Table of Contents
Yadda Ake Hada Cin-Cin
To shi cin-cin kamar yadda aka sani yana daya daga cikin snacks wanda ana yawan cin shi bama al-ummar hausawa ba har ma sauran idan ba’a mantaba a wannan shafi mun koya yadda ake hada yadda ake hada fanke, alkaki, pizza, Donut da sauransu.
A wannan post din kuma muka ce bari mu kawo cin-cin musammam domin yan uwa mata.
To da farko dai zamu fara da lissafa kayan da ake bukata sannan sai mu tafi akan yadda ake hada shi
Kyan da ake Hada Cin Cin Dasu a Lissafe
- Filawa (rabin tiya)
- Mai (rabin gwangwani)
- kwai(daya)
- Backing Powder(Tea spoon )
- Yeast(rabin tea spoon)
- Butter(rabin ledder)
- Ruwa(rabin kofi amma ya danganta ga yadda ake so)
Ga yadda ake hada su kuma kamar haka.
Yadda ake Hadawa
Da farko dai za’a sa filawa da suga sai a motsa su tare, sai kuma a sa backing powder da yeast a motsa su shima daga nan kuma sai a kawo kwai, mai da kuma butter a cigaba da motsawa.
Za’a cigaba da motsawa ne har sai yayi curi haka wato dunkule mai tauri.
Daga nan sai a debi curin a mulmula shi sai a samu wuka a datsa kanana yadda ake son girman ya kasance, shikenan sai a zuba mai a cikin kasko a kunna wuta a dora man da yayi zafi sai a jefa cikin kaskon daga nan kuma dayayi kalar ja wato alamun soyuwa.
sai asauke a zuba a kula ko roba shikenan.
Author Profile

Latest entries
Kimiyya da FasahaSeptember 22, 2023Wuraren da Zaka Samu Kayan Kere-Keren da Kake Bukata
Wayar HannuJuly 17, 2023Yadda Ake Amfani da WPS Software
Wayar HannuJuly 4, 2023Yadda Zaka Zama Dillalin Yanar Gizo
Wayar HannuJuly 3, 2023Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin