hannu a yau inshallahu bayan post din mu na yadda ake Bude YouTube Channel to a yau yadda zaka ci ribar ta zamuyi magana inshallahu akai.

Shin yaya ake samun kudi a YouTube?

hanyoyin samun kudi a youtube

Da farko dai yana da kyau mai karatu ka san cewa yanayin yadda ake samun kudi a youtube kamar yadda ake samun kudi ne a Internet, ba kamar kasuwancin ka na kasa ba offline kamar dai yadda kasuwancin online yake wato internet marketing.

A sanadiyyar cigaban zamani musamman zuwan internet ta sauya ba kamar da ba dole ne mutum yayi wata sana’a ta fgargajiya ko kuma ta zamani wadda za’a biya shi kudi cash wato hannu da hannu a online abun ya sauwa.

Idan akace samun kudi online mutane da dama suna mashi fahimta ba daidai ba suga kamar datar da suka saya daga mtn ce ake maidawa zuwa kudi a youtube a’a kwatakwata bun ko kusa ba haka yake ba, yadda abun yake shi kamfanin waya katin da ka saya ya baka data shine ya karu da kai kawai zai ringa kilga datarka yana kai ka zuwa shafukan da kakeson ziyarta a Internet kuma duk shafin da ka ziyarta baya biyan mtn kudi.

karanta: Koyon Internet da Abubuwan da Suka Shafe ta

Kwata kwata kamar yadda na fadi ba data ake juyawa ba hanypoyin da masu website suke samun kudi da su kamar ace shi kanshi google din tunda website ce gasu kamar haka.

Hanyoyin da masu shafukan Internet suke samu

Ga wasu daga cikin muhimman hanyoyin da yaka mata ka fahimta masu shafukan internet suke samu da su.

  • Hanyar Talla
  • Saida hajoji
  • Biyan kudi bayan anyi wani aiki
  • Han yar Tallafi da sauransu

To tunda kaji yadda kamfunna suke samun kudi ta internet bari muje ga  hanayoyin da ake samun kudi da su a youtube.

Karanta: Yadda ake bude YouTube Channel

Hanyoyin  samu a YouTube

Ga wasu daga cikin muhimman hanyoyin da zamu yi magana akan su tare da bayanin yadda ake samun kudi da su a youtube channel ga su a lissafe.

  • Daukar Nauyin Bidiyo
  • Tallace- Tallace
  • Dan jagorar Tallar kaya
  • Saida kaya
  • Sanya Talla a Bidiyo.

Daukar Nauyin Bidiyo

Hanyar daukar nauyin bidiyo a youtube tana daya daga cikin manyan hanyoyin da masu YouTube channel suke samu da ita. Inda zasu daura bidiyo wadda suka dauka ko kuma suka gyara ta amma kafin su dora ta a youtube channel dinsu wani kamfani ya dauki nauyin bidiyon wato a turance ana cema abun (sponsorshipe).

Amma yana da kyau mai karatu ya san cewa wannan yawanci sai youtube channel dinda take da mutane da yawa da tarin bidiyoyi wanda dubban mutane suke kallo, to da wani kamfani ya zo zai biya ka idana ka dora mashi kuma gaskiya suna biyan kudi sosai masu tsaka ga mutum.

Yadda zaka samu irin wannan dama shine ta hanyar daura abubuwa masu mahimmanci da amfani a cikin youtube channel dinka musamman idan kana daura abubuwan kamfanunnuka na technology wato kimiyya da fasaha ko kuma wasu dai ab ubuwa wanda kamfannunuka suke yi kana bayani akansu.

karanta: Koyon Internet da Abubuwan da Suka Shafe ta

Tallace-Tallace

Wannan tana daya daga cikin manyan hanyoyi da yawancin masu daura bidiyoyi a youtube suke samu da ita kusan ma kashi 90% ta wannan hanyar ce suke amfani, daga kamfanin shi youtube din wato ana kiranshi da turanci youtube pertners program.

Shi yadda yake shine kafin samun damar shiga a cikin shirin sai youtube channel dinka tana da subscribers guda 1000 tare da kallon awar bidiyo kuda 4000.

Daka samu wannan to zaka hada shi da adsense account wanda nan ne zasu samaka talla daga adsense suna biyanka kudi daidai gwalgwadon yadda aka kalli tallar a cikin bidiyonka da yadda yan kallon suka ji dadinta.

Dan jagoran Tallar Kaya

Dan Jagoran kaya yana nufin(Affiliate marketing) a turance yadda abun yake shine zaka tallata masu kaya su biya ka abunda ake cema commission a turance wanda kaso ne taga cikin ribar da suka samu suke biyanka.

Bayan kayi rigister da kamfanin da zaka tallata ma kayan zau baka link wanda zaka saka a kasan bidiyon wajen description da wadanda suke kallon bidiyonka ka masu bayani cewa akwai abunda zasu saya ko ga link da zasu bi a kasa da sun bi to zasu baka kason ka woto commission.

Saida kaya

Saida kayanka a cikin youtube channel yana da matukar amfani kana yafi ma a ce kayan wani kake talla indai ana saye saboda zaka samu customers dinka wanda wasu suna iya dawowa sayayya wajenka musamman idan ma sun ji dadin kayanka.

Ta sanadiyyar hakan zaka iya tara customin ka na kanka da kanka wanda zaka iya ganin wasu idan sunji dadin kayan zasu iya dawowa.

Sanya Talla a Bidiyo

A fannin sanya talla a bidiyo yadda zan kwatanta maka shi shine kamar yadda yan film suke sa tallar wani film kafin ya fito, to kusan a nan ma haka abun yake yake wani kamfani ko kuma wata youtube channel zasu iya baka talla ka saka a cikin bidiyon ka na youtube channel dinka.

Ana samun kudi sosai a wannan hanyar itama amma yana da bambamci da wanda muka magana a sama wato daukar nauyin bidiyo, saboda daukar nauyin bidiyo mutum zai biya kudin ya dauki nauyin bidiyon shi kadai zaka tallata mawa amma a wannan fannin shi zaka iya saka tallace tallace bana kamfani daya ba kawai.

Kammalwa

Kamar dai yadda nayi nayi bayani a sama ana samun kudi a youtube amma dai akwai abu mai mahimmanci kafin haka shine ka kula da abubuwan da kake dorawa a youtube ya kasance abubuwan kirki ne ba na banza ba.

Kuma a fannin samun kudi a youtube kayi iya kokarinka kaga kana sa tallace tallace ko kuma kana saida abubuwan da suka halatta wannan shine abun lura.

Karanta:

Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a

Koyon Internet da Abubuwan da Suka Shafe ta