You are currently viewing Kasuwanci: Hanyoyin Samun kudi masu saukin ga Dalibai

Kasuwanci: Hanyoyin Samun kudi masu saukin ga Dalibai

Samun KudiIdan akayi maganar Dalibi an san a koda yaushe yana bukace da kudi amma karatu ya sha mashi kai kuma kullun yana kokarin habbaka kanshi, to idan kana son ka samu kudi alhalin kana kartu ka zo wajen inshallah, a dalilin mahimmancin kasuwansi ne a yau inshallahu zamu yi magana akan yadda dalibi zai fara kasuwancin sa mai sauki wanda kuma ana samun kudi da shi.

A baya munyi post akan Fara Kasuwanci da karamin jari dakuma wasu post din game da wasu naw’ukan sanao’i kamara yadda ake hada man shafawa to wadannan dama makamantansu amma a yau zamu duba akan wasu masu sauki da karamin kudi sai a fara su kuma a ci riba.

Kasuwancin Dalibai 

To tunda shi dalibi zai dauki masu sauki wanda ba sai ya ta ayyuka da yawa ba saboda karatunsa kada ya tsaida shi ga wasu dana tato kamar haka.

Saida Data

Saida Data ba karamin kasuwanciu bane bama ga dalibai ba kawai a’a kowa ma saboda kowa indai yana da babbar waya yana da bukatar data donmin yayi wani abu inma a yanar gizo ko kuma a kafofin sada zumunta na Internet.

Kasuwancin Data
Zaka iya fara saida datar ka da karamin jari musamman a nan Gida Nigeria da naira dubu Goma kana iya fara wannan kasuwanci ka samu kudi, in ka fara sai ka ringa watsawa ta kafafin sada zumunta kamar whattsapp status.

Domin zamanin yanzu akwai yadda zaka habbaka kasuwancin ka a cin sauki musamman zuwan kafar sada zumunta.

Ta Hanyar Yanar Gizo

A matsayinka na dalibi yana da kyau a ce ka iya Computer yadda ake Browsing a computer da sauran duk yadda ake shiga Internet, Domin sanin wannan shi zai baka damar lalubo hanyoyin da zaka samu kudi ta hanyar Bincike.

A Internet kana iya Bude website ko kuma ka bude YouTube channel ka samu kudi inma ka saida wani abu a ciki ko kuma ka sa tallar kamfanunnuka a ciki wanda ana samun kudade sosai ta wannan hanyar.


Yin Ayyuka a Online

Online ana samun kudi sosai domin a online kana iya samun aiki kayi a biya ka, idan kana dalibi kuma kana bukatar wasu kudin kashewa kana iya zuwa wuraren da ake yin aiki a biya.

Akwai aikin da ake cema Freelance Work wanda aiki ne zakayi ma wani ya biya ka kamr idan kana da fasahar zane wato ka iya zane ko kuma ka iya programming koma kai kana iya rubuta article da sauransu to akwao shafukan yanar gizo kamar su Freelancer.com, Fivver da sauransu idan kayi ma wani aiki zai  iyaka
This Post Has 4 Comments

Comments are closed.