Minene Bitcoin: Har kullun zakaji ana yawan magana akan Bitcoin, ko kuma ace Cryptocurency wanada a kafafen sada zumunta ma zakaji wasu na cewa suna samun kudi da shi, to a wannan post din inshallahu zamu yi bayani akan Bitcoin da abubuwan da suka shafe shi yadda mai karatu zai fahimcesu.
Table of Contents
Minene Bitcoin?
Bitcoin dai daya ne daga cikin nau’ikan cryptocurencies wanda yafi suna kuma shine na farko a duniya wanda kana iya saye da sayarwa da shi kamar kudi na zahiri amma shi a cikin computer ko na’ura mai kwakwalwa ake ganisa ta hanyar wasu yan lambobi a cikin asusunsa kuma babu wata hukuma ko banki da ke kula da shi a duniya.
ko shakka babu Bitcoin na fi alakanta maka shi da zinari da azurfa musamman yadda ake amfani da su a zamanin da, saboda shima ana tono shi kuma yana hawa yana sauka kai bugu da kari ma ana iya amfani da shi wajen sayen abu ko kuma saida shi kamar kudi.
Minene Tarihin Bitcoin?
Bitcoin dai ya samu asali ne a shekarar 2008 daga wani wanada har yau ba wanda ya sanshi wanda ake kira da Santoshi Nakamoto amma mutanen duniya gabaki daya sun fara amfani da shi a cikin shekara ta 2009.
Tun daga lokacin ne aka cigaba da amfani da shi a matsayin kudi, dudda a farkon al’amari bai da daraja kamar yanzu, daga baya ne mutane suka farga suka ga yana da daraja suka cigaba da amfani da shi tare da kuma kirkiro sauran irinshi kudaden Cryptocurrencies din kamar suy Etherium, Dai da sauransu.
Shin ana iya maida shi zuwa kudi?
Amsar wannan tambaya ita ce eh, kamar yadda na ambata a baya shi kudi ne wanda a rubuce zaka gansu a cikin wayarka ko kuma computer dinka ta hanyar asusun ajiyar shi wato wallet.
Zaka iya turama wani bitcoin ta wallet address dinshi idan ka sayi wani abu a wajen sa kokuma ka saida mashi shi kanshi bitcoin din saboda har kullun yana hawa yana sauka ya danganta.
Karanta:
Kasuwanci guda 10 da ake saurin samun kudi da su
Mi ake nufi da tono bitcoin?
Hanyoyin da ake mallakar shi
Ta Hanyar Tonowa
Kamar yadda na fada a baya zaka iya tono bitcoin ta hanyar wasu manhajoji wanda wasu kamfanunnuka suke daukar nauyi zaka warware wani matsalar wani lissafi ne sannan ka tono shi to daga abun da ka tona zasu baka bitcoin, waddannan manhajoji su ake kira a turance da minning softwares.
Ta Hanyar Saye
Akwai wallet da yawa wato asusun Bitcoin wanda zaka iya aje abunka kuma in ka tashi saida shi kana iya saidawa ko kuma ka canza zuwa wani cryptocurency din wato swapping kenan to ta wannan ahanya ma kana iya mallakarshi.
karanta:
Author Profile
Latest entries
- UncategorizedAugust 16, 2024YADDA AKE HADA WEBSITE A KYAUTA DON BUNKASA KASUWANCI
- KasuwanciAugust 16, 2024Kasuwancin Saida Gidaje da yadda ake Samun Kudi da shi
- KasuwanciAugust 16, 2024kamfanin Biredi da yadda ake kasuwancinsa
- KasuwanciAugust 16, 2024Bayani akan Bude Kamfani domin dogaro da kai