Skip to content
Home » Manhajar Software wadanda ya kamata ka koya domin dogaro da kai

Manhajar Software wadanda ya kamata ka koya domin dogaro da kai

A zamanin yanzu abubuwa da yawa sun koma a na’ura mai kwakwalwa wanda mutane da dama suna samun ayyukan yi ta hanayr samun ilimin yadda ake amfani da ita.

A yau a cikin wannan post inshallahu zamu ga wasu daga cikin muhimman manhajoji na software wadanda idan ka iya su zaka samu kudade da yawa.

Kai dai kawai abunda kake bukata shine kokarin koyon wadda ka zaba da kuma kwarewa a faannin.

Manhajar software saboda koyo

Lissafin su

Ga su a nan kasa zan lissafa maka su tare da bayani akan kowace kamar yadda na fahimcesu da ayyukan da ake samu da ita.

  • Blender
  • Sweethome 3d
  • Inkscape
  • Wps
  • Olive

Blender

Blender wata software ce wadda ake amfani da ita wajen hada zanuka na modelind wato ana hada zanuka abubuwa yadda zaka gansu kamar da gaske.

Da wannan software din ce kamfanoni da dama suke amfani musamman na kere-keren manyan engina da kanana da kuma sauran kayan aiki, wanda ake spon ganin taswirarsu a 3d.

yadda zan yi maka bayani kja fahimta shine a zani muna da na’ui kala biyu 2d da 3d.

2d zane ne wanda zaka ganshi normal wanda baida na;i biyu ko ukku kawai zaka ganshi hakanan.

Shi kuma na 3d zakaga kamar yana da na’i duda ukku wanda zakaga zanen ya fita kamar dagaske.

To ita wannan software tana yin dukan su 2d da kuma 3d din amma anfi saninta da 3d din tafi shahara a nan.

SweetHome 3d

wannan software din ta kyauta ce itama wadda ake amfani da ita wajen zanen gida da fidda yanayin awon shi.

Yawancin masu zane wasu suna amfani da irin wannan software din saboda tana da kayan aiki sosai indai na fannin zana gidaje ne.

A zanen da kayi kana iya fidda shi a bidiyo, a hoto ko kuma ka fidda shi a yanayin littafin pdf domin nuna ma wanda kayimawa.

kuma kana iya printing din aikin da kayi a cikin hanay mai sauki kamar yadda na fadi itama wannan software din kyauta ce ba sai ka biya ko sisi ba.

InkScape

Idan ana magana akan software ta kyauta wadda ake zane da ita sosai to da kazo wajen inkscape zaka samu abunda kake so da yardar Allah.

Wannan software din ta kyauta ce wato open source kana iya download din ta kayi install a cikin computer dinka ba tare da ka biya ba.

Daga cikin muhimman abubuwan da zaka iya yi da ita shine kana iya zane kala kala kuma ka fidda shi a format dinda kake so kamar su png da kuma format na svj, kusan ita a svg take aje format dinta.

Kuma tana yin zanuka maya irin na isomerism wanda zaka ga sunyi model sosai kusan kamar yadda zanen 3d yake.

Daga nan kuma sai manhajar software ta gaba kuma ita ce.

Karanta : Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su

WPS Office

Wps software ce daga kamfanin kigsoft na kasar china wadda take da matsayin office suit software.

Yadda zan yi maga bayani ka fahimci office suit software shine wasu irin manyan softwayoyi ne wanda suke ayyuka kala daban daban na office.

Daga cikin abubuwan da suke sun hada da rubutu a fidda shi format kala daban daban kamar text da kuma pdf.

Sai kuma akwai fannin spreed sheet wato excel inda ake hada data base wato rumbun ajiya  na bayani wadda zaka iya amfani da ita kamar microsoft office.

Karanta : Rubutun Littafi: Manhajoji masu amfani ga masu rubutun littafi kamar Hausa Novel

Abu kuma  na gaba shine akwai fannin presentation wanda zaka hada slide wanda zaka iya sawa a projecter domin bayani a gaban taron mutane ko kuma ga masu koyawa musamman lectures kana iya hada presentation da ita.

wps softaware ce ta kyauta wadda kana iya printing da sauran abubuwa kuma tana da wajen ajiya na cloud storage wanda zaka iya adan files dinka a yanar gizo.

Karanta : Yadda Ake Fara Kasuwancin Printing da Photo Copy

Olive

Kamar yadda mukayi bayana a baya akan youtube abubuwan da ya shafe shi da kuma kayan aikin mai youtube.

To ita dai wannan software din ta kyaran bidiyo ce kana iya sa bidiyon da ka dauka ka gyara ta.

Karanta:  Kayan aiki da mai YouTube Channel ke Bukata

Daga cikin muhimman ayyukan da take sun hada da yanke bidiyo, kyara ta da sama ta effects, sanya waka ko kuma sauti, sanya rubutu da ma sauransu.

Ku cigaba da sancewa da mu domin samun post na sana’oi da abubuwan amfani kuma inshallah ba da daewa ba zamu fara koya abubuwa ta hanyar bidiyoyi