You are currently viewing Samun Kudi: Kasuwanci guda 10 wanda aka fi saurin samun kudi da su

Samun Kudi: Kasuwanci guda 10 wanda aka fi saurin samun kudi da su

Kasuwanci: jama’a a wannan post din zamu yi magana akan samun kudi, wadanne kalar kasuwanci ne ko sana’oi da suka fi saurin kawo ma mutum kudi domin dogaro da kai, domin akwai kala kalar kasuwanci a duniya wanda har Dalibai suna iya yi musamman a wannan zamani na cigaban ckimiyya da fasaha harkokin kasuwanci ana amfani da Internet wajen bunkasa su.

Da farko da kafin mu lissafo su samuyi magana akan shi kanshi kasuwanci da kuma minene alakar shi da samun kudi.

Kasuwanci

Minene Kasuwanci?

Kasuwanci dai yana nufin saye da sayarwa na wani abu ko kuma haja wanda abun nan yana iya kasancewa wanda ake gani ne kuma kuma wanda ba’a gani ne kamar mutum yayi wani aiki a biya shi to duka suna daukar ma’anar kasuwanci, wanda yake samun kudi da kasuwanci ba aiki yake a biya shi ba shi ake cema dan kasuwa.
 kasuwanci a musulunci

Minene Matsayin Kasuwanci a Musulunci?

Ko a musulunce ma Allah ya halarta kasuwanci a saya a saida inda kuma ya haramta kishiyar haka ita ake kira da riba yadda zani kwatanta maka misalin riba ita ce mutum misali ya ranta maka wasu kudi sai ya c e ka kawo mashi da kari, kamar misali ya ranta maka dari yace ka kawo dari da goma to gomar ruwa ce haramunce a musulunci wannan yana daga cikin misalin riba.

Gida nawa ne Kasuwanci Ya Kasu?

Kasuwanci ya rabu zuwa gida Biyu wanda sune
1. Sana’ar Hannu
2. Sana’ar Saye da Sayarwa
Tunda munji Matashiya Game da Kasuwanci bari mu tafi zuwa ga kasuwanci guda Goma wadda ake samun kudi da su.

Saida Kayan Chemicals

Wannan kasuwanc na saida kayan chemicals ya kunshi saida irinsu man shafawa, Air freshner da sauransu ana samun kudi da shi sosai musamman ga wanda yayi hakuri da shi wannan kasuwancin.
kuma kamar yadda masu yawan ziyarar wannan shafin suka sani a wannan website din mun koya yadda ake hada irin su Man Shafawa, Air Freshner. Ba su da wata wahala da kudinka kadan ma kana iya fara shi irin wannan kasuwanci.

 

Ga wanda yake da bukatar farawa akwai training da muke koyawa a farashi mai sauki a koya maka/ki idan kuma kana son sayen Sinadaran hada su wadannan kayan to sain ka tuntube mu muna saidawa.

Email address
fasahaltd@gmail.com
+2349037157675
ko a facebook a www.facebook.com/Hausawasite

 

Saida Kayan Sawa

Sana’ar saida kayan sawa ba karamin samun kudi ake da ita ba saboda kowa dai dole ya sanya kaya a kullun wanda kuma kowane mutum yana yawan canza kayan da yake sawa a koda yaushe abubuwan da ake samu da su sun hada da saida Shaddoji, yaduka atamfofi da sauransu.
Saida Kaya
Yadda mutum zai fara wannan sana’a yana da sauki idan kana da jari mai yawa kana iya kama shago da wuri ka fara saida ma mutane kaya musamman a wannan zamani na cigaban zamani kana iya dorawa har a status na kafafen sada zumunta domin abokanka su gani domin  su gane.
Idan kuma karamin jari gareka gana iya hada kai da wasu manyan yan kasuwa wanda zasu ringa baka kayan a kan sari sai ka dora in an nema sai ka saida akwai bayanin da nai akan  Fara kasuwanci da karamin jari kana iya duba shi.

Saida Electronics

Sana’ar kayan Electronics ana samun kudi sosai musamman idan mutum ya zuba jari a cikin harkar domin shi kasuwanci wanda ke da sirri saidai amma ba na karamin dan kasuwa bane saboda yana da bukatar ace kafin mutum ya fara irin wannan kasuwanci ya kasance yana da kudi soisai.
Samun Kudi
To bayan mutum ya samu inda zai ringa sayen kayan ya kamata yayi tunani idan karamin jari ne yana iya saya a nan gida Nigeria idan kuma kamar da yawa mutum yake so so to akwai daular saida kayan Elec tronics kasashe kamar irinsu china, japan da sauransu.
Idan kana da karamin jari kana son ka sawo kaya daga waje kana iya sayen kaya daga China a kawo maka su har gida Nigeri da yan kudinka kalilan.
Karanta:
 

Communication Center

Sana’ar Communication tana daya daga cikin manyan sana’oi wanda mutane ma sun fara gane shi saboda yanayin samun kudin da ake kuma saboda shi kasuwanci ne wanda kowa dai yana da waya a hannunshi musamman zamanin manyan wayoyi irinsu Android da Iphone.
samun kudi
A fannin saida kayan ya kunshi saida irinsu Earpiece, Charger, USB kayan waya da sauransu mai wannan sana’a ma yana iya karawa da kyaran waya domin karin kudin shiga a kasuwancin wanda kamar yadda kowa ya sani kyaran waya abu kadan sai ka ji an ce maka naira 1000.

