Skip to content
Home ┬╗ yadda ake samun kudi online (Cikakken Bayani)

yadda ake samun kudi online (Cikakken Bayani)

Samun kudi online wani abu ne wanda yanzu mafi yawan mutane sukeyi musamman ma turawa wanda a kasashensu suka cigaba wannan ya faru ne duk dai sanadiyyar zuwan Internet.

Ita dai kafar sadarwa ta internet ta kasance wani abu wadda ake yawan amfani da ita wajen aikawa turawa da sko wanda a dalilin haka yake jaza wasu dubarun da ake bi domin samun kudi da ita, a alilin haka ne zan yi bayani akan hanyoyin da ake samun kudi da su tare da bada cikkaken bayani inshallahu akan samun kudi online din.

Samun kudi online

Ya samun kudi Online yake?

Idan akayi magana akan samun kudi online ana nufin bin wasu hanyoyi ko dabaru wanda ake samun kudi da su ta hanyar kafar sadarwar zamani ta internet.

Hanyar ita ce zaka yi connect din computer ko kuma wayar ka internet yadda zaka samu damar.

Wanda yawanci zaka iya cirewa ta hanyar bankinka na Gida.

Kusan yanzu abun lura game da wannan shine ,ba don kasashen mu ba da yawancin mutane suke ganin abu hakanan basu bashi mahimmaci ta hanyar bincike, a’a kawai su da abu ya zo masu su doke shi a matsayin yaudara.

Wannan ita ce babbar matsalar da muke fuskanta a kasashe masu tasowa kamar su Nigeria da Niger.

Hanyoyin da bi a samu

da Farko dai zan fara lissafa muhimman hanyoyin da ake bi ana samun kudin da su daga baya zani yi bayani dalla dalla tare da bada misali ga kowace hanya.

  • Yin Aiki a biyaka(Freelancing)
  • Samun Kamasho daga Talla(Affliate Marketing)
  • Saida Kaya Online
  • Tonar Kudin crypto
  • Rubutu Littafi
  • Hada CouOnline ses da saida shi

Yin Aiki a biyaka(Freelancing)

Wannan hanya ta yin aiki a biya ka a online haya ce wadda ana samu sosai da ita kuma zaka iya samun kudi a dollars inda in ka fassara su zakaga a kudin nigeri sun da yawa.

Yadda abun yake shine akwai shafukan internet wato websites da dama wanda mutane musamman turawa suke zuwa suna bada aiki wanda idan mutum yaga yana iya yin wannan aikin sai yayi su biya shi .

Ya danganta ga yanayin aikin akwai wanda in kana yinsa duk awa ana iya baka misalin dala $5 kaga in kayi awanni da yawa 5 x awar da kayi nawa kenan kaga kudi ne ba kanana ba.

To bari in baka misalen inda ake yin irin wadannan ayyuka wanda sun hada da websites kamar su freelancer, fivver, upwork.

Yadda abun yake domin fara irin wadannan ayyukan sai ka iya wani abu kamar zane, hada android application, hada website da sauransu dole sai ka iya wata sana’a.

Daka iya sai ka rinka shiga website din kusan kullun da wani ya sa aiki sai ka canka kayi in kuma zasu rinka tunatar da kai har ta email ma.

Zan cigaba da post din gobe da jibi inshallahi kasance da hausawasite.com.ng