Skip to content
Home » Kamshin Girki: Abubuwa 10 da Ke Sa Kamshi da Dandanon Girki da Kuma Kyansa

Kamshin Girki: Abubuwa 10 da Ke Sa Kamshi da Dandanon Girki da Kuma Kyansa

Mace dole saida girki, kuma shi kansa iyawa ne, shin kina sa kayan kamshi na girki wanda zasu kara dandanon girki da kuma gyara launinsa, idan ba haka ba to akwai gyara musamman a wajen maigida don kada abincin waje ya burge sa.

Yana da kyau kisani cewa Mace tana zama tauraruwar girki ne idan ta san yadda zata sa abunda ta girka a tukunya ka kansance mai kyau, kamshi da kuma dadi hakan yana kara mata kima sosai a wajen mutane musamman ma mai gida.

Abubuwan da ke sa kamshi da dandanon girki

Abubuwan da Ke sa kamshin Girki

Akwai abubuwa da dama da suke taimakawa abincin da aka girka yayi kamshi yayi kyau kuma yayi dadi wanda  mafi yawancinsu sun kunshi kayan lambu, kayan kamshi da kuma da kanti.

sanya su a cikin sanwar da za’a yi yana sanya ta ta dauki hankullan masu ci ta yadda zasu yi santi kuma abun kulawa ga wadannan abubuwan yana kyau ki sani cewa ba’a zuba su suyi yawa tyadda zasu gundiri mai ci.

Domin duk wani abunda yayi yawa  a Duniya kuma yana komawa marar dadi akwai wadanda kadan ake sonsu sosai akwai madaidata, akawai wadanda za’a sanya yadda zasu fito sosai.

Samun daidaita a tsakaninsu ne yake haifar da kamshin abiunci daga nesa da kuma dandano mai dadi ga wadanda zasu ci abincin, ba tare da jan lokaci ba ga wasu muhimmai daga cikinsu.

Karanta: YADDA AKE GIRKI COMPLETE SANWA YADDA ZANI GIRKA ABINCI KALA KALA

Citta

Citta na da matukar amfani kuma rtana sanya abinci ya zama mai kamshi sosai yadda zai yi dandano mai dadi ga masu ci shioyasa ake son amare dama wadanda suka dade su rika yawan amfani da ita.

Amfanin citta a girki

Bayan kamshi da take sawa tana da amfani sosai ga lafiya a jikin mutum saboda tana maganin abubuwan da suka shafi lalurar sanyi, rashin saurin narkewar abinci da sauran su.

Daga cikin amfaninta a girki tana sa abinci yayi saurin narkewa a cikin ciki ga uwar hanji kuma tana magance ciwuka kamar ciwon ciki.

Karanta: Maganin Ciwon Ciki Cikin Karamin Lokaci

Karanfani

Karamfani wani abu ne baki karami wanda yake da kamshi da yaji kamar yanayin su  citta yana da matukar amfani sosai kuma yana taka rawa wakjen sanya kamshi a cikin abinci da kuma abun sha.

Karanfani yana magunguna kala daban daban da suka shafi ciki kuma yana taimakwa shima wajen samun saukin narkewara abinci.

Bayan haka a fannini magani kuma yana taimakwa wajen maganin ciwon sanyi da kuma mura ko ince tari idana ana shan shayinsa hade da citta.

Karanta: Maganin Tari da Mura da sanyin Maza da Mata

Man Gyada

A faannin mai kuma ana son mata su rika amfani da man gyada saboda yadda yake da kamshi shi kansa kuma duk lokacin da akayi sanwa da man gyada zakaji tana gamshi sosai.

Kuma mai ne wanda baya kwanciya shiyasa binciken da masana ssukayi daga baya suka ce yafi man kwantilora na jarka saboda shi yana bacci yanayin kitsen da za’a samu a man gyada bai kai wancen ba.

Gyadar Miya

Gyadar miya wata yar icce ce karama mai kama da gyada ana bareta yadda ake bare  gyada a fiddo dandan dan dai ita tafi gyada tauri.

Dan da ke ciki shi keda kamshi kuma tana sanya kamshi sosai a cikin girki wanda haka ne ma ya sa masu hada kori suke yawan sanya ta saboda karfinta na kamshi.

