Skip to content
Home » Yadda ake soya Fara

Yadda ake soya Fara

Soya fara nada saukin yi, a  cikin wannan post din inshallahu zamuyi magana akan yadda ake soyawa tare da bayanan matakan kamar yadda muka saba yi ga kowane nau’in abinci.

To kafin mu fara bayani akan yadda zaki soya, yana da kyau ki san san wani abu ita fara akwai mai rai wadda da aka kamo maki da ranta zaki soya ta akwai kuma marar rai wadda ake awna ta a buhunna ana saida ta a kasuwanni.

yadda ake soya fara

Kayan hadin soya fara

  • fara
  • maia
  • yaji
  • magi
  • gishiri
  • kayan kamshi kamar su thyme da korry da sauransu

Yadda ake ma fara mai rai

Da farko abunda ya kamta kiyi idan tana da ranta kafin ki fara saya farar zaki daura ruwan zafi a cikin tukunya ki zafka  farin a cikin ruwan zafi domin su daina motsi gabakidaya.

Daga nan kuma bayan sun daina motsi sai ki juye ta ki canza ruwan zafin ki sa wasu ruwan, a wannan ruwan na biyu zaki gyara ta ne ki fidda kai daban, jiki da kuma kallema har da ma gashin da ke a bayanta daman shi wannan kusan dole ma ne ki fidda shi.

Byan nan kuma sai ki samu ruwa ki dauraye ta ki sata ta  a wani wuri mai fadi ta bushe a rana ko kuma wajen da take samun iska yadda ruwan jikinta zai dan tsane.

hoton fara wadda zaa soya

Rabewa tsakanin kallema a nan hoton kallemA NE

 

Yadda ake soyawa

A wajen soyawar zaki samu tukunyar ki mai kyau sai ki dora ta a saman wuta, bayan nan kuma sai ki dakko farar amma yana da kyau a wajen gyarawar a ce kin rabe tsakaninin jikin farar da kuma kallema da kaia.

Daga nan ki fara soya jikin saboda yafi wahalar soyawa idan kamar bayan kin zuba shi yayi rabin soyuwan sai ki kawo sauran kallemar da kai ki hada su su soyu tare gabakidaya kina yi kina juyawa yadda zai soyu da kyau.

Karanta:

Yadda Ake Hada Cin-Cin mai Gurus Gurus

Yadda aKe hada Alkaki a saukake

 

SOYEN JIKIN FARA

Hoton jikin fara wanda aka gyara shi kafin a soya shi a tukunya

Yadda ake ma wadda batada rai

ita kawai bayan kin fara gyara ta kin bambance tsakanin kafa, kai da kuma jikin sai ki samu ruwa mai zafi kidan zafka ta a ciki yadda datti, hoda da duk wata kura wadda ta dangance ta zata rabu da ita sai ki sanya ta a cikin rana.

Bayan kin sa ta a cikin rana da kin ga ruwan jikin ta ya dan tsane haka sai ki dauko ta ki sata a tukunya ta ki samu kayan hadinki kamar mai ki sa a cikin tukunya tare da farar.

kar a manta ana tare da website din Hausawasite.com.ng ne wanda ta Al’ummar Hausa ce inda ake koyon abubuwa daban daban daga masana da dama a cikin harshen hausa musamman sana’oi don dogaro da kai  Domin kasancewa damu kana iya Rubuta Hausawa SIte a Google don samun sabbin rubuce – rubucenmu

ki fara soya jikin yadda soyen zai yi kyau sannan sai ki dauko sauran kayan kamshi kamar yadda muka ambata su a sama ki sanya su a cikin tukunya kina soyawa kina motsawa har ta soyu yadda ya kamta sosai

karanta:

Yadda ake Spring Rolls Cikakken Bayani Tare Da Hotuna

Hanyoyi da ake bi don adana Naman Sallah ya jima ana Amfani dashi

:

Kammalawa

Kamara yadda nayi bayani a wajen soya fara akwai abunda ya kamata a ringa kula wanda shine idan kika zuba ta duka, ma’ana jikin da kafar da kuma kan to zaki ga cewar kai da kafa sun yi saurin soyuwa sun bar jikin.

Amma yadda zaki magance wannan matsalar a cikin hanya mafi sauki shine ki fara zuba jikin ki soya shi ya fara soyuwa koda kamar rabi ne ko kusa da haka ko sannan jikin.

ko kuma ki saya su daban daban yadda zata yi dadin ci aamma da zaran kika zuba duka zaki ga ba kamar yadda in kika raba ba kina ma iya ganin sun kone kafin jikin ya fara soyuwa yadda ake so.

karanta :

Yadda Ake hada Alala mai Kwai a cikin matakan yi masu sauki yi

yadda ake Spring rolls da meat pie

Fanke: yadda ake hada fanke