A yau zamu yi magana Akan nau’ikan abincin Hausawa na gargajiya wanda tun da dadewa ana cinsu a kasar hausa wanda wasu daga cikin abincin gargajiya na hausawa har yanzu ana cinsu Duk da Zuwan zamani.
Tun kafin zuwan zamani bahaushe ba kamar wasu yaruka bane yana da abinci sa na kansa wanda yake yi kamar yadda akwai sana’oin gargajiya tuni suma.
Table of Contents
Mi ake Nufi da Abincin Gargajiya?
Abincin gargajiya yana nufin wasu nau’uka na abinci wanda tun kafin zuwan zamani ana girka su domin a ci.
Wadannan irin nau’kan abincin suna zama daya daga cikin abun da suke zama ado na al’adar alumomi a fadin duniya.
Mafi akasari ire-iren abincin gargajiya zaka ga idan zamani ya zo suna canza launi ko kuma kaga yan al’ummar suna kin su musamman matasa wanda hakan wani lokacin ke jawo bacewarsu idan al’umma batada karfi sosai.
Ire- iren su
A kasar hausa muna da abinci na gargajiya ikamar haka:mn
- Tuwo da miya
- Fura
- Fate
- Alala
- Dan- wake
- Dambu
- kwado
- Waina
- Alkubus
- Kunu
- Kwokwo
- Kosai
Misalan abincin da muka ambata a sama sun rabu gida biyu akwai na ci akwai na sha.
Abincin da Ake ci
Tuwo da Miya
ko shakka babu tuwo yana daya daga cikin sanannun abincin hausawa na gargajiya, wanda indai kai bahaushe ne to ka sanshi, kuma yana daga cikin abiuncin da ake cinsa.
Muna da misalan Tuwo kala-kala kamar Tuwon Masara, Tuwon gero, Tuwon dawa da sauransu mun koya yadda ake tuwo a baya.
Alala
Alala itama nau’in abincin da ake ci ce wadda an dade ana yinta, ana sarrafa wake ne inda ake hada shi da kayan hadi su bada alala.
Kwado
Shima kwado yana daya daga cikin abincin alada na hausawa wanda suka dade suna yinsa.
Yadda kwado yake shine ana dafa ganyaye ne sai a samu abin hadinsu kamar kuli ko kuma daddawa a hada a yamustse misalin kwado sun hada da;
Akwai kwadon, zogala, na rama, na tafasa, na ungududu da sauransu
Kosai
Ko shakka babu kosai na daya daga cikin abincin gargajiya na hausawa wanda a yanayi ja ne ana dankwalashi da yaji.
Kosai wani abinci ne wanda ake hadawa da Wake inda za’a markada wake sai a hada shi da kayan hadi, bayan haka sai a samu man kyada a samu kasko a soya shi a ciki.
Dambu
Damabu abinci ne wanda ake dade ana yinsa akwai irinsu dambun masara, dambun alkama da sauransu wanda za’a barza tsaba ne sai a dafa ta a hada da kayan hadi.
Abincin da ake sha
Fura
Fura wani na’uin abincin da ake hadawa wane da gero wanda da farko sai an hada dawo.
Daga baya kuma sai a dama dawon da Ruwa a sha ana zuba nonon dabbobi ga masu bukatar hakan.
Kwokwo
Kwokwo wani abun sha ne wanda hausawa suka cika shansa da safe a matsayin abun da za’ayi kalaci da shi.
kwokwo Fara ne a launi kuma ana hada shine da gero, mafi akasari ma an fi shansa da zafi da safe.
Kammalawa
A kasar hausa kamar yadda na gabata da bayani suma suna da nau’in abincinsu na gargajiya wanda suke ci tun asali ba wai kawai na zamani suka dogara da shi ba.
Author Profile
Latest entries
- Sana'o'iJanuary 6, 2025Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a
- Kiwon LafiyaJanuary 3, 2025Maganin da Ganyen Parsely yake da suka hada da sanayi, cancer da sauransu
- KasuwanciJanuary 1, 2025Hanyoyi 5 na Juya Kudi da Suke da Riba mai Yawa
- Sana'o'iJanuary 1, 2025Gyaran Waaya: Yadda ake Fara Sana’ar Gyaran Waya