Skip to content
Home ┬╗ Kayan Noma: Inda zaka samu kayan Hydroponics noman da ake batare da kasa ba

Kayan Noma: Inda zaka samu kayan Hydroponics noman da ake batare da kasa ba

 To kamar yadda a post din mu na baya mukayi bayani akan samfarin noma na zamani wanda ake yi batare da amfani da kaasa ba kawai ya kunshi sinadarai, haske ko na fitila sai robar da zata rike shufkar wanda ake kiya da hydroponics a turance kana iaya karanta fasahar shi wannan noman.

To bayan rubutun da mukayi kuma mukayi alkawarin kawo inda idan kana da sha’awar fara shi zaka sayi kayan yinsa.

A dalilin haka ne yau inshallahu zamu yi maku bayani akan inda zaka iya sayen kayan irin wannan noman na zamani tareda bada shawara akan yadda zaka saye su a cikin kwanciyar hankali.

Abubuwan da yakamata ka sani kafin sayen kayan Noman

Shi irin wannan noma yana bukatar Bincike da fahimtar yadda yake, to kar ka damu Alhamdulillah yanzu idana zaka duba YouTube turawa sun yi bayani akan irin wannan noma sosai a cikin bidiyoyi da dama.

Kana iya duba su don samun haske sosai da fajimtar yadda abun yake.

kuma yana da kyau ace kana da ilimin sayayya a online ka iya sayen abu koda dan karami ne a online domin inda ake saida kayan kusan mafi akasari bama a cikin Nigeria bane.

Amma idan kasan hannunka ka iya sayayya har kaya su zoma garinku wadanda ka saya dahga cikin watarka ay shikenan bakada damuwa.

Manyan Wuraren da Ake sayen Kayan

Kamar yadda na ambata a baya inda ake sayen wadannan kayan zaka saye su ne a online daga wasu kamfanunnuka sanannu  na kasashen wajea wanda gasu kamar haka:-

Mnayan Wensite da zaka ziyarta

Aliexpress

Aliexpress

Aliexpress babbar website ce wadda ake yo odar kaya daga kasar china su zomaka har nigeria zaka biya kudi bayan ka saya ta hanyar application dinsu ko kuma ta website dinsu.
kana iya shiga sai ka rubuta Hydroponics zakaga kayan da yawa sai ka zaba.

Amazon

Idan ka iya sayayya a babban shagon online na America amazon to lafiya lau sdhima ana sayen kaya a cen amma nafi baka shawara ka saya a Akiexpress saboda sunfi dadin aiki kuma su dama don duka mutanen duniya suke saida kayan.
Misali idan baka iya sayen kaya a online ba ga wani brush nan mai amfani da wutar lantarki mai sauki jeka saya kaga
kaga hotom shi a sama fa linik dinda zaka bi nan https://s.click.aliexpress.com/e/_AsBELI