Skip to content
Home » Kayan aiki da mai YouTube Channel ke Bukata

Kayan aiki da mai YouTube Channel ke Bukata

Kamar yadda a baya dai mukayi bayani a baya game da YouTube da yadda ake bude youtube channel to a yau zamu yi maka bayani akan wasu muhimma kayan aiki da mai youtube channel yake bukatar ya mallake su.

Wadannan abubuwa wanda zan ambata inshallahu indai kayi kokarin samun su idan na samu ne ko kuma ka iya su zaka sha mamaki akan yadda zaka ga ka gara samun subscribers da kuma yan kallo wanda zasu taimaka ma channel dinka  ta habbaka sosai.

kayan aikin da mai youtube ke bukata

Kayan Aikin YouTube channel

Kamar yadda ka sani cewar a YouTube dai ana dora mashi bidiyoyi ne wanda mtane da yawa a fadin duniya zasu iya gani a cikin wayar hannun su ko kuma ta hanyar amfani da computer su kalla.

Kuma kafin su kalli kowace video a youtube kasani cewar sai sun sayi data ko kuma dole ne suyia amfani da internet wato yanar gizo kafin su shiga a youtube.

Karanta: Yadda ake Connecting din Computer da Internet

A dalilin haka ne kafin ka daura wata bidiyo a matsayinka na mai channel a youtube ka tabbata ingantacciya ce ka dauke ta da kyau ka kuma kyara ta saboda wadanda zasu kalla in ba haka ba kaga ana kushe bidiyonka da kuma comment marar amfani a kasanta wanda illar hakan yake ja yan kallon su ragu.

A fannin wadannan kayan aikin zan raba su zuwa gida biyu ne akwai wadanda na fili ne akwai kuma wadanda softwares ne download dinsu zakayi a cikin computer dinka ko kuma wayar hannun ka, a baya munyi yadda ake Download da install din software kana iya dubawa.

Da farko bari mu fara da wadanda suke a ke ganinsu fili wanda zaka yi amfani da su.

Abubuwan aiki na fili

wadannan kayan aiki sune wadanda zasu taimaka maka wajen daukar bidiyo wadda kake son ka dora ta a youtube channel wanda yan kallon ka zasu kalla kuma ya danganta ga yanayin kudinka da kuma yadda ka dauki abun da mahimmaci amma dai ga su kamar haka zan lissafo su tare da bayani.

kayan aikin da da mai youtube channel yake bukata na gani a fili

  • Camera
  • Waya
  • Ear Piece
  • Microphone
  • Abun dora camera(triport)
  • Computer

Wadannan abubuwan dana ambata a sama kana da bukatar su musamman ma idan aka ce kana da kudin da zaka iya sayensu.

Duk da dai cewar idan kana matsayin dan koyo zaka ga kana amfani da waya wajen daukar hoto to amma akwai bukatar ka samu triport koda karami ne na waya idan kuma a fannin camera ne sai ka samu na camera babba.

Sai kuma idan mukayi magana kan abubuwan sauti wanda suka hada da microphone na magana  ko kuma kayi amfani da ear piece saboda wasu ear piece din musamman manya suna da mouse na daukar magana.

Su dadin abubuwan sauti kamar su ear piece shine yana taimakawa sosai wajen graya maganar da kake yi a cikin bidiyonka ba kmar idan baka sa shi ba zaka ji maganar tana yin karar iska amma idan kayi amfani da su zaka ga sun taimka maka wajen samun sauti mai kyau.

Karanta: Hanyoyi 5 da Ake Samun Kudi da su a YouTube

Abu na gaba itace computer wadda yana da kyau ace kana da ilimin computer ma’ana ina nufin ka koyi computer yadda zaka yi amfani da ita saboda tana da matukar amfani sosai domin da ita zaka yi amfani ka rinka gyara bidiyoyin da zaka dora a channel din taka.

Karanta : Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su

Amma fa ba dole sai ka sayi computer zaka iya kyara bidiyo ba a’a ko ta hanay amfani da wayar ka zaka iya yi musamman idan babu halin hakan.

Daga nan kuma abubuwa na gaba kamar yadda na fara ambata maka a farko sai wadanda zaka iya saukewa a cikin wayarka ko kuma computer din ka.

Abubuwan aiki na Softwares

softwayoyin da mai youtube ke bukata

Bayan wadancen abubuwan da muka ambata wadanda zaka iya sawowa sai kuma fanni na biyu wanda sukuma yawanci download din su zakayi kawai ko da dai zaka sawo ba a fili ake ganin su ba zaka aje su ne a cikin wayar ka ko kuma computer dinka.

Ga kuma abubuwan suma zani lissafa maka su kamar haka daya bayan daya tare da bayaninsu.

  • Video editor
  • Screen recoder
  • Audio editor da sauransu.

video editor tana matukar taka rawa sosai wajen inganta maka bidiyoyin ka da kuma gyara su yadda yan kallo szasu ji dadin kallon bidiyoyin da kake dorawa a koda yaushe.

Muna da kala kalar video editor amma ga misalin wasu daga cikinsu kamar filmorago da kuma kine master suna da matukar kyau da kuma kayan gyara bidiyo kuma kana iya downloading dinsu a cikin computer dinka ko kuma wayr ka, suna da software da kuma android app.

Sai kuma idan mukayi magana a fanninin screem recorders shi gaskiya ba kowane mai youtube channel ne yake da bukatar su ba domin su wasu softwayoyi ne wanda zaka iya nadar ko recording din abunda kake yi a cikin computer dinka ko kuma wayar hannun ka.

Idan kawai daukar bidiyoyi kawai zaka yi ba yare da recording ko koya wasu abubuwa da ya shafi waya ba ko kuma computer ba kada bukatar su kuma misalansu sun haba da bandicam, screen recorder for android da sauransu.

Daga nan kuma sai Audio editor itama dai kamar screen frecorde ce ya danganta idan kana da wasu audios wanda kake bukatar ka gyara kafin ka daura su a cikin youtube channel dinka sai ka yi download dinsu suna taimakawa sosai suma.

Kammalawa

A karshe dai kamar yadda na fadi maka cewar kafin ka daura video a youtube ka tabbatar da ingancin ta da kuma kayi tunani akan yadda zata burge masu kallo yadda koda youtube ya bada recommend dinta watau ya kara ma wadanda basu yi subscribe a channel dinka ita ba zasu koma subscribers.

Sukuma wadanda suke subsrcibers dinka yadda zaka rike su shi rika maka like da comment wanda hakan zai taimaka maka sosai wajen samun kudi a youtube channel dinka, a nan nazi karshe ga mai tamabaya ko karin bayani yayi a comment section dake kasa.