Fanke: yadda ake hada fanke

Yadda ake fanke

 

 

Assalamu alaikum kamar yadda take ya gabata zamu yi magana akan yadda ake hada fanke a cikin hanya mai sauki, wanda wannan post ne da ya ya kunshi kayah hadin fanke, yadda ake hadin kayan fanken da ma sauran mun yi shi ne bayan jerin post da dama da mukai a cikin wannan website mai albarka wato hausawasite.com.ng inda muke koya abubuwa da dama tun daga sana’oi, girki dama sauransu inda ire iren na girki sun  kundhi yadda ake springrolls da meat pie, irisu yadda ake fried rice, cin-cin da kuma yadda ake donouts dama sauransu in ba’a karanta su ba sai a karanta.
To ba tare da bata lokaci ba shidai fanke abinci nedaga cikin abincin hausawa wanda ake hada shi da filawa a ci a gida koma ma a rika yin sa don a saidama mutane.
Ko sana’ar fanke kanta ana samun kudi da ta saboda yawanci zaka/ki ga ana yawan cinsa a dalilin haka ne mai saida fanke zaku ga yana samun kudi kuma dama tana daya daga cikin sana’oi na hausa da akai ittifaki suna kawo kudi da sauri a dalilin duka kayan da ktum zai saya ba su da yawa kuma gashi abinda zai yi sai albarka.
 To kamar dai yadda muka saba a post din mu na baya kafin mu koya yadda ake abu sai mun lissafo skayan da ake amfani da su wanda za’a samo ko kuma a sawo a kauswa

kar a manta ana tare da website din Hausawasite.com.ng ne wanda ta Al’ummar Hausa ce inda ake koyon abubuwa daban daban daga masana da dama a cikin harshen hausa musamman sana’oi don dogaro da kai  Domin kasancewa damu kana iya Rubuta Hausawa SIte a Google don samun sabbin rubuce – rubucenmu

Kayan da ake sawowa a yi amfani da su don hada Fanke

1. Filawa 
2. Sugar
3. Gishiri
4. Mai
5. Yeast
6. Gishiri (kadan ga mai so)
7. Ruwa
To kayan da muka ambata su a sama sune ake hada fanke dasu yanzu kuma zamu tafi akan yadda ake hadin kayan fanke ko mayakan da ake hadawa don yin bayani akai.
 

Matakan da ake bi wajen hadin kayan fanke

Da farko dai a samu filawa mai kyau a kamar misa tiya sa a smu sugar a da yeast amma shin kamar cokali daya da  rabi ko kuma biyu idan ana so ya tashi sosai bayan an zuba su, shi kamar yeast din ana iya dan gauraya shi da ruwan dumi a farko yadda zai saurin tashi lokacin da aka zuba a cikin kwabin musamman a lokacin sanyi.

To bayan an hada filawa da sugar da kuma yeast din sai ana dan iya zuba gishiri dan kadan kamar rabin tea spoon  ga masu so dalilin shine yana bada wani test ne mai dadi yayin ci.

Daga nan kuma sai a kawo ruwa a zuba yadda kwabin zai yi laushi sosai a cigaba da bugawa wato ana motsawa  sosai yadda kayan zasu hade sosai.
Bayan ya motsu an buga shi da hannu sosai sai kuma a samo marfi a rufe kwabin kuma a sa shi a cikin rana dan   ya tashi da yayi minti ashirin zuwa talatin indai ya tashi ya danganta da ranar wajen ko yanayin zafin ranar to.
Kuma sai dora mai a samam kasko a rinka diba ana soyawa har sai fanken yayi ja ya soyu sai a kwashe shi a zuba cikin kula a ciki.
Karanta: 
 

A bubuwan da ya kamat musamman mata Su  Kiyayaye kafiun Girki

 
Wadannan abubuwa suna da kyau musamman ga mata su tsare don gyaruwar zaman gida
  • Tsafta
  • Yin Abinci da wuri
  • Yin mai dadi da inganci
  • Kiyaye kayan dandano kamar gishiri

Kammalawa dangane da Fanke

To Alhamdulullah mun zo karshen wannan post mai bayanin yadda ake fanke wanda keda tambaya kar aji komai a yi a wurin comment section da ke a kasa da mun gani mun maida inshallah.
Kuma har ila yau wannan website ta hausawasite.com.ng ,mai kokarin koyar da hausawa yadda ake hada abubuwa dama yadda ake kasuwanci daban daban mun yi post wanda ana iya karanta su kamar yadda ake hada man shafawa verselin, yadda ake sabulu da ma sauransu.