Skip to content
Home » Hanyoyin 5 da Suke Taimakawa Wajen Maida Karamin kasuwanci Zuwa Kamfani

Hanyoyin 5 da Suke Taimakawa Wajen Maida Karamin kasuwanci Zuwa Kamfani

Sau da dama muna yin kasuwanci kullun ko kuma mu dauke she a matsayin karami wanda abu kadan zamu yi wani lokacin ya koma babba ya kai matraki na Kamfani.

Kasuwanci yana zuwa da kalubale wanda akwai bukatar ace mutum ya tsaya ya kula tare da amfani da muhimman abub uwan da zasu taimaka mashi wajen gina kasuwanci tsayaye.

Wanda yin hakan yana da matukar amfani shi zai haska kasuwar ta koma yanayin yadda mutane zasu girmama ta a fadin duniya bakidaya, saboda zakaga kasuwanci a ce a bu kamfani ne yafi daukar hankalin muitane sposai fiye da karamar sana’a.

A dalilin haka ne a yau a cikin wannan post din zaniyi bayani akan wasu muhimman hanyoyin da ya kamata ka bi domin habbaka daga karamin matakin samun kudi zuwa babba na kamfani wanda zai kawo kudade da yawa sosai.

kayan aikin kamfani

Hanyoyin Inganta  Karamin Kasuwanci Zuwa Kamfani

  • Hada Daular Kasuwanci
  • Bincike Akan Manyan Kayan Aiki
  • Registration
  • Daukar Ma’akata
  • Yawaita Yanayin Harkoki

Wadannan hanyoyi da na ambata a sama sune wadanda zani yi bayaninsu dalla dalla wanda indai a fannin kasuwancinka ka b i ahankalai ka yi amfani da su yadda ya dace zaka ga cigaba sosai.

Wanda hanyoyi ne da dama daga cikin manyan kamfanoni na duniya a nan gida da kuma kasashen waje suke bi wanda zakaga sun cigaba, kuma ka tsaya ka lura duk kamfanin da yayi suna yana da abubuwan da na zayyana a sama ga kuma bayaninsu kamara haka.

Karanta: Bayani akan Bude Kamfani domin dogaro da kai

Hada Daular Kasuwanci

Idan akayi magana akan hada daular kasuwanci a turance ana kiransa da Brand, wanda ana nufin hada wasu tsare-tsare da lkuma abubuwan da ana ngan in su za’a ga cewar wannan kamfaninka ne ko kuma kasuwanka ne ewanda kakeyi.

Daga cikin irin wadannan abubuwan sun hada da design na logo na kamfaninka, zabar kaloli wanda zaka rika mafani da su ga ma’akatanka da kuma abubuwsanka wanda kake hadawa.

Shi amfanin wannan shine idan har ka yima kasuwancin ka haka to kamar ka yimasa wani fasali ne wanda customominka zasu rika tunawa da kai suna da sunga kalar sai suce ay kamfani kaza ne kamar misali macline close up ja ce kalarsa, MTN Dorowwa ce kuma kowa ya san logon MTN.

karanta : Yadda zaka kyara kasuwancinka da hanyar hotuna don jawo hankullan masu saye

Bincike Akan Manyan Kayan Aiki

Kayan aiki a kowace irin harka ta samun kudi dole ne a ce akwai su kuma kullun zamani yana canzawa ana samun cigaba sai kaga abubuwa suna zuwa da sauki musamman a dalilin cigaban da duniya ke samu na kimiyya da fasaha.

To na daya daga cikin abunda zai gkara daga darajar kasuwa shgine bincike wanda duk babban kamfani da yake son ya cigaba da samun kasuwar sa a wajen masu sayya dole ne sai yana yinsa inba haka ba yanzu an bar sa a baya saboda cigaba ya zo bayayi.

Bincike akan hanyoyin samun kudi

Amma da zaran abu sabo yana zuwa har ka binciko ka sani to hakan na taimakwa sosai kuma hanya mafi sauki wadda zaka bi domin samun saukin bincike ita ce ta sanadiyyar Internet.

Domin ta internet ne zaka samu bayanai masu yawa kana wuri daya zanne kuma kana iya kallo ta bidiyo rubutu da kuma hotuna.

Karanta: Kasuwancin Online: Yadda ake amfani da fasahar yanar gizo(internet) a habbaka kasuwanci

Registration

Mallakar shaida ta kana da register kusan dole ma ne shi za’a ce ga duk wanda yake son ya zauna lafiya idan yana da wani babban kasuwanci haka kamar kamafani.

Saboda illar hakan shine ana iya samun matsala idan kana hada kayan amfani irin na ambinci ko wanda ake sama jiki NAFDAC su tuhumeka su lalatas maka tsarib wanda ba mai son hakan ta faru gare shi.

Amma iddan kayi register ka mallaki duk wani abu da kasarka take so kuma ka hada da shiga a cikin kungiyar irin kasuewanka ko tallafi ya zo cikin ikon Allah ka samu.

karanta: kamfanin Biredi da yadda ake kasuwancinsa

Daukar Ma’akata

A lokacin da kake son kara bunkasa yana da kyau ka kara yawan masu yimaka aikace – aikace wanada hakan zai sa saurin saye da sayarwa a harkar kasuwarka.

Domin kasan fa shima kasuwanci wani abu ne wanda ana son a tafi da sauri bada nawa ba, misali da wuri ka saida tirela goma a rana ba daya kake ba da mai saida kwara daya kuma yawan ma’akata bama daya bane kwata kwata.

Yawaita Yanayin Harkoki

Idan kana son kara samun cigaba yana kuma da kyau ka kara yawaita yawan harkokin da ke gudana a wajen samunka ta hanyar abub uwa wanda zasu ciyar da kimar abun a gaba.

Misalin da zan iya baka akan haka shine kara zuba jari mai yawa, bude rassa a garuruwa da kuma kara habbaka hanyoyin da zasu sa a sayi hajarka a cikin sauki daga ko ina’