Samun Kudi da Computer: Abubuwan da ya kamata ka iya na fannin computer domin dogaro da kai

 Kamar yadda a baya mun yi bayani akan yadda ake sayen computer mai lafiya to a wannan post sai mukaga ya kamata mu kawo ma masu karatu bayani game da fannoni daban daban na na’ura mai kwakwalwa tare da fayyace amfaninsu da kuma yadda za’a samu abun dogaro da su.

Gabatarwa Game da Na’ura mai kwakwalwa(Computer)

Da farko dai mai karatu ya kamata ya fahimta cewa itafa computer abu ce mai amfanin gaske ba wai kamar yadda wasu daga cikin mutanenmu suka dauke ta ba misali kana iya ganin mutum ya sai laptop amma baya komai sai kallace kallace kila ma baida aikin yi.

Hakan bai kamata ba ya kamata ace ka iya wasu abubuwa masu amfaniwanda bayan samun abun yi ko gaba zasu taimakeka wannan ya shafi duka maza da mata.

Ga wasu daga Cikin fannoni da na zakulo wadanda suke da matukar amfani.

Fannonin da ya kamata ka Iya a Computer

A nan zaniyi tskaci kadan game da su akwai littafin PDF da muke shiryawa game bukata sai ya yunyube mu.
Daga cikin fannoni masu mahimmaci sosai wanda ya kamata ka iya gasu kamar haka.
  • Fannin Programin(Ba Computer Umurni)
  • Fannin Office
  • Fannin Editting
  • Fannin Design

Fannin Programming

Wannan fannin nada matukar amfani saboda kusan wadanda suka fi kowa samun kudi a duniya a fannin computer Idan ana lissafa su dole asa masana ba komfuta umurni.
Domin kwarewar mutum a wannan fanni nasa kamfanunnuka su neme shi a duk inda yake a fadin duniya saboda abu ne mai matukar amfani albashinsa wasu kamfanoni a naira yana wuce million 5 ko goma.
Kuma har ila yau abun ba a nan ya tsaya ba mutum zai iya Kirkira wani abu wanda zai samu kudi dashi misali software wadda mutane musamman turawa suna sayen license dinta a Dollar.

Karanta

Fannin Office 

Idan aka ambaci fannin office ana nufin iya aikin da computer a aikace aikacen office misali rubutu typing, Kidaya ta lambobi da yawa, iya hada Presentations wato fafofin gabatarwa da dai sauransu.
hoton spreed sheet wadda ake buga data dayawa a karamin lokaci

kaga wannan fanni na da amfani kuma kamar yadda a baya mukayi bayani akan kasuwancin Printing da Photocopy munyi bayani akan cewa sai mutum ya iya softwayoyi na rubutu, to duk hakane idan ka kware a wannan fannin kana iya kama shago ka fara kasuwancinka cikin sauki.