Skip to content
Home » Fasahar ChatGPT da Yadda take

Fasahar ChatGPT da Yadda take

Kamar yadda labarai suka karade duniya a kwanannan masana sun samu damar kirkiro wata sabuwar fasaha wadda suka kira ta da chatGPT, wanda zaka tambayeshi koma minene a cikin wayarka ya baka amsa kgamsashiya mai amfani.

yanayin yadda abun yake bada amsa ya ja hankalin mutanenen suniya sosai saboda abun ya kai ko lissafi ka sa mashi yana iya lissafa maka shi lafiya sanadiyar anyi amfanui da fasahar Artificial inteligence.

Cikin makallar mu ta yau inshallahu zamuyi bayani akan yadda yake da ma kuma kara bayanin akan fasahar artificial inteligence yadda za’a fahinceta sosai.

bayani akan fasahar chat gpt da yadda takeG

Minene ChatGPT

Kamar yadda mujallar wikipedia ta bada ChatGPT yadda aka hada kalmomin a turance suna nufin (Chat Generative Pre-trained Transformer) ma’ana da hausa kamar ace abun hiri wanda aka haifar ta hanyar horaswa.

Manhaja ce dai wadda aka yita a matsayin chatbot ma’ana abunda zaka tambaya ya baka amsa, to a nan yana da bambanci da a ce kamar google domin yanayin yadda zai baka amsar kamar mutum ne.

Yadda abun kuwa yake shine  an bashi horo sosai yadda zai bada amsa mai ma’na mai alaka da abunda ake so misali idan aka tambayeshi miye rayuwa zai baka amsa mai ma’ana sosai ta yanayin yadda aka sama masa ma’anarta.

Yanayin karfin shi ya kai kana iya sama shi tambaya ta lissafi ya yi fidda maka amsa kai tsaye wanda masana suka ga cewa akwai matsala musamman ga dalibai a lokacin jarabawa su shiga da waya kenan.

Karanta: 

Bayani game da sama computer tunani kamar na mutum

Bayani akan Samuwar Gas daga Shara ko Bola

Tarihinsa

Da dadewa mutane suna ta jaraba yin mahajpji masu kaifin basira irin chatGPT amma ba’a samu wadanda suka yi irinsa sai a shekarar da ta 2022.

A wannan lokaci ne masana daga wani kamfani da ake kira da OpenAI suka samu damar kaddamar da shi a 30 ga watan Nuwamba na shekarar 2022 kuma bayan kaddamarwa bada jimawa ba kamfanin yanayin kudinsa suka haura dala biliyan 29.

Karin bayani akan fasahar machine learning

Abubuwan da suka shafi Artificial inteligence da machine learning sune suke ta sama yanzu a fadin duniya saboda yanayin yadda suke taimakawa sosai wajen habbaka harkokin kasuwanci, noma, kiwon lafiya, kimiyya da fasaha, ilimi da ma sauran bangarori na rayuwar dan adam.

Machine learning wata kimiyya ce da ake amfani da ita wajen horar da na’ura mai kwakwalwa ta koyi wani abu daga datar da aka sama ta yadda zata fahimceta bayan nan ta fidda mafita mai amfani wadda ta daga darajarta ko wadda ta maida ta fiye da da.

Misali manhajjin da suke amfani da wannan fasaha zakaga cewar kamar kamfanin sabulu misali yana samun kudi naira 1000 duk satyi ko dubu 2000 wani lokacin to zata iya lissafin tabada mafita a an da shekara ukku yanayin kudin da za;a samu kuma ta fidda riba da kuma faduwa.

Ma’ana dai ita wannan kimiyya tana nufio horara da na’ura yadda zatayi yunani irin na mutum idan ta tashi bada amsa ko bada mafita akan wata matsala.

Ciagaba sosai ta irin wadannnan abubuwa yakai ta ana hada manyan wanda sune ake cemea artificial inteligence su sunfi machine learnin wanda nayi bayani a sama su kuma kamar robot yana iya yimaka aikin da kake so ko kuma irinsu mota mai tuka kanta zaka samata ida zaka ta kaika kai tsaye tana kaucema duk wani hadarin da zai samu kamar dai dan adam ke tukawa.

Karanta: 

Yadda Ake Fara Kasuwancin Data Card

Yadda Ake cike Application na Aiki a online da kanka

Bayani akan Sana’ar Canjin Kudi