You are currently viewing Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su

Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su

Kana son sanin fannonin da aka fi samun kudi da su wanda ana neman wanda suka fi kawarewa a fannin? ko shakkah babu a wannan post din inshallahu zanyi maka bayani akan abubuwan da yakamata ace ka koya na computer kamar yadda a baya mukayi magana akan Yadda ake koyon Computer da kuma Bayani akan Ilimin Computer.

Mutane da dama musamman a kasashen da suka cigaba sosai suna amafani da computer wajen samun kudi wanda wasu sanadiyyar hakan yake zama hanyar dogaro da kansu.

samun kudi da computer

Ko dayake har nan kasashe ma su tasowa ma a africa sanadiyyar canzawar zamani wasu sun fara zama hakan to da farko bar muga menene ma’anar computer da kuma fannon da muke magana akai.

Minene Computer?

Kamar yadda ake yawan bada ma’anar computer wani abu ce wanda take ansar data wato wata kididdiga wadda take maida ita zuwa bayani mai amfani.

Computer tana da fannonin da yakamata a koya da yawa wanda ake samun kudi dasu wanda kuma zani lissafa su kamar haka.

Fannonin da aka fi samun kudi da su

  • Programming
  • Database
  • Software Operation

Bayan zayyani muhimman fannonin da aka fi samun kudi da su a computer wanda ya kamata lka koya ga bayanin su kamar haka.

Karanta:

Yadda Zaka samu kudi da abubuwan da ka iya da Computer su zama Sana’arka da inda zaka koye su

Android App:Yadda ake hada Android Application

 

 

Programming

Koyon Programming a computer

Fannin programming fanni ne da yake da alaka da ba computer umurni ta yadda zata tayi wani abu ko tasa ayi ayi wani abu.

Ana rubuta shi inda za’a tattara zuwa abunda ake cema software wanda hakan zai bada damar computer ta fahimci abunda ake nufi.

Wannan fanni yana da matukar amfani wanda iya shi yana sa mutum ya kai matakin da bai tsammani kuma fanni ne wanda masu kudin duniya Irinsu Bilgate mai microsoft da wanda keda Facebook Mark Zukerbarg suka kware har suka tare kudaden da suakayi suna a duniya.

Wadanda na lissafa su a sama su suka kirkiro wani abu amma idan so kake karinka aiki a biyaka wannan ma lafiya lau ne daka dage shikenan domin abun naci ne da juriya yake bukata sosai kafin a cimma guri.

Database

Koyon database

A wannan fanni na database yana nufin kwarewa a wajen adana abubuwa masu yawa domin yin amfani da su ta dakuma sarrafa su ta hanyar mai amfani.

Misalin irinabubuwan da wadanda suka kware a database suke sun hada da hada invoice wadda take nuna maka abun da ka saya a shago da kudinsu da total dinsu.

Dama shagon sun saka bayanan koyane abu na hajarsu da kudinsa a database kawai da ka zo sai a zaba a lissafa maka ayi maka printing ta papper wadda ake cema invoice.

Akwai software da ake irin wadannan abubuwan kamar su Microsoft Acces, Excel da sauransu wanda suka shafi database.

Ana samun kudi sosai idan har ka kware domin manyan wurare da suka hada da shaguna, masana’antu, makarantu da sauransu suna bukata su sosai.

Software Operation

Yadda ake koyon computer

Idan akayi magana a kana wannan fanni na computer wato software operation ana nufin sashe ne da ya shafi kwarewa ta hanyar amfani da software wadda zata rinka aiwatar da wani aiki.

Muna softwayoyi kala daban daban akwai wadanda ake rubutu da su, akwai na zane, na Gyaran Video da sauransu.

Samun kwareawa a irin wadannan fannoni yana ba mutum damar aiki a wurare daban daban daban wanda suka hada da office domin ka rinka yimasu rubutu, editing na video ko hoto kamar kidajen television duk suna bukatar irin wadannan kuma suna biyan kudi mai tsoka.

Banda haka kuma ma akwai wata dama ta ka bude kasuwancinka na kanaka kamar printing da photocopy wanda kana iya dogaro da kanka idan Allah ya taimake ka.

Karanta:

Yadda ake koyon Computer da kuma Bayani akan Ilimin Computer

yadda ake samun kudi online (Cikakken Bayani)

Ire-Iren Sana’o’in Zamani 5 da ake yi da waya don samun kudi

Kammalawa

To abunda zan cika da shi a nan dai shine koyon computer kamar dai yadda na ambata a baya yana da matukar amfani wanda idan ka rike shi kana iya dogaro da kanka da shi sosai.

Kawia dai abunda ake buta shine kasa ,ma ranaka hakuri da kuma son abun yadda komin wahalarsa ba zaka gajiya ba tunda har dai wani yayi to kaima ko shakka babu zaka iya.

 

 

 

 

 

 

 

 

This Post Has 2 Comments

Comments are closed.