Sana’ar POS

Shi wannan kasuwanci na POS kamar kaima ka zama wani dan karamin banki ne wanda mutane za su zo wajenka su yi zuba kudi kuma idan sunaso su cire kudinsu suna iya cirewa bayan ka yimasu wannan aikin sai su baka ladar aikin da ka yi masu.

POS yana da sirri saboda gaskiya indai ana zuwa kai shi ko duk rana kana yin transaction guda goma zaka ga kana tashi da kudi musamman yanayin yanzu  mutane basu cika son yin layi a banki ba.

bayani akn pos

Shi wannan kasuwancin kana iya fara shi da zarin kamar dubu dari ko abunda ya wuce haka yadda zaka samu walwala ba kullun sai ka rinka shan wahalar komawa a banki ba kana fidda kudi saboda customomi

Kuma yana da bukatar mutum ya samu shago mai tsaro musamman idan zai ringa aje wasu daga cikin kudadensa a ciki .

Noma

Ga wanda yake iya yin noma yana da Gona ko kuma yana da halin da zai iya amsar hayar gona to ina bashi shawara ya fara noma saboda shi noma ko a addinance shine hanyar arziki wanda hara a cikin Alkur’ani an ambata hakan.
Idan ka kula shi ciki dole a ba shi ya ci kullun hidimarshi ake yi kuma kayan abincin nan har kullunkara tsada kawai suke yi, sai kaga manomi indai har Allah ya kawo damana mai albarka ya samu kudi sosai tunda misali in na tambayeka nawa buhun masara yake da wannan ma kana iya fahimtar lissafin.
Kuma a yanzu zuwan kimiyya d fasaha akwai Noman da ake ba tare da kasa ba wanda mukayi magani a baya musamman ga masu yawan ziyarrar wannan shafi sun sani kuma munyi magana akan Yadda zaka sayi kayan duk munyi bayani to yanzu kasashen da suka cigaba suna ta kokarin yinshi.
Karanta:
 

Kiwo

Ire-iren sanaoin gargajiya kamar kiwo

Kiwo ba karamar riba ake samu da shi ba kusan ko wane kala ne misali bari mu fara da masu kiwon kaji idan ka samu kwarewa akan yadda ake kiwon kaji domin fa shima dole sai kana da ilimin abun ma’ana ka san yadda zaka yi alaka da su to indai ka kula cikin ikon ikon Allah ana samjun kudi sosai saboda baccin su kansu kajin ga kwai ga kuma taki duka kana iya szaida su.
Baya ga kiwon kaji akwai na dabbobi wwanda raguna dai kamar yyadda kowa yake gani tsada suke karawa kowace shekara kusan ga shi daman mafi yawancin layya dasu ne ake yi, sauran sun hada da kiwon kifi duka kan aiya farawa idan kana da wuri da kuma jari matsakaici.

Saida Kayan Noma

Bayan an noma Hatsi ko kuma wasu yayan marmari riba ce ace kai kana amso su kodai kai tsaye daga manomin ko kuma ace kana zuwa wajen yan sari wadanda daga gona suka sawo su.
Kamar misali kayan marmari irinsu ,lemu. ayaba, gwanda duka ana samjun riba sosai da su saboda mutane suna yawan cinsu musamman lokacin azumi, in kuma kana da sha’awar kayan miya to kaga suma kasuwanci ne wanda kullun kowane gida dole ayi cefane.

Sana’ar Printing

Ga wanda yake da kwarewa a fannin computer  in dai kana da computer mai lafiya ana samu da ita  musamman idan mutrum zai tsaya ya koyi abubuwan da ake samun kudin da su maar yin irinsu Invitation, calender, printing da photocopy da sauransu.
Wani abu kuma mai mahimmanci ita computer ba wai kawai a fannin irinsu prin ting ake samun kudi da ita ba a’a har ma da fannin Internet kana iya samun kudi online akwai hanyoyi da dama, ko kuma ta hanyar hada Android Applications  indai kasan kayan da zaka samu wadanda zasu taimaka maka wajenhada apps din wato software ta hada android apps.

Sana’ar Provision

Kayan provision su fa indai aka cemaka akwai customers to lafiya lau musamman wanda yake dealer na wannan harkar saboda yawanci zakaga abinci ne wanda akeyi packeging a ledder da sauransu kuma kullun ana yawan amfani dasu.

 

Author Profile

Ibrahim Buhari
Ibrahim Buhari

This Post Has 3 Comments

  1. GBPLUS

    There is no way to get this useful info . Its very fabulous and easy for me to get it from FM WhatsApp. I am very thankful and I appreciate your intelligent work. Awesome!!

  2. Mobile Legends Mod Apk

    Thank you for sharing this. It was helpful. Keep sharing such things.

Comments are closed.