Skip to content
Home » Yadda Zaka Bude Kamfanin Abunda Ya Shafi ko Abun Sha Abinci a Nigeria

Yadda Zaka Bude Kamfanin Abunda Ya Shafi ko Abun Sha Abinci a Nigeria

Bude Kamfani abu ne mai matukar kyau kuma ana samu da shi musamman abunda ake yawan amfani da shi a kullun wanda ake ci ko kuma ake sha ka gyara kasuwan ka maida shi a leda, gwangwani ko kuma kwali ya fito a kimar kamafani ana samun kudi sosai.

Sai dai kafin ka samu damar bude irin wadannan kamfunnan ya kamata ka san wani abu da kuma wasu dokoin abunda ya shafi bude kasuwanci a Nigeria wanda sune zamu yi magana akan su a cikin wannan post din inshallah.

Bayanin Bude Kamfanin Abunda ya Shafi Ci da Sha

Bude Kamfani shima kasuwanci ne wanda mutum zai shiga yana da kyau ya tsaya yayi tunanin mi zai yi wanda zai ja hankalin mutane wanda ake cinsa ko kuma shansa.

Kuma kamar yadda na fada a baya irin wadannan kamfunnan sunfi samun kudi saboda kullun dole ne mutum ya ci ko kuma ya saha shiyasa kafiun ka shiga kasuwan zaka tsaya ka duba shin sabon abu zan kawo koko kyara ne nikeson kawowa a inda naga akwai matsala ba’ayi yadda ya kamata.

Gyarawa daz kawatawa gami da sauki shi ke jawo mutane su so abunda kake kuma suna ba wasu shawarar su sya ma ma’ana suna tallata maka hajarka bada saninka ba.

Karanta: 

Hanyoyin 5 da Suke Taimakawa Wajen Maida Karamin kasuwanci Zuwa Kamfani

Abubuwan da ke Haska Hajar Karamin Kasuwanci su maida shi Kamfani

Matakan da ake bi

Ga wasu matakai da zaka bi kafin ka bude kowane kasuwanci a Nigeria da ya shafi abunda za’a ci ko kuma za;la sha.

Tsara Kasuwancin

Kowane irn kasuwanci da zaka fara kafin ka fara shi an son ya zaman acewar an tsara komai ma’ana ka tsarea yadda zaka gudanar da shi wanda shine ake kira a turance da Business Plan.

Tsarin kasuwanci yana taimakwa sosai saboda ta hanyar shi ne kawai zaka iya fahimtar ina kasuwancinka ya dosa, suwaye customimi masu saye kuma suwaye kuke rige rige a irin kasuwancin kuma ya zaka fi su.

Bayan haka kuma ta hanyar hakane zaka fahimci wane tsari zakayi ma kasuwancin yadda zai tafi a farko da kuma abunda ake son cimmawa a nan gaba duk ta shi ne ake ganewa.

dama komai a duniya yana son tsari to shima kasuwancin da aka tsara yafi tafiya yadda ya kamata fiye da wanda yake tafiya kara zube ba wani tsari

Registration Na NAFDAC

Abu na gaba kuma shine register da samun dama daga NAFDAC wadda kungiya ce da ke kula da kasuwanci ko kamfanonin da ake kokarin kafawa a Nigeria da suke sarrafa abinci ko kuma abun sha ko kuma suke hada magani.

Bude kamfani ba tare da izininsu ba matsala ce wadda kasuwanci zai iya fuskanta indai dan adam na cin abun saboda duk yadda abun ya girma idan suka waiwayo ana yin asara kuma mutum in bai bi sannu ba yaje ga hukuma.

Hakan yana faruwa ne musamman man ma mutum ya fara a samu matsala ko wasu suyi rashin lafiya ko mutuwa ko wani abu da ya sahfi irin wannan ta sanadiyyar mutum don haka yana da kyau kayi register da su kana iya karanrata bayanansua a sahafinsu na NAFDAC.

Mallakar CAC Number

Mallakar lambar CAC nada matukar mahimmanci saboda da ita ne mutum zaya yi samu cikakkiyar shedar kasuwancinsa a Nigeria.

Yana da kyau kasuwancinka a ce yana da wannan lamabar saboda idan kayi la’akari ko tallabi, rance ko wani samun jari da gwamnati take badawa dole saida ita wanda baya da ita kusan baya cikin lissafi saboda haka tana matukar mahimmanci kayi ma kasuwancinka registration nata.

Kulawa

Abu na gaba shine kualawa kowane na’uin kasuwanci yana son kulawa musamman ma ga wannan da muke magana aknsa dole sai an kula sosai saboda abunda mutane da yawa zasu sa ne a cikinsu.

Kulawa ta shafi daga tsaftar kayan masarufi, ynayin tsaftar ma’aikata da kiyaye masu hakkin su saboda kaima kada suyi maka wasa.

Sai kuma tsaftace muhallin saboda gudan cututtuka da ke iya shafar abun wanda ana iya yada ma mtane da yawa da ba’a ma san iya adadinsu ba.

Karanta: kamfanin Biredi da yadda ake kasuwancinsa