You are currently viewing Wasannin Kasar Hausa na gargajiya

Wasannin Kasar Hausa na gargajiya

Bahaushe kamar yadda sauran yaruka suke shima yana da aladun sa da yake yi wanda suka danganci wasa wanda ake cemasu da wasannin gargajiya, a lokacin kaka da kakanni ana yawan yinsu saboda a lokacin babu ciba na radio, TV da sauransu ba kamar yanzu da zamani ya canza ba.

wasanin gargajiya da ake yi a kasar hausa

Wasannin gargajiya suna taka muhimmiyar rawa sosai a lokacin da musamman a rayuwar yara saboda yanayin yadda shakuwa take tsakanin makwabci da makwabci a wancen lokacin to mafi yawancinsu yayan makwabta suke hadewa suna yi tare.

Abubuwan da Wasan Gargajiya na Hausawa suka Kunsa

Bahaushe ko kafin zuwan turawa ba’a bar shi a baya ba yana da al’adunsa kala daban daban wanda yake yi kuma ya rike su sosai daga cikinsu akwai fannin nishadantarwa wanda dama don haka ne ake yin wasa.

Karanta: TARIHIN BAYAJIDDA Tarihin Asalin Hausa Na Bayajidda Gamsashe

Wasannin gargajiya suna da matukar tasiri a rayuwar yara da manya saboda akwai fannin wasannin da yara kawai ke yi akwai kuma wanda har ma manya suna yinsa kamar dambe.

Wadannan wasannin ya danganta da yanayin lokaci akwai wadanda ake yinsu a kullum za’a iya yi akwai kuma wadand sai lokaci lokacin ko yanayi yanayi a duk shekara, akwai ma wadanda a’a ba kowa yake iya yinsu ba sai masu alka da abun kamar tauri da wasa da dabbobi kamar kura.

Wasu Daga Cikinsu

  • Yar gala-gala
  • Kwado
  • Dambe
  • Tauri
  • Wasa da kura

Yar gala-gala

Wannan wani nu’in wasa ne da yawanci mata suka fi yinsa wanda za’a samu kasa musamman a lokacin damina sai a yi zane a dage kafa ana ana tsalle.

Ana rike dutsi a tulla inda za’a isa kuma ba’a so mai wasan tana cikin yi ace an aje kafa a kasa ana so ya kasance an dage kafa a rika yin tsalle a sasannin gidajen da aka zana

Kwado

Kwado wani wasa ne wanda maza da mata suke yi amma yawanci mata sunfi yinsa, wasa ne mai nushadi wanda kusan a koda yaushe ana yin sa a zamani da.

Yadda yake shine ana amfani ne da duwatsu kanana ayi rami ko kuma a ja layi, mai buga wasan yana/tana jefa danda ytana jawo yaya tana tarawa ba’a so dan da ake tullawa ya fadi.

da ya faidi an rasa ko kuma daman in aka tulla an zawo yayan kuma ba’a son sun fito daga raminsu mutum ya fadi, to in dai hakan bai fari ba su fito ko diyar ta fadi sai mai yi ya cigaba da tara ya’ayansa a wajensa.

Dambe

wasan dambe wasa ne da ake yi tsakanin mutane guda biyu wanda daya zai yi kokari yaga ya kada dan uwansa domin ya samu kyauta mai tsoka.

Ana sa yashi a kasan wajen da masu dambatawar suke yadda zai bada kariya ga ,masu buga wasan baza su ji ciwo in sun fadi ba. Wannan dadeddan wasa ne wanda har yau ba’a bar yinsa ba a kasar hausawa.

Tauri

Wasan tauroi yana daya daga cikin wasanin da aake yinsu akasara hausa, yadda yake shine dan ana yinsa ne domin nishadantar da yan kallo, inda dan wasan zai sha ,maganin karfe ya rika kirari yana dadarawa aajikin sa inda zata ki kamasa ya yanaka wukar ko wani abu mai kaifi amma taki kamawa.

Wasa da Dabobi

Wannan ma yana daya daga cikin wasannan da muke da su na gargarjiya inda zaka ga mai wasa da dabba musamman a kasuwannin da suke ci sati-sati ko lokaci bayan lokaci.

Dabbobin da ake wasa da su a irin wannan nau’in wasan sun hada da kura, maciji, kada, biri da sauransu mafi yuawanci dai dabbobin daji ne ake yi da su.

Karanta: Tarihin Dr Sani Umar Rijiyar Lemu da Da’awarsa