Skip to content
Home » Koyon Programming na Computer cikakken bayani akan yaren computer

Koyon Programming na Computer cikakken bayani akan yaren computer

oyon programming na computer abu ne mai matukar mahimmaci wanda duniyar yanzu take takama da masana irin wannan fanni, wanda zaka samu da dama daga cikin wadanda suke da kwarewa a fanning suna samun kudi sosai.

Akwai hanyoyi da dama da programmers na computer suke samun kudi wanda a cikin wannan post din zamuyi bayanin su dalla- dalla yadda mai karatu zaya fahimta.

To kafin nan amma bari mufara da matashiya akan minene computer programming daga nan sai muje ga sauran muhimman abubuwan da suka shafe shi.

Karanta : Yadda ake koyon Computer da kuma Bayani akan Ilimin Computer

Mi ake nufi programming na Computer?

Idan akayi magana akan shi ana nufin tsara yadda zaka ba na’ura mai kwakwalwa wato computer yadda zata rinka aiwatar da wasu aika-akace wanda kammalallen tsarin shi ake kira da software.

Software ita tana aiki ne a cikin computer ba ka iya taba ta amma zaka iya ganin abubuwanta a cikin screem na na’urar ka imma computer, waya ko kuma duk wani na’in naura mai kwakwalwar sarrafa kanta.

Wadanda suka iya yadda zasu ba computer umurnu ana kiransu programmers wato yan tsari, sukuma wadanda ke kirkire kirkire na manhajojin da suke da amfani ga alumma ta hanyar warware masu matsallolin yau da kullun ana kkiransu developers ko kuma software engineers.

koyon programming

Ina ake koyon programming na Computer?

Tabbas mai karatu zai yi mamaki yayi kuma wannan tambayar inane ake koyon programming, kuma yadda abun yake musamman ma ga wadanda ba daliban computer ba wadanda suke karanta computer a matsayin course a babbar makanta ko kuma jami’a.

Akwai hanyoyi da dama na koyon programming amma ga wasu daga cikin muhimman da suke taimaka ma mutum wajen cimma gurin shi.

 Ta Hanyar Koyo da Kanka

Kasani cewa musamman a zamanin yanzu idan kana son koyon computer ko kuma ka koyi wani abu wanda ya danganta da Internet(yanar gizo), akwai hanyoyi da dama wanda zaka ji wasu mutane suce su suka koya ma kansu.

A duniyar yanzu musamman dalilin cigaban da aka samu na yanar gizo koyon abubuwa ya zama sauki a wajen mutane daban daban a fadin duniya wanda ta hanyar wayarka zaka iya neman bayani koda hausa na idan ka tambayi Google ko kuma abubuwan nema na internet masu kama da shi.

To kame da koyo da kanka musamman programming kana iya ziyartar shafukan yanar gizo masu bayani akan haka, kalon bidiyoyi a youtube da kuma tambaya a shafukan tambayoyi na tattauna abubuwa musamman wadanda suka shafi programming din.

A hanyar ka ta koyo zakaga cewa kana makalewa ko kuma wata matsala tazo kawai kaje manyan forum kamar su Quora.com da suransu da ka tambaya ba dadewa inshallahu zaka samu amsa.

Bisa ga haka kuma suma kafafen sada zumunta na zamani kamar su facebook, twitter, Instagram da sauransu suna taimakwa sosai zaka karu kuma iidan ka yi tambay zaka samy amsa domin akwai wahala wani abu ya shige maka a duniya kayi tambaya a ki amsa maka.

karanta : Koyon Internet da Abubuwan da Suka Shafe ta

Ta Hanyar Training

Wannan hanya ta biyu ita ce ta hanyar training a kaginku ko kuma unguwar ku amma ka sani cewar koda ka samu training a unguwarku ku sai ka hada hada a hanya ta farko wadda itace hanyar kara koyama kanka ta bincike.

Yawanci wai kaje makaranta a koya maka baka cika kwarewa sosai ba idanb baka yin abunda ka iya a makarantar aikace, gashi kuma shi prigramming yana da bukatar ta kasance kana yawan yinshi a aikace ta hanyar kirkira mafita a dama a kan wasu matsaloli.

Amma hanyar training ian kana yin abun a aikace yana taimakawa sosai saboda ga malami a kusa da kai ita inda take da karin amfani kenan kuma ga abokai wanda kullun suke kara harzuka ka a kan abun.

Ta Hanyar Karantar Computer

Hanya ta gaba kuma itace ta hanyar karanta computer a makaranta a jami’a ko kiuma sauran manyar makaranta a matsayin abun yi.

