You are currently viewing Forex Trade: Bayanin Forex Trade da Yadda ake yinsa

Forex Trade: Bayanin Forex Trade da Yadda ake yinsa

Forex Trade harka ce ko kuma ince nau’i ne na kasuwancin online wanda mutane da yawa suke samun kudi da shi ya kunshi canjin kudi na kasashe guda biyu, inda za’a iya saye kuma a saida, saboda mahimmancinsa ne muka ga ya kamata mu kawo ma ma’abota bibiyar shafin nan bayani game da shi da abunda ya kunsa.

Mi ake nufi da Forex Trade?

Idan aka ce Forex Trading ana nufin canjin kudi daga wannan na’uin kudi zuwa wannan, ma’ana shine canjin da ya ke zuwa na fannin kudi tsakanin kasashe guda biyu.

Dole idan zaka bar wata kasa ka tafi zuwa wata kasa kana bukatar ace ka canza kudinka misali daga Nigeri zaka je America dole sai ka canza Naira zuwa Dollar yadda idan kaje America zaka iya amfani da su.

Wanda shi aikinsa shine ya rika sayen kudi yana canzawa yana samun banbaci wanda shine a matsayin riba a online shi ake kira da Forext Trader wato mai yin kasuwancin forex.

Shi kuma yana saye ne daga wani wanda ake kira da broker shi zaya iya saida mashi yanki na kudaden kasa wanda bayan broker ya saida ma dan kasuwa zai rika lura da hawa ko saukar farashin kudin daya samu riba ya sayar.

Karanta:

Bayani akan Sana’ar Canjin Kudi

Bayani akan yadda zaka ga canjin kudi online

Hukuncinsa a Kasa da Mahangar Addini Take

A addinance forex kafin mutum ya fara shi akwai bukatar ya tsaya yayi karatun ta natsu indai har yana son ya samu kudin halal da shi saboda malamai da dama a duniya sun tofa albarkacin bakinsu akan halaccinsa ko haramcinsa.

Akwai fannin da suka ce halal ne wanda sun bada hujjarsu da dalilai gami da ayyukan da indai zakayi su ga abunda zakayi a cikin harkar ma’ana ga abunda yake halal ga kuma na haram.

hukuncin kasuwancin forex

To akwai banbancin maganganu na malamai da dama game da halaccinsa ko haramcinsa wanda idan ka duba shafukan internet zaka samu bayanai dayawa da suke magana akan hakan.

A dayen bangaren kuma idan akayi magana akan kasa ma’ana kundin tsarin mulki na kasa na Nigeria dama mafi yawancin kasashe na duniya yabada damar a yisa a saya a saida.

Abubuwan da Ake Bukata Wajen Farsa

Wannan kasuwancin ba sai mai kudi sosai ba ko karamin ko da kananan kudi kana iya farawa kamar da dala ashirin $20 ko abunda yayi sama shine a fannin jari kenan.

sai kasamu app na Broker idan a cikin waya zakayi kasuwancxin saboda a nan ne ake saye ake saidawa kuma ake ganin bayanai akan ya kasuwar take tafiya da sauransu.

Bayan nan demo trading ake farawa kada kace kai tsaye zaka fara shi a’a kana koyo kana zuwa demo trading accoung kana yi shi demo trdaing account broker ko appa na broker suna ba yankoyo damar koyo ne kafin su zuba kudinsu na gaskiya bayan kana iya kayi register ka cigaba.

Muhimman Abubuwan da Ya kunsa

wannan na’uin kasuwancin ya kunshi abubuwa da yawa amma ga wasu kadan da zan haskoma yadda zaka fahimceshi da kyau.

Koyonsa

Na farko dai dole ma sai ka koye sa don abu ne mai bukatar iulimi da kuma nazari sadoda yadda yake saurin canzawa da kuma hadari.

Dole kanemi ilimin kanana abubuwa kasansu kasan yanayin yadda ake cema kowane abu karami a ciki domin gudun matsala saboda kudinka ne zaka saka a ciki

Broker

Akwai abunda ake cema broker application ne ko kuma manahajar computer tunda muna maganar abun na online ta hanyar shi ne zaka sayi kudin kasar da kake sha’awar saya idan kuma ka tashi saidawa haka kuma kana iya saidawa batare da wata matsala ba.

Technical Analysis

Technical Analysis abu ne mai matukar amfani a fannin forex saboda dashi ne zaka fahimci kasuwa sama taka ma’ana ana cin riba ko faduwa ake.

Duk forex trader dole ne ya iya Analysis rashin wannan ilimin yana haifar da mummunar asara sanin sa kuma yana saurin sa mutum ya rika cin riba cikin karamin lokaci ya samu kudi masu yawa.

Saboda ya kunshi hasashen yadda kasuwar ke tafiya ne shin in chart ya kai wuri kaza akwai riba ko faduwa ce.

Currency

Idan akayi maganar currencyu ana nufin kudin kowace kasa akwai bukatar kasan alama ko yadda ake rubuta kudin kowace kasa domin haka ne zai baka damar gane mi zaka saya akan mi kuma.

Labarai da Kwarewa

Maai forex akwai bukatar ya rika bin llabarai da sauran bayanai na duniya musamman na fannin tattalin arziki, saboda abu kadan yana iya sa ka zama millionaire ko kuma ka kare cikin karamin lokaci

Karanta:

Samun kudi ta Zuba Hannun Jari

Yadda Zaka Samu Kudi a Wayarka ta Hanyar Zuba Hannun Jari a Kamfanoni

Muhimman Abubuwan da suke Taimakawa wajen samun Nasara a Kasuwanci

Matsalolinsa

Kamar kowane irin kasuwanci yana da riba yana kuma da faduwa shima haka forex yake kusan ma yana daga cikin nau’in kasuwancin dayafi saurin riba da saurin faduwa.

Shiyasa a farko ba’a zuba kudaden da ake so kai tsaye don gudun matsala kuma ba’a shiga batare dsa ilimi ko experience ba saboda yanxu mutum ya zuba yaga bai dawo da naira ba.