You are currently viewing Samun kudi ta Zuba Hannun Jari

Samun kudi ta Zuba Hannun Jari

Shin ko ka san cewa har kana kwance kana iya samun kudi ta jarin da ka zuba? a kamfunnan wannan ba bakon abu bane ba kuma mafi yawancin kasashen da suka ciagaba yanzu suna amfani da wannan dama su sayi sharae a kamafani a riaka basu wani kaso in ta tashi su saida.

Kusan duk wani wanda kaga yanzu ya zama mai kudi kamar wanda yafi kowa kudi a duniya ko kuma a Africa zaka ga cewar suna da hannayen jari a wasu kamfunna ko kuma ana zuba masu a nasu famfanonin.

Hannun jari

Mi ake nufi da Zuba Hannun Jari?

Zuba hannun jari a kasuwanci yana nufin sanya kudi a kasuwanci domin habbaka shi ya danganta daga karamin kamfani ne ko kuma kuma babba wada ake son a habbaka.

Makasudin zuba hannun jari a kasuwanci shine domin kara fadada ayyukan kamafani. ta yadda zai iya samun damar kara yawan abubuwan da yake hadawa don samun karuwar kudaden shiga.

Kusan duakan kamfunnan da kaga a duniyar yanzu sun girma har suna yin rassa a garuruwa koma a fadin duniya to ta hanyar sharae ce suke cimma burikan su kuma shiyasa a bayani na na hanyoyin maida karamin kasuwanci zuwa kamfani na kawo hakan.

Idan mutum yana da hannun jari a kamafni ribar da wannan kamafni ke samu ana rabawa ga wasu kamfanin kenan wanda shine ake cema devidents a turance ya danganata ana iya badawa a duk shekara ko bayan shekaru.

Karanta: Kananun Sana’oi 10 Masu Saurin Kawo Riba Wanda ake Iya Farawa Da karamin Jari

Bayan bada kason riba kuma idan kimar kamafnin na sama sahare sa na kasa hawa kamar yadda idan yana asara tana rage yawa sai dai wasu kamafunnan basu bada devidents kawai zaka tafi ta kimar shareka shin ta karu ko kuma ta ragu.

Hannun jarin da ka saya daga kamfani koda yaushe kaga dama kana iya saida shi idan kana son kudinsa kuma kana iya saye saidai masu wayau suakna saida bayan ta tashi su kuma saya bayan tayi sauki ko ta fadi.

Karanta: Abubuwan da ke Haska Hajar Karamin Kasuwanci su maida shi Kamfani

Nau’ukan Hannun Jari da Muke da Su

Hannun jari kala kala ne ya kuma danganta daga karami zuwa babba kuma kai da zaka zuba ya kamata ka tsaya kayi karatun ta natsu kafain kayi kokarin zubawa saboda kawcema yawan asara a fannin.

sayen hannun jari

Kasuwar Jari (Stock Exchange)

Kasuwar hada hadar jari iata ake kira a tuarnce da stock exchange , babban wuri ne wanda kamfunna suke neman a zuba masyu jari kuma ake saye ake saida jari na kamfanoni da dama kamar Nigerian Stock Exchange ta Nigeria.

Idan zaka sayi sharae a stock exchange akwai buakatar ka samu broker wanda shi yake saye yake saidawa ka saya wajensa idaan kuma zaka saida kayi masa magana ya saida maka yanxu ma da aka samu cigaba applications kamar irin na c hipper cash kana iya sayen share kuma kana iya saidawa.

A cikinsu kuma zaka ga yanayin yadda share dinka take yi shin tana sama ko kuma tana kasa ta hanyar graph da ke nunawa a kullun a cikin application din.

kanannun yan kasuwa

fanni na biyu kuma shine ta hanyen zuba jari a karamin kasuwan ci na yan uwa ko kuma abokai, shima yana daya daga cikin hanyar sayen jari wanda idan kasuwancin yayi gaba zaka samu kudi soisai.

Saboda shifa kasuwanci kullun yana son ya zama akwai jari mai yawa a tare da shi kuama idana aka hada kudaden mutane da yawa yafi ace na mutum daya ne aka sa kawai saboda yanayin  yadda abun zai girma.

Da wannan ne kasashen da suka cigfaba zaka ga kusan koda ace mutrum yana da karamin kasuwanci to zaka ga shi kullun tuanani yake ya za’a zuba masa jari ya koma kamfani na billioyin kuade.

sanya hannun jari a kasuwanci

Amfanin Zuba Hannun Jari

Zauba hannun jari yana da amfani da dama ga kuma wasu muhimm ai daga cikinsu .

  • Juya kudi amadin aje su hakanan, wanda hakan zai kawo riba.
  • Samun karin hanyoyin kudin shiga ga mutum.
  • Maganin ajiya hakanan a banki wanda suma bakin juwa kudin suke.
  • Taimakawa kanana da manyan yan kasuwa wanda yake saurin habbaka tattalin arzikin kasa da yanki bakidaya.
  • Fadada kamfunna ta yadda zasu dauki ma’akata wanda hakan yake taimakawa wajen magance zaman banza a cikin al’umma.

 

 

 

 

Author Profile

Ibrahim Buhari
Ibrahim Buhari