Skip to content
Home » Sana’ar Design na Printing da Yadda Ake Fara ta

Sana’ar Design na Printing da Yadda Ake Fara ta

Sana’ar zane zane na abubuwan da ake design dinsu na daya daga cikin sana’oin zamani da ake samun kudi da su sosai saboda yawan abubuwan da ake yi na irinsu bukukuwa da kuma harkokin da suka danganci siyasa.

To Inshallahu a yau zamu duba muhimman abuwan da wannan sana’a ta kunsa da kuma yadda zaka fara yinta Ka samu hanyar dogaro da kanka, saboda mutane da yawa suna samun alheri da ita.

sana'ar printind da design

Yanayin sana’a Design na printing

Ita dai wannan sana’a ta kunshi abubuwa da yawa wanda ake yinsu da computer, kaga akwai bukatar kafin ka fara ta ya zamamto cewar ka iya computer.

Kamar yadda a baya mukayi bayani akan fannonin computer wanda ya kamata ka iya to a cikin su sai ka iya zane wato ka san yadda zakyi amfani da manhajar zane koda daya ce ta computer.

Domin da shine zaka zana ko kuma ka tsara yadda aikin da aka baka kamar calender ko kuma invitation zai iya kasancewa.

Da farko ga wasu muhimman abubuwan da kake da bukatar mallaka ko iyawa.

Karanta:

Yadda ake koyon Computer da kuma Bayani akan Ilimin Computer

Sana’ar Dinki da yadda zaka fara ta

Abubuwan da kake bukata kafin fara sana’ar

 • Computer
 • Iya manhajar zane ta computer
 • Sanin yanayin papper da abubuwan amfani
 • Printers
 • Scanner

Manhajojin da ake amfani da su

To bayan ka mallaki wadannan abubuwa kamar yadda na fada maka dole ne sai ka iya computer musamman a fannin zane, kuma akwai wasu manhajojin da masu wannan sana’ a suka fi yawan amfani da su a koda yaushe.

Karanta: Abubuwa 5 da suke sa dan koyon computer ya kware

Corel Draw

Corel draw indai a fannin design ne tayi kaurin suna sosai wajen zane da tsara abubuwa su fito sosai kamar su logo, invitation,poster, certificate da kuma calender.

koyon corel draw

Iya amfani da wannan manhaja ba karamin abu ne mai amfani saboda kusan duk abubuwan da na ambata maka su a baya kana iya yinsu da ita har ma da karin wasu fiye da su.

Manhaja ce ta zane wadda bayan kayi kana iya fiddo shi a formate na Jpg, jpeg da kuma png kuma kana iya converting din normal png na zane zuwa Bitmap yadda zai fito kamar hoto.

Amfanin hakan shine a lokacin da kayi printing a papper zaka ga yayi kyau kamar ba zane ba yayi kama da hoto sosai.

Corel drawa ta game duniya kana iya koyonta a fadin Internet ta irinsu Bidiyoyin Youtube da sauransu tare da kuma kana iya downloading sample na zane kawai ka dora naka a sama ka fidda.

Inkscape

Inkscape itama wata manhajar software ce wadda ake design da ita kuma kana iya koyonta ko a internet ne.

Ita ma dai kamar yadda corel take ana yin abubuwan zane da ake kira da vector kusan ita tafi corel drawa ma karfin yin vector drawing saboda kusan kamfaninta domin hakan suka yita.

Kana iya fiddo design wanda kayi na invitations ko kuma wasu ko kuma wasu ayyuka na kalendoji lafiya lau kuma kana iya sa hoto ka gyara shi yadda zai hau da aikin  da kake.

zane acomputer

Wane abun burgew ga wannan software din shine ita license  dinta kyauta ne kana iya downloading dinta daga website dinsu kayi installinga a windows, linux ko kuma a mac operating sysm ba tare da an nemi ka biya ko sisi ba kuma ba tare da ance ka sa lisece key ba.

Abubuwan da zaka iya yi

A lokacinda ka tsunduma a cikin irin wannan sana’a kaga ka samu sana’ar hannu wadda kana iya yin abubuwa daban daban ga custominka wanda ga su kamar haka zan ambata maka su.

Amma kafin nan yana da kyau ka sani cewar koda ka gaza fidda wani abu kamar kaga baka da irin wata printer zuwa ake wajen manyan masu printing suna fidda su kamar misali a ce banner ko kuma poster.

Ga lissafin abubuwan

 • Invitation
 • poster
 • Banner
 • Memo
 • Littafi
 • Sticker da sauransu

Karanta: Sana’ar Rubutun Littafi da Bayani akan Marubuta

Kasuwancin Application da yadda ya Habbaka a Duniya

Yanayin yadda zaka fara

Kamar dai yadda ka sani a duniya ba wani kasuwanci ko kuma acxe wata sana’a wadda zaka ba tare da kudin farawa ba ko yaya ne, to ita ma wannan sana’ar haka take saidai ya danganta kana iya farawa da kudi kamar naira Dubu 300.akalla.

Dalilin da yasa na cemaka haka saboda yanayin abubuwan da za ka saya na kayan aiki da kuma yanayin wurin da zaka kama na shago a matasyin haya.

kana iya ceewa wai wannan kudi sunyi yawa wannan a matakin a ce kana son ka zanna da kanka ne wanda har printer ka mallaka amman idan kawai kana so ka fara  amatsayin karami kana iya daga computer sai kmaramar printer idan babban aiki ya zo sa ka tafi wajen manyan masu yin printing.

Amafnin ita wannan sana’a shine kana iya ganin aikin dubu 3000 ko ma dubu goma ko kuma fiye da hakan ya zomaka a lokaci daya kaga kuma abu ne ba wanda za’a ce yana iya rubewa ba.

karanta: Yadda zaka fara Sana’ar Saida Data

Kammalawa

Kamar yadda na fada dai ita kafin ka fara wannan sana’a kana da bukatar a ce ka iya computer a musamman a fannin zane kai harma fannin office akwai bukatar a ce ka lakanceshi sodsai.

kuma idan ka sa himma don wai ka iya zane a cikin computer wata daya zuwa biyu ka kware ba mai wai a ce ka iya ba kawai ya danganta ga yadda ka dauki abun da kuma da yadda himmarka take.