Skip to content
Home » Bayani akan Bude Kamfani domin dogaro da kai

Bayani akan Bude Kamfani domin dogaro da kai

Kamar yadda kake gani yawancin kasashen da suka cigaba zaka ga cewar suna kamfanunnuka da yawa ne bawai dogara sukayi da aikin gwamnati ba kamar yadda kashashe wadanda basu cigaba ba sukeyi, to a nan inshallahu zamuyi bayani akan abubuwan da ya kunsa da yadda zaka fara naka.

Kamfani da abunda ya shafe shi

Mi ake nufi da Kamfani?

Idan akace kamfani kalma ce wadda a turance ake rubuta ta a matsayin company wadda tana nufin taron mutane da suke yin abu ko kuma suke kokarin aiwatar da abubuwan da suke son su cimma burikansu.

A fannin kasuwanci ma haka yake komin yawan ma’aikatan ka idan ba su son su taimaka maka ka cimma muradinka na bude shi to an samu matsala sosai saboda zakayi ta wahala ne wanda kuma wadannan ba su ne abokan aikin ka ba kwatakwata.

Don haka dole ka canza su zamu kara magana akan abokan yinshi  a gaba inshallahu yanzu bari muga amfanin sa fiiye da aiki.

Karanta : Samun Kudi: Kasuwanci guda 10 wanda aka fi saurin samun kudi da su

Shin yana da Bambanci da sana’a?

Eh tabbas kamfani yana da bambanci sosai da sana”a saboda shi ya ta’alaka ne akan kirkira sabon abu wanda da babu shi a cen baya.

Ko kuma koda akwai abun zaka yi kokari kaga wace hanya ce zaka bi ka canza abun ta kirkiro abunda zai burge mutane tare da inganta fannin da ka dauka .

Amfanin kamfani fiye da aiki

Bude masana’antar ka ta kanka ta fiye maka sosai akan ka tsaya kana yima wani aiki musamman idan kana da halin hakan saboda  kowane irin aiki kake indai ba gashin kanka kake ba to kamar bauta ce kake yi.

Ga wasu daga cikin aamfaninsa fiye da aiki.

  • Samun kudi wadanda ba’a iya cewa an kididdige yawansu a lokaci lokaci
  • Taimakama mutane su samu aikin yi wanda zai rage yawan zaman banza
  • Zama a cikin yanaci
  • Samun karin haske(experiance) akan yadda kasuwanci yake.

Matakan Budewa

A nan kuma inshallahu zamu yi bayani tare kawo wasu muhimman matakan da zaka bi domin kaga ka fara bude kamafin naka koda karami ne domin ai dama daga karami ne ake koakin tafiya zuwa babba.

Mataki na Farko 1

Ka tsaya kayi tunani mi ka iya kuma mi kake da sha’awar yi a duniya wannan tabbas shine abu na farko wanda zaka fara yima kanka, saboda shi duk abunda ranka yake so kafi jure mashi akan wanda ranka baya so.

Kuma shi kamfani yana da kyau kasan cewa yana daukar tsawon lokaci a rayuwar mutum wanda mutumin nan yana kokarin kirkira ko canza yanayin yadda wani abu yake ko kuma ya kawo sabo to kaga akwai batun sa kafi da lokaci sosai hadi da sha’awar abunda ake son yi.

Mataki na Biyu 2

Mataki na Biyu zsai ka tsaya kaga cikin wadannan abubuwan da kake da sha’awar yi wane ne mutane suke da bukata akai ko kuma suke son ka warware masu wata matsalar da ke addabar su.

Domin ta hanyar warware matasalar muatne ce kawai ake samun kudi wannan ita ce kaidar kudi sai ka yima wani abu wanda yanji dadi ya biyaka.

To da ka fahimci inda suke da matsala sai ka fara tunanin hanyoyin da za ka bi domin ganin ka warware matsalar tasu yadda zasu ji dadi kaga ka maida su customers dinka kenan wato masu sayayya a wajenka.

Mataki na Ukku 3

Bayan kayi tunani akan abubuwan da na ambata a sama to a nan bangaren ne fa zaka fara tsara yadda zaka fara hadi kamfaninka idan akwai bukatar bincike ina zaka samu ilimin in kuma a’a sai ka nemo shi ina ne zaka nemo shi.

Kuma a nan ne zaka hada team wato mutanen da zasu goya maka baya domin ka cimma burinka na aiwatar da shi kamfanin da kake son ka yi.

Karanta : Kasuwanci: Yadda ake fara kasuwanci da karamin jari

Team wato wadanda zasu taimaka maka wajen gina kamfaninka suna da matukar amfani kuma suna taimakawa wajen gyaruwar kamfani ko wargajewar sa saboda haka sai ka samu mutane nagartattu kuma kaima dole ne sai kasan yadda zaka zanna da mutane ka yi mu’amala da su yadda ya dace.