Skip to content
Home » Sana’ar Art da printing ta fenti da abubuwan da ta kunsa

Sana’ar Art da printing ta fenti da abubuwan da ta kunsa

Idan muakyi magan akan sana’ar da ake amfani da karfi da abubuwa kadan a samu kudin shiga nan take masu yawa to tabbas wannan sana’a ta art zata shiga a sawu na gaba.

Saboda tana daya daga cikin sabna’oin zamni wanda ake bukata a dalilin amfaninta inda zaka kara ganinta ta fito fili shine kashi 90 na shaguna an yi masu zane na sunan su wanda aiki ne na masiu art.

A wannan post na yau zamuyi magan akan wannan sana’a da kuma yadda zaka fara ta da wasu kadan daga cikin muhimman abubuwan da kake bukata ka fara taka tafiyar.

Abubuwan da Sana’ar Art ta Kunsa

Ita dai sana;ar art ana yin abubuwa sosai da ita kuma ana samun kudi idan an jure bayan wasu lokutta, kamar design na irinsu banner, symbol na talla da sauransu duk masu wannan sana’ar ne ke yinsu.

Bayani akan fara samun kudi da art

Dole zakayi amfdani da abubuwa da yawa kamar su chemicals, penti da ma computer domin ita wannan sana’ar idan kana da ilimin computer zaka fi jin dadinta.

Dalilin da yasa na ce haka shine akwai da dama daga cikin design ko zane wanda dole sai da computer ne zaka iya yinsu ko kuma ka ba wani ya yimaka dudda tafi kunsar shafe- shafen penti sana’ar.

Ga wasu daga cikin abubuwan da ilimin computer ya kunsa nayi bayaninsu dalla dalla kana iya duba su:

Abubuwa 5 da suke sa dan koyon computer ya kware

Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su

Samun Kudi da Computer: Abubuwan da ya kamata ka iya na fannin computer domin dogaro da kai

Yadda zaka fara taka

Idan kana son ka fara ita wannan sana’a akwai hanyar da zaka bi mafi sauki wanda ga yadda abun yake.

Da farko kamar yadda nayi maka magana akan iya computer to ka koyi yadda ake zanen ko kuma abubuwan na printings a computer, akwai softwares wanda nayi bayaninsu a baya da kuma amfanin su wanda wasu na gini ne wasu kuma na printings ne.

Karanta:

Manhajar Software wadanda ya kamata ka koya domin dogaro da kai

Sana’ar Design na Printing da Yadda Ake Fara ta#

Daga nan kuma a fanni na biyu sai shi fannin ace an tsara abu to yaya za’a fiddo shi a ganshi karara ayi printing ko kuma a shafa sa a wani bango.

To wannin fanning shine na biyu wanda shine ginshikin kusan sana’ar ya kasance aikin da zaka yi ya fito sosai yayi kyau yadda zaya burge duk wani wanda zaya kalla.

Kuma ya kasance kana kulawa da yanayin kala wace kala ce idan ka sa ta a cikin wata zata bace wace ce kuma idan aka sa ta tana da zan hankalin mai kallo sosai dole sai ka sa lura akan irin wadannan abubuwan.

Abubuwan da zaka iya yi

Ga wasu daga cilkin muhimman abubuwan da idan ka iya zaka iya yinsu kamar haka:

  • Poster
  • Steaker
  • Calender
  • Symbole
  • Stamp
  • Rubutun Riga
  • Binding
  • Baje da sauransu

Kammalawa

To kamar yadda na ambata maka ita wannan sana’ar babban sana’a ce ma da za’a ce yawancin masu hyinta idan akwai gaskiya da alkawari suna samun kudi sosai da ita kamar yadda na gayama tana da bukatar ka iya computer domin samun saukin wasu abubuwan, sai kuma fannin hadin chemical da penti wanda zakasan wace ka;la zata fiddo aikin ka.