Skip to content
Home » Abubuwa 5 da suke sa dan koyon computer ya kware

Abubuwa 5 da suke sa dan koyon computer ya kware

Dan koyon computer koda yaushe yana da sha’awar ya kware saboda kwarewarsa zata bashi daman yin wasu abubuwan da sauri a lokacin da ya dace.

To kamar yadd a baya nayi magana akan fannonin da ya kamata ka koya na computer wanda ake samun kudi sosau da su a yau inshallahu zamu yi magana ne akan wasu abubuwan da zaka kula da su domin ka kware a fannin d ka zaba.

kuma kamar yadda na ambata a baya kwarewa ita ce babban ginshikin da mutane zasu ji suna son ka yi masu aiki

Muhimman Abubuwan

Domin kwarewa akwai bukatar ka riga yin wadannan abubuwa kamar haka ga kuma bayaninsu

kwarewa a computer

Yawan yi

Duk wani abunda ya kasance ka koya a cikin computer to akwai bukatar ace kana yawan maimaita shi kuma dama ko a karin magana ana cewa yawanyi shike sa a kware.

A matsayinka na wanda dan koyon computer to yana da kyau a fannin da ka dauka ka rika yinshi kullun yadda zaka kware sosai.

Ba dole sai ka ce ka takura kanka ba sosai a’a ka yi tsari misali a duk kullun zaka maimata kamar awa day shin fanning programming ne ko kuma wani fanni na desighn na hoto ko kuma bidiyo.

Musamman ga wadanda suka dauki koyon fanning programming idan basu yawaita yinsa to basu iyawa sai da tyawan maimaitawa a ke iyashi.

Karanta: Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su

Kirkira project

Abu na biyu mai kuma matukar amfani shine da ka iya ka samu wani project da kake yi da kanka a fannin abunda ka koya saboda hakan yana taimakawa sosai.

Abunda nike nufi a nan shine duk bayan ka iya wani abu to sai ka hada wani abu da shi

misali idan kamar ka kmoyi zane to sai ka fara yin zanen na abubuwan da ka iya in kuma kamar gyaran hoto ne sai ka samu hoto ka gyara in kuma bidiyo ce itama dai hakan.

Wani misalin kuma idan kamar programming ne sai ka hada wani application ko kuma software.

Karanta:

Yadda ake hada Android Application

Yadda zaka fara Sana’ar Saida Data

Yawan amfani da controls

Contols suna daya daga cikin abunda yake sa sauri sosai wanda yake bambamta dan koyo da kuma wanda ya kware

Saboda amfani dasu yana sa ka rika yin sauri amadadin a ce kullun sai ka taba mause din computer da ka taba malatsi a cikin keyboad zai yi maka wani aiki a cikin saurin wanda kila da da mouse zakayi amfani sai ka je nan ka kuma tafi a cen sannan kayi shi.

Muna da short short cut a computer kusan wanda suka kai tun daga harafin A har zuwa Z da kuma wasu sauran da F da ake amfani da su.

Gaskiya lakantar su ka iya koda ba duka ba ka san wasu muhimmai masu yawa yana da amfani sosai kuma duk inda ka je za’a gane cewar wannan ya kware a harkar na’ura mai kwakwalwa.

Karanta: List of keyboard control shortcut keys and their functions in the computer

Bincike

Yawan bincike yana taimakawa sosai saboda ta hanyar bincike ne zaka iya gano wasu sabbin abubuwan da ake inganta wanda zaka kara a cikin ilimin computer dinka.

Ko kuma kaga yadda aka sauya wata manhaja ko kuma kara inganta ta yadda zata zama mai amfani ga alumma bakidaya gami da kara mata sabbin abubuwan da za’a iya yi da ita.

A lokacin bincike ne zaka san hakan kafin mutane su ankara kana iya samun wani sabon ilimin da ba kowa ya iya shi ba a garinku koma a kasa baki daya.

Yadda zan baka wani misali shine a farkon zuwan Bitcoin wanda suka fara bincike akan sa kuma suka bashi mahimmanci sun zama millionaires wasu ma a matakin Billionaires suka a yanzu.

To ka ga minene ya taimaka masu hadda bincike akan wane sabon abu ne ya kunno kai wanda sauran basu yi ba.#

Karanta: Yadda zaka habaka kanka ta fuskar karatu da bincike a koda yaushe ta hanyar amfani a yanar gizo

Sa hikima

Abu na gama kuma shine yin amfani da baiwa ko kuma hikimar da Allah ya baka wajen gane wasu abubuwan da sanin yadda zaka bullo ma wasu abubuwan.

Karanta: Sana’ar Rubutun Littafi da Bayani akan Marubuta

Saboda indai kana aiki da computer zaka ga harkullun kana sake gane wata sabuwar dabara wadda a da cen baka fahimce ta ba.

To hakan yana taimakawa gaskiya sosai kuma yana kara inganta maka iliminka na na’ura mai kwakwalwa.