Skip to content
Home » CIKAKKEN BAYANI AKAN SAMUN KUDI ONLINE TA FREELANCING

CIKAKKEN BAYANI AKAN SAMUN KUDI ONLINE TA FREELANCING

Koyon aikin freelandcing aiki online yana da matukar amfani saosai saboda yanayin yadda ayuka suka yawaita a fadin duniya, a dalilin haka ne a cikin wannan post din inshallahu zamu yi bayani akan mi ake nufi da freelancing abubuwan da ta kunsa da kuma yadda zaka iya fara ta.

Mi ake nufi da Freelancing?

Freelancing yana nufin yin aiki a biya mutum kudin aikin shi a wani lokac in da aka kidya za’a biya shi, wanda yake irin wannan aikin ana kiranshi da freelancer.

A irin wannan aikin ana iya cema mutum yayi aikin da duk awa zaa bashi naira kaza misali duk awa 7000 ko kuma idan kasashen waje ne ace duk awa $50 kokuma ace kayi aikin idan ka kammala shi zaa baka kudin jimilla kaza.

Yadda ake yinsa

Kamar yadda na ambata dai abaya hanya ce ta samun kudi kuma a onine ne yanzu kusan ya koma ba kamar da ba da daewa da babu cigaban Yanar Gizo (Internet)

Yadda ke yinsa shine ana amfani ne da computer ko kuma waya haka misali inda idan mutum aka bashi ya fara zai yi aikin a biyashi yanayin yadda aikin yake misali ace zane haka ko kuma a ce yayi rubutu kalama dubu kaza akan naira kaza ko kuma a ce yayi abu aiki kaza duk awa zaa biya shi naira kaza yadai danganta ga yanayin yadda aikin ya kasance.

Karanta:

Fasahar ChatGPT da Yadda take

Fasahar ChatGPT da Yadda take

Data Card: Yadda Ake Fara Kasuwancin Data Card

Misalan Ayuka da ake Ba yan freelancing

  • Rubutu (content writting)
  • Graphic Design (zane)
  • Web development
  • Application Development
  • Translation
  • Transcription
  • Book writting

Yadda ake farawa

Kafin ka fara freelancing akwai bukatar ace ka fara iya wani abu ma’ana ka fara iya wata sana’a ko wani skill saboda da shine zaka yi amfani ka yima clent ko wanda yazo ayi masa aikin aikin shiyasa akwai bukatar ka iya wani abu a karpn farko kusan ma ana son ace ka kware a fannin abun yadda za’a fi biyanka kudi sosai.

Iyawarka ce kesa idan kayi apply ko biddin ma’ana ka nemi aikin su baka musamman ma ace ka nuna ayyukan da ka gudanar ko kayi ma wasu a baya haka wanda zai baka aiki ke a nuna mashi cewa akwai aikin da akayi a baya.

Akwai bukatar kasa kafafen sada zumuntar ka kamar su facebook instagram musamman ma irinsu linkedin wanda don aikin daman akayisu asamar da aiki kuma a nemi aiki.

Daga nan kuma sai hanyar biyan kudi idan yan kasashen waje ne zasu biya ka a dollar kana iya mallaka domicilliary account, ko kuma ka rika amfani da irinsu payoneer wanda yana nufin kamar ka mallaki banki ne a kasar Ameri a sama kudinka kayi withdraw ka cire su.

Kafafen da zakayi register domin farawa

Akwai wurare da dama online da ake samun ayyuka amma ga wasu sannanu da kasuwar abunce inda aka tara su.

wadannan dama sauransu idan kayi bincike zaka ga cewa duka akwai masu sanya ayyuka akwai kuma masu amsa a biyasu, wasu ma daga cikinsu kamar fivver zaka sa ko kayi posting abunda zakayi kace a Naira kaza zakayi a biya ka wani yace ayi masa.

Bayani Game da Kafafen

Karanta:

Yadda ake Gano Waya Bayan ta Bace ko an Sace ta

Kasuwancin Saida Gidaje da yadda ake Samun Kudi da shi