Shima hakan yana da kyau kuma yana taimakawa matuka amma yana kyau ka rika binceka kuma ka karanta ta da niyyar ba wai kawai a yi a wuce wurin ba kawai ta hanyar sha wato craming akamr yadda yan boko ke cewa.

To karantawa ta hnayar iyawa da fahimyar abunda aka karanta shine yafi saboda yadda zaka hada wani abu da ka iya wanda hakan zai taimaka maka wajen samun kudi kamar yadda na ambata a farko masu irin wannan ilimin siuna samu.

Sassan Programming

Abu na gaba da ya kamata ka sani shine shi kanshi masu programming suna da sassa ta fannin abubuwa ko kuma mahajojin da suke hada ma al’umma wanda ake biyansu ko kuma su samu kudi da su kai tsaye.

Ga su a nan kasa zan lissafa su tare da bayaninsu sai kaga wane fanni ne kake da sha’awar shiga ciki ka taka rawa ko kuma ya kasancema hanyar sana’a ko kuma samun kudi.

Fannin Shafin Yanar Gizo

Fanni na farko shine na kirkira shafukan yanar gizo ta hnayr tsara shi, yimashi kyalliya da kuma abubuwan da ya shfi inganta tsaron shafukan yadda abun zai kasance mai amfani ga masu ziyarta.

A wannan fanni idan kana son ka iya shi akwai yarukan da suke da m atukar amfani ka iya kafin ka iya kirkira shafin kamar su:

HTML wannan yare ne wanda zaka hada abubuwan da ake gani na shafukan internet wanda ya hada da rubutu, abubuwan latsawa, akwatutuka da sauran abubuwan da wanda zai ziyarta zai iya gani a cikin computer din shi ko kuma waya.

Css sHI kuma yare ne wanda za ka koyi yadda zaka yima shafukan da ka hada da html da mukayi magana a sama kwalliya yadda zasu burge mai kallo da kuma taimaka mashi wajen fahimtar shafin.

JavaScript: Shikuma wannan yare ne da ya dogara da abun da ya shafi abubuwan motsi na shafin tyanar gizo duk yawancin motsin da zaka ga shafin yanar gizo na yi to da wannan tyaren ake yin shi.

Php: Wanna fanni shikuma ya danganci server wadanda akwai yaruka da dama wanda ba dole sai wannan ba kamar su python, ruby dama sauransu amma shi dai wadannan fannin yarukan sune na server wanda zasu taimaka maka wajen amsar bayanai na wanda ya shiga.

Ana hada shi da abunda ake cema database inda zai zama wata ma’adana ta abubuwan rubutu hotuna, da ma sauransu.

 

Fannin Manhaja

Fanni na biyu kuma shine fannin manhaja wanda shi kuma a nan zan raba shi zuww gida biyu kusan wanda sun hada da.

  • Manhajar Waya
  • Manhajar Computer
Manhajar waya

Wannan fanni shine ake kira da app developers wanda suke hada application na waya irin androi ko kuma wayar iphone.

Ga wadanda suke son kirkira manhaja ta android suna da bukatar iya proggramming languge kamar irinsu java, kotlin, C++ da sauransu duk daya daga cikinsu da mutum ya iya yana iya amfani ya kirkira mahajar android.

Sai kuma a fannin wayar iphone shi kuma akwai wani programming da ake kira da swift wanda da kafinshi ana amfani ne da wani yare wanda ake cema action script to iya daya daga cikin su kana iya fara hada apps na iphone.

Manhajar Computer

Abu na gaba kuma shine hada mahajoji wadanda suke aiki a computer wanda su irin wadannan mutanen ake kiransu da software develkopers ko kuma injineers.

Su aikin su shine su kirkia manhaja wadda zata iya gudanar da wani aiki a computer kamar ta rubutu gyaran bidiyo da sauran abubuwa da computer ke yi.

Akwai yaruka da dama da ake amfani da su wajen hada softwayoyi na computer wanda wasu daga cikinsu sun kunsi wadanda muka ambata a baya kmar na website ana hada su su zama na software ta kasa sune, HTML, CSS da Javascrip, ko kuma irinsu Java, C++ da sauransu.

Ita mnhajar computer ana iya kirkira ta da yarukan computer da dama wanda idan kana son cikakken bayani kana iya kara cikakken bincike akan hakan.

karanta: Yadda ake bude YouTube Channel

Kammalawa

Kamar dai yadda na ambata a baya computer programming yana da matukar mahimmanci kuma hanya ce wadda mutum idan ya dage yana iya dogara da kansa saboda yadda ake samun kudi da ta tana daya daga cikin fannonin computer da ake samu da su.