Skip to content
Home » Girki Adon Mace: Kala-kalar Girki da yadda zaki kware akan kirki don shine adon mata

Girki Adon Mace: Kala-kalar Girki da yadda zaki kware akan kirki don shine adon mata

Girki ko shakka babu shine adon mace musamman ma a gidanta wadda ta yi aure tana da miji, saboda yana daya daga cikin abubuwan da ke sa a samu kwanciyar hankali a gida kiga kau ay girki ya zama adon mara.

To a dalilin haka ne a wannan post ko makallar inshallahu zamu yi magana akan wasu muhimman abubuwa wanda ko yace mace ta sani yadda zata inganta girkinta na zamani.

Duk da haka kuma zamu dan yi tsokaci akan wasu muhimman abubuwa da ke kara ma hakan armashi tare da bada misalin girke-girke kala-kala.

Girke-Girke

Nau’ikan Girki

Muna da kala- kala na abincin wanda hausawa suke na gargajiya tun kafin zuwan na zamani wanda a baya munyi magana akan ire-irensu.

Karanta: Abincin Hausawa: Ire-Iren Abincin Gargajiya na Hausawa

Ire-irensu sun rabu gida biyu akwai na ci akwai kuma na sha wanda shansu ake yi ya danganta a kullun ne ko kuma wani lokaci ne ga nauikan su kamar haka.

  • Fannin Abinci
  • Fannin abin sha
  • Fannin soyayyu (snacks)

Ga yadda suke da abubuwan da za’a kula dasu.

Fannin Abinci

Kalar abinci na ci

Wannan fanni ya ta’allaka ne da abubuwan da ake ci wanda yawanci dafasu ake musamman ta hanyar tafasa su da ruwa har su tsane.

Abubuwan da ya kamata a kiyaye akan su gasu kamar haka

Abubuwan Kiyayewa a fannin abinci

  • Kar a bari su kone
  • Kulawa da tsaftar wurin zubasu
  • Yawan kulawa da dan- danon su
  • kulawa da yanayin kamshinsu
  • Kula da rike yadda akayi yadda kullun za’a inganta su yadda na yau ya fi na jiya

Misalansu

Ga wasu daga cikin misalansu wanda yawancinsu munyi su anan kina iya duba su domin karantawa daya bayan daya sun hada da irnsu Tuwo, Frid Rice, Burabisko da sauransu.

Fannin Abubuwan sha

faninin abun sha

Fannin abin sha shima yana da matukar amfani saboda yana daya daga cikin abubuwan da ake son sha, iya shi na sa ya ado ga mace kamar yadda aka ce Girki adon mata.

Suma a wannan fanni na abubuwan sha yawancinsu za’a ce sun kunshi kayan sanyi ne kamar su sobo, kunun aya, Jinja da sauransu

Abubuwan Kiyayewa a fannin abin sha

  • Kulawa da dandano
  • kulawa da tsaftar kayan amfani kafin yinsu
  • kulawa da sasu waje mai sanyi saboda shan gaba don gudun tsami
  • Kulawa da launinsu yadda zasu burge.

Misalansu

Daga cikin misalansu sun hada da irinsu zobo, kunun aya, jinja  ga fannin masu sanyi kenan amma akwai abubuwan da ake sha masu zafi kamar kunu kwokwo da sauransu.

Fannin Soyayyu

Wannan fanni na ya kunshi kala-kalar girki ne amma wanda aka soya shi wanda yawanci ana amfani ne da kasko a soya irin wadannan naikan.

Kwarewa akan snacks ya kara ma mace ado da kuma kima awajen mijinta yadda zata shiga cikin jerin matan da ake masu ado da girki daga Girki adon mata, ga abubuwan da ya kamata ki kula.

Abubuwan Kiyayewa a soyayyu(snacks)

  • Tsaftar kayan suyar da inda za’a zuba
  • Shina abun na bukatar ya suyu sosai ko sama sama yakeso
  • kulawa da dandanonsa
  • kulawa da kamsinsa

karanta: YADDA AKE GIRKI COMPLETE SANWA YADDA ZANI GIRKA ABINCI KALA KALA

Misalansu

Daga cikin misalan abubuwan da ake soyayawa akwai irin su soya nama sai kuma akwai fannin su kayan kwalam din wato sanacks kamar su spring rols, cin-cin, pizza, donut da ma sauransu.