Sai dai a kula ita tana da kamshi mai karfi sai asan yadda ya kamata a sanyata saboda yadda abincin zai tafi yadda ya dace ba tare da isar mai ci ba kuma a daka ta sosai don gudun kar mai ci ya rika karo da ita a baki bata narke ba batada dadin dandano a baki hakanan saboda kamshinta.

Cabeji

Kabeji abu ne daga cikin kayan ganye na lambu wanda suke gyara abinci kuma suke kara masa kyau da kuma gandano mai dadi,

Ana zuaba shi a cikin yadda ba zai narke gabadaya ba yafi dadi ya kasance dai ya dahu amma bai rididdige ba yadda ba’a ganinsa sosai.

Domin kwalliya da kuma haska abinci ana iya dora shi a saman abinci kusan da yawa a sa shi kamar yadda ake xuba latas don kara haska kyan abincin.

Yana da sinadarai da yawa na vitamins wanda suke taimakama jiki kuma suke hara lafiyar jiki da kuma kare cututtuka da ke iya samun dan Adam.

Tafarnuwa

Tafarnuwa tana daga cikin katan kamshi na sanyi wanda suke tare da su citta da karamfani, tun zamani dayawa da suka gabata mutane suna amfani da ita saboda kamshinta.

Ba ‘a iya kamshi kawai ta tsaya ba har ma wajen sa dandano mai kyau na abinci duk tana karawa, kuma bugu da kari tana taimakawa wajen lafiya musamman wajen fannin lumfashi, jini da sauransu.

Karanta: Yadda uwar gida zatayi Fried rice dinta a saukake

Kurkur

Kurkur yana da matukar amfani a wajen mata musamman yadda suka sanshi ta fannin kwalliya da gyaran fuska da fata to ba nan kawai ya tsaya ba ana sa shi a cikin abinci kuma yana gyara abinci ko miya ya sa dandano da kuma kala har ma kamshi.

Sai dai a kula idan za’a zuba kurkura a tabbata ya daku saboda idan kacishi a cikin abinci a matsayin babba wasu launin baya masu dadi sai a kula shi kamshinsa da kalar sa yafi burge masu cin abincia.

Albasa

Idan kana maganar abinda cikin kayan miya yake sanya kamshi da kuma canza gdandanon abinci gabakidaya to kazo wajen albasa saboda tana sauya launi tasa abinci yayi dadi sosai.

Amfanin albasa wajen kamshin abinci

Bayan haka kuma tana da mahimmaci sosai a fannin lafiyar jikin dan adam domin yanayin sinadaran da take da su na vitamins wanda suke kara lafiya a cikin jikin mutum.

Karanta: Yadda ake Spring Rolls Cikakken Bayani Tare Da Hotuna

Thyme

Thym kayan kamshi ne kuma yana da kyau a kula da sanya shi yana canza launin kalar abinci kuma ya zanja yanayin kamshinsa sosai zuwa dandano mai dadi.,

Thyme abu ne wanda baya da tsada sosai kuma gashi da matukar taka rawa a fannin girki.

Karanta: yadda ake Spring rolls da meat pie

Kori

Abua na gaba kuma shine kori wanda kala kala ne, kori hadin kayan kamshine da yawa kamar wadanda muka ambata a baya su gyadar miya, kurkur da sauransu dama wadanda bamu ambata su ba.

Kori idana ana sa shi a cikin abinci kusan ya maye mafi yawancin abubuwan da muka mabta a baya, yana taka rawa wajen canza dandano, launi da kuma kamshin girki.

Dudda kala biyu na gida da kuma na kanti amma ya hada abubuwa da yawa musammam dai na gidan wanda yake da kayan miya na kamshi da sauransu.

Karanta: Yadda ake soya Fara

Tarugu

Tarugun yan adaga cikin dangin kayan miya wanda yake da yazi don haka sai an kula akwai lokacin da kuma yajinsa yake karanta wanda akan dan sa da yawa.

Girkin da aka sanya ma tarugu da wanda ba’a sanya mawa ba kwatakwata bama a hada su ta fannin dandano da kuma kamshi, shiyasa musamman masu abincin saidawa basu wasa da shi.