Yadda Ake hada Alala mai Kwai a cikin matakan yi masu sauki yi

 Yadda Ake hada Alala mai Kwai a cikin matakan yi masu sauki yi


     To Alala daidaya ce daga cikin nau’oin abincin hausawa wanda aka sani kuma yadda ake alala ba wani abu ba ne mai wahala kusan kowa ma yana iya yin sa in ya iya kuma yana da kayan hadin Alalar, wanda wannan shine kusan dalilin da yasa muka rubuta a cikin wannan website din wato hausawasite.com.ng yadda ake hada alala da kuma kayan hadin da ake hadawa.

To kamar dai yadda muka saba a wannan website din muna koya abubuwa ne da dama inda har Yadda ake hada Alkaki mun koya shi kuma komai zamu koya kafin mu koya shi sai mun fara zana kayan hadin shi kanan mu shiga a yadda ake hadawa, to itama alala haka zamu yi inshallahu.

Yadda ake hada alala ko hada alallaZamu fara da zayyana kayan da za’a sawo a kasuwa ko kuma a nemo sannan kuma mu tafi akan yadda ake hadin kyan da ake hada alalar da su.

  1. Yadda ake gika abinci  Mai dadi kala kala duba su suma

1. yadda ake sunasur

2.  yadda ake tsire

3. yadda ake samosa

4. yadda ake yamball

5. yadda ake hada Doungnut


6. yadda ake cake

Kayan da ake hada alala dasu

  1. Wake
  2. Alayyahu
  3. Attarugu
  4. Curry
  5. Kwai
  6. Albasa
  7. Maggi
  8. Mai


    To tunda mun zayyana kayan da ake hada alala dasu bari mu tafi zuwa yadda ake hada kayan hadin alalar da su don yi tare da kuma bayanin su dalla dalla don mai karatu ya gane sosai.


Yadda za’a Hada Kayan 


To kamar yadda dai muka ambata abaya ga yadda ake hada kayan ko kuma matakan da ake bi don hadin alala.

To akaron farko dai a samu wake a surfa shi sosai sannan bayan an surfa waken sai a sa attarugu da albasa a markadesu sasai su markadu.

To bayan an yi hakan sai kuma a zuba ruwan dumi a kwaba kamar dai yanayin kaurin da ake so alalar ta kasance.

To daga nan kuma sai a maggi, curry ko kuma da kayan kamshin da ake da su da kuma mai sannan kuma sai a yanka albasa.

To baccin an zuba wadancen kayan sa a smu alayyahu a wanke sa sosai a yanka shi yadda ake so a cikin alalar sai a zuba sai a daukon kwai a fasa tunda alalar mai kwai za’a yi , daga nan kuma sai a samo kifi a sulalashi a zuba a cikin kayan hadin ko kuma kwabin.

 To fa daga fa nan kusan an kusa gama alala abunda ya rage shine a dauko leda ko kuma wani gwangwani azuba kwabin a samo tukunya mai tsafta a dora ta a saman wuta a dafa shi har sai ya dafu, sai a samo Kwano a zuba in ya dafu a ci.

A  takaice


      To alhamdulillah alala ta kamala mun yi bayani akan yadda ake alala da kuma yadda ake hada kayan hadinta kuma mun yi bayani akan steps din sosai wanda bai fahimta ta ba ko bata fahimta ba yayi tambaya a sahen comment wanda ke a kasa ayi masa bayani mun gode, Kai/ke ya kun hda tayi!!!