Skip to content
Home » Hada Game: Yadda Zaka Kirkira Game da Kanka

Hada Game: Yadda Zaka Kirkira Game da Kanka

Shin ka taba tunanin yadda Video Games suke yadda ake hada Games da Kuma ya kasuwar su take a fadin duniya, tabbas kau games suna samun kudi sosai a fadin duniya ga kuma bayanin yadda ake kirkira Games din.

Kamar yadda a baya munyi bayani sosai akan koyon computer duk mai yawan bibiyar mu a wannan shafi mai albarka na Hausawa Site ya san akqwai post dayawa na kimiyya da fasaha musamman abubuwan da suka shafi computer.

Karanta: Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su

To a yau zamu yi bayani akan Game yadda ake hada da idan ka tashi muhimman abubuwan da ya kamata a koya domin ka hada taka game din.

yadda ake hada game

Micece Game Kuma mi ta Kunsa?

Game dai wasa ne wanda ake yi kuma kowace alumma tana yinsa kamaer muma a nan kasar hausa yadda muke da wasannin gargajiya haka kowace kasa tana da na gargajiya da kuma na zamani.

Sai dai a zuwan cigaba d a ak samu na kimiyya da fasaha ta canza fasalin yadda abubuwan suke kasancewa gabadaya har fannin wasannin na games.

Dalilin cigaban da aka samu suma komfutoci da wayoyin hannu aka hada masu wasannin da ake kira a turance da Video games.

Wasannin nan sai dai a kula akwai wanda lafiya kayi su baci karo da adddini ba akwai kuma masu matsala kamar wanda ake sa badala, da kuma abubuwan zanen surar mutum, abubuwan sha ka kadede kade.

Karanta: Yadda ake hada Android Application

Suwaye ke Kirkira Su

Wadanda suke hada games na video sune game developers a turance, mutane ne da ke da kwarewa a fannin programming wato yaren computer zasu iya ba computer umurni ta hanyar yarenta wanda ake kira programming langue a turance.

koyon kirkira game

Karanta: Koyon Programming na Computer cikakken bayani akan yaren computer

Ya Ake Samun Kudi da Ita

Wadan da  suke hada game suna samun kudi ta hanyoyi da dama wanda suka hada game suna samun kudi ta hanyoyi da dama gasu kamar haka kuma zanyi bayaninsu wadanda aka fi sani da kuma samu ta su.

  • Saida copy ga duk wanda  zai buga a playstore
  • Saida coins da abubuwan da zasu taimaka wajen bude gidaje a ciki na wasa
  • Sanya talla a ciki ta kamfunna daban daban kamar su Google Admob da sauransu
  • Samun tallafi da gudummuwa saboda wadanda suka buga sunji dadi sai su bada inda za’a tura masu kudi.
  • Saida ta gabadaya ka manyan kamfunna kamar yadda Microsoft ya sayi wata game minecraft a $2 Billion Dollars.

Karanta:

Abubuwa 5 da suke sa dan koyon computer ya kware

yadda ake samun kudi online (Cikakken Bayani)

Ya Zan Fara

Yadda zaka fara shine sai ka yi programming languge wato yaren computer koda daya ne musamman ma wadanda aka fi sanin ana yin game da su.

fara kirkira game taka ta kanaka

Wasu daga cikin programming lnaguages da aka fi amfani da su wajen hada game sun hada da C# ko C-sharp, Python, Java, C++ da sauransu.

Kusam ma mafi yawancin programming languages din ana iya hada game da su indai akwai wani abu da ake kira da Game Engine.

Shi game Engine wata software ce da jata baka dsamar programming din game a cikin sauki kamar misali in ka bude wata gamer a android zakaga ansa Unity farko to da unity game engine aka yita shi kuma yana amfani da yaren C# ne.

Karanta: Koyon Programming na Computer cikakken bayani akan yaren computer

A ina zaka koya

Akwai wurwre da dama da zaka iya koyon abubuwa da yawa a wannan zamanin a yanar Gizo Internet, kodai ka karata ta hanyar shafukan sada zumunta, ko kuma shafukan yanar gizo  koma ta hanyar kallon Bidiyo a Kafar Youtube da sauransu.

Karanta: Yadda zaka habaka kanka ta fuskar karatu da bincike a koda yaushe ta hanyar amfani a yanar gizo

Ka duba post din sama da nayi kan yadda ake habbaka kai ta fuskar bincike da karatu, kai da ka kanaka indai ka rike Google da .sauran kafafe na tambaya forums in kana da ita lafiya lau inshallah.

In kuma kana maganar litattafai akwai su na saye dana kyauta duk kana iya download a internet, apps da sauransu, wanda ke da tambaya yana iya yi a comment section.