Skip to content
Home » kamfanin Biredi da yadda ake kasuwancinsa

kamfanin Biredi da yadda ake kasuwancinsa

Biredi yana daya daga cikin manyan abinci wanda ake yawan cin shi a fadin duniya bama wai a kasar hausa ba kawai.

A dalilin haka ne kasuwancin biredi yana da riba kuma ana samun kudi da shi wanda hakan yaja mukayi dubi akan muyi bayani akan yadda zaka bude kamfanin biredin ka da kuma yanayin kasuwar sa.

Ya kamfanin BIredi yake?

Kamfanin biredi

Kamfanin biredi yana daya daga cikin kamfanoni da ya kamata ka sani wanda suka ta’allaka da abubuwan da mutane da dama suke yawan ci.

Kaga a dalilin haka ne yana da kyau kafin ka bude shi kuma bayan ka bude kayi taka tsan tsan ka kyautata saboda mutane da yawa zasu ruka ci.

Ga wasu muhimman abubuwan da kake bukata wanda zaka fara kamfanin biredi da su.

  • Jari
  • Wurin yi wato kamfanin
  • ,Ma’akata#
  • Kayan masarufi kamar su fulawa, yeast, maia butter, suga da sauransu.
  • gwangwanayen gasa shi
  • Rumbun gasawar na da ko kuma na zamani
  • Hanyar raba biredin

Bayan ka tanadi wadannan abubuwan sai kuma ga wasu masu amfani wanda suka shafi kmafnin da gwamnati.

Karanta : Bayani akan Bude Kamfani domin dogaro da kai

Muhimman abubuwan da ke taimakawa

Mallakar Lambar CAC

Idan kana son ka bude kamfani musamman ina magana ne da yan Nigeri mallakar wannan lamba tana da matukar amfani gare ka da kuma kamfaninka saboda kana da shaidar kasuwanci ta kasa.

Inda amfanin hakan yana taimakawa koda gwamnati tana son ta bada wani tallafi ko kuma rance ga masu kamfani ana saurin samu.

Zakaji suna cewa mutum ya sa lambar CAC kuma masu ita ana basu kudade masu yawa yawanci miliyoyin kudi suke samu daga gwamnati

Karanta: Manhajar Software wadanda ya kamata ka koya domin dogaro da kai

Register da Nafdac

Tunda yanayin kamfaninka yana kalkashin kamfunna masu abinci dole ne ka biyo ta hanyar kungiya mai kula da hada abinci da magungunnna ta kasa wato Nafdac.a

Dole ne ma kayi register idan ba haka ba akwai matsala suna iya tuhumar ka ko su kama ka.

Kuma suma yan kasar masu sayen kayan ka sun fi jin dadi suga akan abun akwai wannan lambar sun san gwamnati ta tantance shi.

Register da kungiyoyin Biredi

Abu na gaba shine hada kai da sauran takwarorin ka a cikin harkar kasuwancin wadanda kuke sana’a iri daya.

Hakan yana taimakawa saboda ko karin kudi sun karu ko kuma wani ragi zaka sani a nan.

Bayan haka kuma akwai kyautuka da kungiyoyi masu zaman kansu suke samu daga wasu ko kuma daga kwamnati musamman idan wata mtsala ta samu.

Kai ko babu matsala haka nan kuna iya samun tallafi a ce sai wadanda suke a ciki kaga tyana da kyau kayi register da ka hadu da su domin samun cigaba.

Abu na gaba kuma sai mu tafi akan yanayin kasuwancin.

Karanta : Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a

Yanayin Kasuwancin

To kasuwancin biredi yana kasancewa a matakai daban daban ga wadansu wanda aka fi yi ake kuma yawan samun nasara kamar haka.

  • Daga kamfani zuwa yan talla
  • Daga yan talla zuwa masu shayi ko kuma shaguna
  • Daga masu shayi ko masu shaguna zuwa masu saye dai daya
  • Daga kamfani zuwa masu saye dai daya

Karanta : Sana’ar Dinki da yadda zaka fara ta

Wadannan abubuwan da muka lissafa a sama suna da buka kayi masu karatun ta natsu da kyau ka fahimce su don nan ne customominka suke.