Akwai Ire-iren sana’oi da yawa wanda ake samun kudi da su na zamani ta hanyar amfani da wayar hannu, saboda idan ka/kika duba a wannan zamani da muke ciki mafi akasari muna amfani da manyan wayoyi ne irinsu android, iphone da sauransu wanda ya kamata ace suna taimaka mamu wajen habbaka kasuwaci ko kuma sana’a.
Bama kawai ace su taimaka wajen kasuwanci ba a’a har ma a samu damar yin sana’a dasu, a post na baya a wannan website munyi bayani akan kasuwanci guda goma da ake samun kudi da su, a yau inshallahu zamuyi dubi akan wanda za’a yi amfani da wayar tafi da gidanka.
Table of Contents
Abun Lura kafin Zaba
Sana’oin zamani wanda maza da mata suke sun banbanta da Sana’o’in Gargajiya na kasar hausa wanda hausawa suke akwai yan bambancebanbance amma dai na zamanin ga wasu daga abubuwan da zaka lura da su din
Na Daya
Kafin ka fara kowane irin kasuwanci ko kuma sana’a yana da kyau ka tsaya ka lura da yaya kake, ina nufin ya kake da lokaci da kuma karfin yinta.
Domin abunda yasa shine wani dalibi ne kuma ba kowane irin kasuwanci ne yake iyawa ba a dalilin karatusa amma akwai sana’aoi masu sauki ga dalibai wanda munyi magana a kansu a baya.
To yana da kyau ka/ki yi tunani da ya kake kafin fara wani kasuwancu domin gudun gazawa da kawo cikas a ciki.
Na Biyu
Sai kuma abu na biyu yana da kyau a da yanayin kudin jarin da shi kuma kasuwancin yake bukata, domin yadda zaka iya in kuma da bashi ne zaka fara to ba matsala amma sai dai ayi taka tsantsan.
ka tsaya ka shirya tsarin kasuwanci wanda ake cema lesson plan akan shi domin hakan zai taimaka maka wajen fahimtar shi.
Na Ukku
Abu na ukku kuma shine suwa kake tunani a matsayin masu sayen hajar, shin akwai bukatar ta a jaha ko kuma unguwar da kake.
Wannan nada matukar amfani domin hakan zai haskaka maka ko suwaye kake yin kasuwancin don su misalin haka shine baka zuwa wajen dalibai ka kama sana’ar saida gini domin ba shi suke soba na karatu suke bukata.
Sana’oin da zaka zaba
To bayan ka gama lura da matakan dana ambata a sama, ka zabi sai ka zabi wanda zai maka ga wasu daga ciki zamu lissafo su kamar haka.
Saro kaya waje online da saidawa
Ga masu binmu a wannan shafi na HAUSAWA SITE idan basu manta ba zasu san cewa a baya munyi magana akan yadda ake sawo kaya daga china suzo maka Nigeria.
To zaka iya amfani da wannan dama wajen kasuwancinka domin mutane dayawa musamman mata suna wannan harkar yanzun kuma suna samun kudi sosai.
Yadda suke abun shine zasu sayi kaya daga china a kawo masu nan sai su saida mafi yawanci ma a online suke saida kayan su hada group mutum ya biya in kaya sunzo su bashi kokuma lokacin da kaya suka zo su saida.
Wannan kasuwancin karkace na masu jari da yawa ne a’a masu karamin jari ma suke yinsa yan kaya kada yadda za’a kawo masu har post office ta garinsu.
Wannan kasuwancin da kudade kadan kana iya fara shi kuma ba tare da wata matsala ba inshallahu.
Karanta: Yadda ake sawo kaya daga chine suzo Nigeria
Abubuwa 5 da ake lura kafin sayen kaya online
Saida Data
Wannan kasuwancin na saida data wasu da yawa suna raina shi kuma ana samun kudi sosai dashi saboda ai kowa kafin ya hau internet yayi browsing kokuma wani chatting dole sai da data imma ta MTN, AIRTEL da sauransu.
Yadda ake fara wannan kasuwancin saboda shi yana da dan hadari musamman ga masu farawa don kar tayi expire suna samun wanda ya dade a cikin harkar ya dan rinka saida masu kadan da customer yazo su amshi lambarshi dsu tura mnashi shikuma ya turo masu kafin su tara customominsu.
Daga baya da sun samu nasu sai kawai su cigaba da saye da yawa wanda ahankali suna posting da kuma statusa a social medi sai kaga sun samu wani abu mai yawa.
Online Tutorial
Shikuma wannan shima wani launi ne na kasuwanci wanda ake cema kasuwancin online ko kuma Digital marketing, shi kuma zaka/ki yi amfani da ilimin da Allah ya baka/ki koyama wasu su baki wani dan tukuici.
Yadda ake yin wannan kasuwanci mafi akasari ana amfani ne da kafafen sada zumunta kamar su facebook, whatsapp da sauransu, inda ake hada group wanda yayi regfister zai shiga bayan ya biya kuda ya samu karatu a hotuna,. video da kuma PDFS.
Irin wannan kasuwancin a nan mata sun ma maza wayo saboda sunfi yinshi, kai hasali ma ko search na abubuwa masu amfani a google da hausa mata sunfi yi.
Saida Katin Waya
Wannan itama wata sana’a ce wadda ana samu da ita musamman idan aka san mutum kamar dai shigen yadda sana’ar data take.
Saboda samun cigaba na zamani yanzu mutum yana iya yin sana’ar saida kati kawai a tura mashi kudi shi kuma ya tura kati ta lambar da aka turo mashi cikin sauki.
Dudda dai ace saida katin waya ba shida riba sosai amma matukar kana da customi sosai to shikuma ba karamar riba kare shi ba, klawai dai hakuri yake so.
Saida haja Online
Saida kaya onlinea ahankali yana ta kara habbaka saboda kan mutane yanzu yana kara wayewa ba kamar da ba kowa tsoron tura kudi yake dudda wasu ma har yanzu haka suke.
Amma idan mutum yana sawo kaya irinsu shaddodi da takalma akan farashi mai sauki yana saidawa ba karamin samun kudi ake ba.
Yanzu ma kusan ga masu hawa facebook zasu lura da sun kara kawo marketplace wato inda zaka saida kayanka ga wayanda suke a online wanda wannan ba karamin cigaba bane, kuma shi kanshi kana iya habbaka hajarka a facebook ta hanyar talla a facebook din.
Kammalawa
kamar yadda muka ambata a sama ababen da suka gabata sune hanyoyi 5 daga cikin hanyoyin da ake samun kudi ta hanyar amfani da waya .
Me yakon mutum ya bata lokacinsa akan abubuwan da basu da amfani a waya kwara yayi masu amfani kodai ka yada abun alkahiri kokuma kasuwanci.
Karanta:
Yadda Zaka samu kudi da abubuwan da ka iya da Computer su zama Sana’arka da inda zaka koye su
Sanaoin Mata wanda zasu iya yi a Gida domin su samu kudi
A nan muka zo karshe a kasance da mu a WWW.HAUSAWASITE.COM.NG wanda keda wata tambaya ko kuma karin bayani yayi a comment kasa.
Author Profile
Latest entries
- UncategorizedAugust 16, 2024YADDA AKE HADA WEBSITE A KYAUTA DON BUNKASA KASUWANCI
- KasuwanciAugust 16, 2024Kasuwancin Saida Gidaje da yadda ake Samun Kudi da shi
- KasuwanciAugust 16, 2024kamfanin Biredi da yadda ake kasuwancinsa
- KasuwanciAugust 16, 2024Bayani akan Bude Kamfani domin dogaro da kai