Skip to content
Home » Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin

Yadda Ake Samun Aiki Online ta Hanyar Linkedin

Shin ko ka san cewa Kafar sada Zumunta ta Linkedin tana taimakama mutane da yawa suna samun ayyuka a kullun, hanaya ce wadda idan ka iya wani aiki zaka iya dogaro da kai da ita dudda ana ganin cewar kafar sada zumunta ce amma ba kamar sauran ba irinsu facebook, twitter da sauraqnsu domin it ba wasa ciki sosai.

Minene Linkedin

Linkedin dai daya daga cikin kafafen sada zumuntar zamani ne da muke da su kamar yadda a baya muka yi bayani akan kafafen sada zumunta da kuma bayaninta to itama tana daya daga cikinsu.

Kamar yadda idan ka lura dukkanin kowace kafar sada zumuntar zamani zaka fahimci cewar abunda take yima aiki ko abubuwan da suke son cimmawa su burin linkedin itace su hada alaka tsakanin masu neman aiki da kuma masu yin aiki na online wato freelancers tare dama wanda kamfanoni zasu dauka aikin dindin din.

Kamfunnan da dama suna zuwa wureren suna neman ma’aikata masu experience ko ilimin sanin abunda suke nema inda suke daukar haya su rika biya duk awa ko kuma su tsara yanayin lokacin aiki tare da lokacin biya wanda wasu kamfannan na kasasgen waje ne a dollars ake biyan mutum ya danganta da ya kamfanin ya daukai.

Nau’in Ayyukansu

Kamfunna a kafar suna daukar mutum cikin wadannan nauoin kamar gaka:

  • Remote Jobs
  • Partime Jobs
  • Inside Job
  • Parmanet Job

Abubuwan da ya Kunsa

Kafar Ta kunshi abubuwa da Yawa ta Kunshi abubuwa kamar haka

Kamfunna ko Masu Daukar Aiki

Daga cikin manya ko muhimman abubuwan da ta kunsa sune masu daukar aikin da kuma wadanda zasu dauka, masu dauka suna iya zama yanayin mutum guda yace zai dauki aiki ko kuma kamfunna su watsa cewa suna son wanda zai yi masu aiki kaza a lokaci kaza tare da bayanin yanayin aikin da kuma yadda ake son shi.

Wanda Suke Aikin

Wadanda ake dauka sune wanda suna da sani ko kuma kwarewa akan waata sana’ar hannu ko kuma aikin zasu kyara shafinsu na profile inda zasu rubuta abubuwan da suka iya yadda idan sun nemi aikin su masu nema zasu duba suga cancantarsu ko akasin haka shiyasa ake son mutumharma aikin da yayi a baya ya rika dorawa a sama.

Yadda Ake Samun Aiki

Bude wanna kafa bayada wuya zaka ziyarci shafinsu na likedin.com  ko kuma kayi download din app din su a play store a wannan link din kamar haka Linkedin app.

Daga nan saiu ka bude account ta hanyar yin registration sai kayi login ka cike bayanen abubuwan da ka iya ka ke iya yi idan an neme ka kayi aikin.

Karanta:

CIKAKKEN BAYANI AKAN SAMUN KUDI ONLINE TA FREELANCING

Yadda ake samu kudi ta Hanyar Referral Mobile App Referral Marketing

Hanyoyin Samun Kudi a Tiktok