Skip to content
Home » Yadda aKe hada Alkaki a saukake

Yadda aKe hada Alkaki a saukake

    

Yadda ake hada alkaki

 

 Yadda ake  hada Alkaki a saukake

Alkaki dai kamar yadda kowa ya sani yana daya daga fannin abinci wadanda ake cema snacks kuma daya ne daga cikin abuncin da ake amfani da alakma a matsayin babban abin sarrafawa, inda kamar wajen biki ko kuma ma hakanan a gida ana yin sa don a ci.

A dalilin haka ne a yau cikin yardar Allah zamu yi bayani akan yadda ake alkaki a saukake inda zamu lissafa kayan da ake sawowa a kasuwa wato kayan hadin da kuma matalkan da ake bi a wajen hada shi idande baa manta a baya ba mun kowa yadda ake hada cake inda muka koya shi kuma akwai Yadda ake alala Mai kwai in baa karanta ba ana iya dubawa suma.

kar a manta ana tare da website din Hausawasite.com.ng ne wanda ta Al’ummar Hausa ce inda ake koyon abubuwa daban daban daga masana da dama a cikin harshen hausa musamman sana’oi don dogaro da kai  Domin kasancewa damu kana iya Rubuta Hausawa SIte a Google don samun sabbin rubuce – rubucenmu

Kayan da ake hada Alkaki da su

  1. Alkama (Ba’a so a wanketa da ruwa).
  2. sugar
  3. Tsamiya
  4. Kanwa
  5. Mai
  Abubuwan da muka ambata a sama sune ake hada alkaki da su wanada ake son a samo ko kuma a sawo su a kasuwa saboda kusan dukkan su ba su da wahalar samu.

Karanta

yadda mace zata zama tauraruwar girki
yadda ake fried rice
yadda ake yamball

yadda ake alkaki

Yadda ake hadin kayan hada Alkaki

 Da farko dai za’a samu ita alkamar sai a bakace ta sannan bayan an yiu hakan sai a kai ta a wajen masu barji sai a barza ta ta sosai.

To bayan an barzata sai a sameta da daddare a zuba ,mata tsamiya a motsa su sosai su motsu sannan sai kuma a samu marfi a rufe kwabin da shi zuwa safe.

Da gari ya waye sai samu kanwa a zuba a cikin kwabin sai samu turmi a daka su ta yadda da kwabin alakmar da kuma kanwar su hade sosai.

Karanta: 

Kamshin Girki: Abubuwa 10 da Ke Sa Kamshi da Dandanon Girki da Kuma Kyansa

Girki Adon Mace: Kala-kalar Girki da yadda zaki kware akan kirki don shine adon mata

Fanke: yadda ake hada fanke

Daga nan kuma sai a dora mai a cikin kasko yayi zafi sai a rika zubawa ana soyawa har sai sun soyu sai a kwashe a sa a mazubi bayan an gama sai a samu suga a soyashi wasu ma har lemun tsami suke sawa sidan ya soyu yayi ruwa sai a zuba a cikin alkakin da aka soya sai a ci.

Wasu Daga cikin Amfanin da Alkali yake a Jiki

  • Yana kara gina jiki
  • Yana taimakawa wajen inganta karfin jikin mutum
  • Yana kara habbaka lafiyar mutum dalilin vitamins musamman a ruwan suga idan aka sa lemon tsami
  • Abubuwa irin na alkama suna daga cikin abubuwan dake kara ma mata ni’ima.

Kammalawa

To a nan muka kawo karshen yadda ake hada alkaki sai a duba wasu sauran kayan girkin ko kuma na sanaoi domin amfana suma.

Idan akwai wata tambaya ko kuma wani karin bayani akan wannan post din ana iya yinsa a comment section da yake a nan kasa da mun duba muka gani zamo maido inshallahu mungode.