Skip to content
Home » Sana’ar Communication da Abubuwan da Suka Shafe ta

Sana’ar Communication da Abubuwan da Suka Shafe ta

Sana’ar communication tana daya daga cikin sana’oin zamani da suka zo daga baya wanda a da cen ba sana’oin gargajiya bane, kuma lokacin yanzu din ma da aka same su ana samun kudi da su yadda ya kamata idan Allah ya taimaki mutum yayi abunda da ya dace kuma ya inganta tare da bi da hakuri.

A cikin wannan post din namu na yau zamuyi magana akanta ne da kuma abubuwan da suka shafi ita wannan sana’a saboda samun haske kafin fara taka sana’ar.

Bayani Akan Sana’ar Communication

Ita wannan na’uni sana’a ta ta’a laka ne musamman akan abubuwan da suka shafi kayan wayar hannu wato salulu, abuwan da suka shafi saida kayan kara mata kamar su air piece, screen gard, charger dama sauran abubuwan da zasu taimaka a wajen gyara ta.

Kamar yadda kowace sana’a zakja ga tana da abunda dole sai da shi to itama tana da shi kumamafi akasarin abubuwan da ya shafe ta ta dogara ne da abubuwan wuta musamman mu a irin kasashen mu inda babu tsayayyar wuta kaga kana da bukatar sayen generator wanda zai rike ka.

To a cikinta ita kanata akwai abubuwan da ta kunsa wanda shi mai son fara wannan sana’ar ya kamata ya sani cewar ana hadawa da su a cikin kasuwancin wanda ga zamu sune.

Karanta:

Yadda ake fara kasuwanci da karamin jari

Hanyoyin Samun kudi masu saukin ga Dalibai

Abubuwan da ta kunsa

Kamar yadda zaka ga cikin wata sana’ar  zakaga ta kunshi wasu kananun abub uwan da za’a iya saidawa a tare da ita to itama wannan sana’ar ta communucationa kwai abubuwan da ake hada ta da wasu ma sune jigon kasuwancin gabakidaya .

Sana'ar communication

kayan Waya

A cikin wannan sana’ar koma ince ginshikin ta shine saida kayan waya wadanada ake sama wayar ko kuma ake makala su daga baya wanda yanzu kusan kowa da ya sayi waya yana neman su kuma bayan yan watanni ma zaka ga an kara neman su saboda  yawan amfani da ake yi da su kullun kayan sun hada da.

  • Ear piece
  • Charger
  • Battery
  • Screen Guard
  • Memory
  • Bluetooth da sauransu

Karanta:

Kasuwanci guda 10 wanda aka fi saurin samun kudi da su

Bayani akan Dalibai da yadda zasu dogara da kansu

Chargi

A dayan bangaren kuma mai irn wannan kasuwancin yana iya hadawa da yin chargi a matsayin hanyar da zata iya taimaka mashi wajen samun kudi musamman a inda ke da karancin wuta ko kuma ma babu ita gabakidaya.

Chargin a sana’ar yana kawo kudi sosai kuma yana kara yawan kawo muatane a shagon, sai dai amma wani hanzari ba gudu ba kafin ka fara chargi a kasuwancinka yana da kyau ka kula sosai saboda kayan muatane ne zaka amsa ka je wajen masu sana’ar printing su hada maka da an kawo ka ba mutum.

Saida Data da kati

Wani abu kuma da zaka iya karawa a cikin wannan sana’ar shine kara hadawa da saida Data da kuma katin waya, saboda yawancin masu zuwa sayayya ko kuma ince customominka masu waya ne.

To saida data da kati baya da wani wahala kuma a baya mun koya yadda ake yinta da kuma abubuwan da ya shafi ita kanata sana’ar dama yadda zaka fara taka tafiyar kana iya dubawa.

Kaaranta:

Yadda zaka fara Sana’ar Saida Data

Gyaran Waya

Abu na gaba kuma wanda ake hadawa da shi shine gyaran wayoyin mutane amma a wannan yanayin yawancin sai shago ya habbaka ya kasance akwai masu aiki fiye da daya saboda gudun matsala amma ya danganta ga yanayin yadda kasuwar wajen take.

gayaran waya yana bukatar a ce mutum ya iya iya saboda ba wanda ya ke son ya kawo wayarsa ayi masa shirme kuma yana bukatar kula saboda ana iya kawo maka kayan sata ko abubuwan rigima.

Downloading

Wasu a cikin wannan sana’ar suna hadawa da tura abuwa da suka shafi softawre, Bidiyoyi, audiyoyi da sauransu wanda hakan ma yana taimakawa wajen samun kudin shiga a kasywancin.

Amma yawanci abubuwan a cikin computer suke don haka akwai bukata koma ince dole ne ya kasance kana da fahimta computer koda kuwa baka zama kwararre ba a cikinta

Karanta:

Yadda ake koyon Computer da kuma Bayani akan Ilimin Computer

Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su