Skip to content
Home » Abubuwan da ke Haska Hajar Karamin Kasuwanci su maida shi Kamfani

Abubuwan da ke Haska Hajar Karamin Kasuwanci su maida shi Kamfani

Akwai wasu muhimman abubuwa wanda idan karamin dan kasuwa yana amfani da su a wajen hajarsa da yake hadawa ko saidawa yake haska kimarsa a wajen masu sayen katansa wanda zasu maida hajar kamar ta kamfani.

A cikin wannan post din inshallahu zamuyi duba akansu da kuma yadda suke da matukar tasiri ga yan kasuwa wajen taimaka masu su habbaka kasuwar su.

Saboda Mi Karamin Kasuwanci ke son komawqa kamfani?

Kowane karamin dan kasuwa yana son katramin kasuwancinsa ya zamana a ce shima wata rana ya girma ya zama babban kamfani wanda ma’aikata da yawa suke aiki a cikinsa kuma karkashin kulawarsa.

bayani akan maida hajar karamin kasuwanci zuwa na kamfani

To amma su kuma hajojin kamfani ko kuma kayan da suke kerawa suna da wasu halaye wanda ya sha bamban da wadanda ba su ba wato kananan masana’antu.

Haskawar da hajar take yi ita ke sa  kamfanin yayi suna kuma mutane a koina suna iya gane abubuwan da suke yi saboda wannan abubuwan.

Yadda zan baka misalin irinsu su shine kamar logon ceminti na dangote duk wanda ya ganshi sai ya gane a kasashen da su ke saida siminti a fadin africa.

Karanta:

Samun kudi Cikaken Bayani Akanshi

Hanyoyin 5 da Suke Taimakawa Wajen Maida Karamin kasuwanci Zuwa Kamfani

Abubuwan da ke maida karami Babba

maida karami babba

Akwai abubuwa da dama da da ka gansu zasu fahimtar da kai cewa wannnan babbn kamfani ne kuma idan kana da karamin kasuwancinka kaima zaka so a ce ka girmama shi.

Da farko bari in lissafo wasu muhimmai da ke nunawa kafin bayani akansu.

  • Tambarin Kasuwanci
  • Sticker
  • Take
  • kaloli
  • Rufe Hajar

Wadannan abubuwan da kaga na ambata a sama idan ka tsaya ka yi tunani a kan su zakaga duk wani babban kasuwanci da ya kai matakin tsayayyen kamfani yana da da su.

Karanta:

Addua ko Wuridin Samun Kudi

Muhimman Abubuwan da suke Taimakawa wajen samun Nasara a Kasuwanci

Tambarin Kasuwanci

Duk wani ko wata babbar masana’anta da ka gani a duniya yan da wannan abun wato shine tambarinsa ko kuma ince logo a turance kenan.

zakaga duk abubuwan hajar da suka hada ko suke saidawa suna sa tambarinsu saboda hakan yake sa masu sayayya a wajensu su sansu su san kayansu koda daga nesa ne da sun gani.

Tambari na da matukar mahimmanci kuma duk kasuwancin da ke da shi baka hada shi da wanda baya da shi a fannin girma kwata-kwata.

Sticker

Sticker ko ince abun likawa a saman haja nada matukar mahimmaci kuma yana taimakawa wajen fahimtar abunda hajar ta kunsa kuma da yadda za’a yi amfani da abun idan na sarrafaw ne ko kuma amfani.

Shiyasa kamfunna suke amfanu da ita a duk kayan da suka ga sun hada su domin fahimtar da masu saye, kuma da karin tallata hajara su gami da bada adireshin da suke domin a zo wajensu ko kuma a tuntube su.

Take

wannan ma daya daga cikin abubuwan wanda da zaran ka gansu yana nuna ma da gaske masu abun suke kuma suna son girmamama kasuwancinsu.

yadda take yake shine yana ba customin ka bayani kan cewa ga abunda kullun kuke ma aiki kuke son ku cimmawa misalin sa shine  taken kamfani MTN shine evry were you go wato koina ka je.

kaga suna bayanin yadda suke kokari domin kwantar da hanaklin customin su su samu yarda a wajen su ta huddodin kasuwanci.

Rufe Hajar

rufe haja

Rufe haja wanda aturance ake cema packejing yana nuna cewar ba karamin dan kasuwa bane ba kai koda cikin daki kake hada abun misalinsu shine kwali, leda da sauransu.

ko kai idan kayi tunanin zaka ga hajar da ka saya a rufe tafi kima a wajenka bisa ga wadda aka sama a bakar leada wadda kowa da kowa yake sa kayansa.

kaloli

kala nada matukar amfani kuma ita ke nuna wannan kamfani kaza ne idan aka hada ta da tambari domin kusan tare suke tafiya daya abokin daya ne.

Duk kasuwancin ka da kake son ka girmama to ka zabi kala daya ko biyu ko ukku mafi yawanci amfi tsayawa a hakan wasu ma kala guda daya ce rak misali kalar MTN shine dorowa.

Sa kala yana kara tallata hajarka da sabunta ma masu saye kamfanin ka duk lokacin da suka ga abubuwan ka da suke da ita hakan na zaunar musu a zuciya.