Skip to content
Home ┬╗ Yadda ake Spring Rolls Cikakken Bayani Tare Da Hotuna

Yadda ake Spring Rolls Cikakken Bayani Tare Da Hotuna

Yadda ake spring rolls nada sauki wanda kamar yadda kika sani yana daya daga cikin na;ikan abincin snacks, wanda yawanci indan mutum yana son ya hada wani abu wanda ya kunshi snacks dole ne sai ya hada da jigon kayan hadi filawa to inshallahu zamuyi bayani akan yadda ake hada spring gross zallanshi kamar yadda a baya muyi yadda ake hada spring ross da meat pie.

Kafin mu shiga ga yadda ake hadawar ga wani dan takaitaccen bayani akan spring rolls da kuma amfaninsa ajikin mutum da kuma lafiyarsa.

Minene Spring Rolls da kuma amfaninsa?

yadda ake spring rolls

matakan da ake be wajen hada yadda ake spring rolls

Kamar yadda na ambata asama yana daya daga cikin na’ukan abincin snacksa wanda hausawa suke ci abinci zamani ba Abincin Gargajiya ba.

Kuma ana hada shi ne da fulawa a launi kalar ruwan kasa ne wanda a ciki ake samashi kayan miya domin a gyara shi. a dandano yana da saukin ci ba tauri ba.

Amafaninsa ga lafiyar mutum kuma yana kara bada karfin jiki a sanadiyyar fulawa kuma akwai sinadarai navitamins wanda suke kara ma mutum lafiya kamar su Vitamin C.

Bari mu tyafi akan Kayan hada shi da kuma yadda ake hada shi.

Kayan Hada Shi

Ga kayan da ake bukatar a sawo a kawu kamar haka zan lissafa su daya bayan daya.

  • Fulawa
  • Mai
  • Kwai
  • Kabeji
  • Nama
  • Kyan kamshi(maggi,gishiri da kuma thyme)
  • Karas
  • Albasa

Yadda ake hadawa

Tunda mun lissafa kayan da ake bukata a sama ga bayani nan zan yi yadda zaki fahimta daki-daki yadda da kin tashi yi ba wahala.

Mataki na Farko

Zaki samu namanki mai kyau ki sai ki wanke shi sannan kuma sai ki samu tukunya ki dora shi a kan wuta ki dafa shio ya dafu sosai.

Bayan ya dafu sosai sai ki yanka shi kanana sai ki daka shi ko kuma ki samau blender kiyi blendin dinshi

Bayan haka kuma sai ki samu karas da kuma kabeji sai ki yanka su kanana, sai ki kuma kawo manki ki zuba a cikin kasko ki zuba su duka da naman, kabejin da kuma karas din duka sai ki zuba ki soya su su.

Kar ki manta ki sa gishiri da maggi da kuma kori a wajen soyawar kina motsawa amma kar ki bari su soyu sosai kadan ake so su soyu.

Mataki na Biyu

Bayan wannan a wannan mataki kuma sai ki sai ki samu fular ki ki kwaba ta ki samata kwai a ciki da kuma ruwa kidanyi mata damun laushi haka kamar zakiyi waina.

Daga nan kuma sai ki samu kasko ki rikka zuba mai kina soyawa kamar yadda ake waina daidai suyar waina yadda zatayi falan-falan haka.

Mataki na Ukku

Bayankin kinyi matakin dana ambata a sama sai ki dauko nama da abubuwan da kika soya shi a matakin farkon dana fadi.

Sai ki samu naman kina yabawa akan wannan filawa wadda kika soya kamar waina kina yabawa a saman ta kina nannadewa kamar tabarma.

Yadda zaki rufe bakin shine zaki samu kwai sai ki rika shfawa abakin filawar sine zai taimaka wajen like filawar yadda kayan baza su fito ba.

Mataki na Hudu

A wannan mataki kuma sai ki dauko kasko ki zuba mai acikinsa sai ki samu nadin da kikayi aa sama sai ki rinka zaubawa a ciki.

Zabi yimashi wara-wara yadda ba zai hade ba a wajen soyawar da ya soyu kuma sai ki safke ki samu wuri ki zuba si, shikenan.

Karanta:

Abincin Hausawa: Ire-Iren Abincin Gargajiya na Hausawa

Kala-kalar Girki da yadda zaki kware akan kirki don shine adon mata

YADDA AKE GIRKI COMPLETE SANWA YADDA ZANI GIRKA ABINCI KALA KALA

 

Kammalawa

Spring rolls dai kamar yadda muka yi bayani in afatan kin gane matakan yadda suke kuma da yadda ake yinsu, idan akwai wata tambaya ko kuma wani karin bayani kina iy yinshi a kasa wajen comment section.