Skip to content
Home » Blog da Abubuwan da ya Kunsa

Blog da Abubuwan da ya Kunsa

A cikin wannan post din zamuyi bayani ne akan blog abubuwan da ya kunsa da kuma ma’anarsa hadi da yanayin yadda ya kasu wanda idan mai karatu ya natsu zai gane inshallahu.

Mi ake nufi da Blog?

Idan akayi magana akan blog ana nufin shafin da mutum zai kirkira wanda yana yawan dora mashi abubuwa yadda mutane zasu rika shiga suna amfana.

A cigaba da aka samu na internet akwai skhafuka kala kala na website wanda zaka iya gani wanda yana daya daga cikinsu kuma wadannan shafukan suna da rawar da suke takawa kala daban daban a yanar gizo.

Abunda blog yake nufi da kuma abubuwan da ya kunsa

To shi kamar shafi ne wanda zaka iya yada abubuwan da kake so a internet wato website a saukake.

Muna da website kala kala wadanda suka kunshi irinsu shafukan labarai, wajen tattauna batutuwa, na saide saide, shafukan ayyuka da sauransu.

Karanta: Fahimtar yadda shafukan yanar gizo suke aiki kafin ka koyi bude su

kala kalar shi

A da kafin a samu cigaba kafin ka mallaki wani shafi na website ko kuma blog sai ka sha wahalar programming ko kuma dole sai ka kira wanda zai hada maka wannan shafin da kake so.

To kaga idan bakada kudi ko kuma baka da ilimin programming akwai matsala kenan amman yanzu zuwan cigaban internet cikin ikon Allah kana iya hada naka ta hanyar irin waddannan manhajojin,

  • Blogger
  • WordPress
  • Joomla
  • Drupal
  • Wix da sauransu

Tundaka gansu a lissafe bari in yi bayanin wadansun sdaga cikin su wadanda suka fi amfani kuma aka fi yin amfani da su a fadin duniya kabakidaya.

Blogger

Wannan manhaja ta blogger tana daya daga cikin manhajojin da kamfanin Google yake kula da su wannda ake hada shafukan yanar gizo da da su.

Mutane da dama suna amfani da ita kuma tana da saukin fahimta da gudanar da ayyuka musamman ga yan koyo kana iya duba bayanin da nayi a baya kan yadda ake bude ta

Karanta : Rubuta Post: Yadda ake Rubuta Post a Website din Blogger

Kana iya daura abubuwa a cikinta da yawa wanda suka hada da hotuna, bidiyoyi da sauransu kuma tana da templates da themes wanda zaka iya canzawa a koda yaushe kake so.

WordPress

bayani akan wordpress

WordPress tana daya daga cikinsu wadda ita tafi yawan jan hankalin mutanen duniya saboda ita kusan kashi 80% a cikin dari na masu website suna amfani ne da wordpress.

Kana iya dora hotuna, bidiyo da sauran abubuwa da dama fiye da wadda mukayi bayani a sama.

WordPress ta rabu zuwa gida biyu akwai wordpress.com ta kyauta wadda zaka iya bude account a cikinta amma baka samun sauran damar abubuwa kamar domain yadda kake so sai ka biya kudi.

Sai kuma ta b iyu akwai wordpress.org ita kuma self hosted ce wato zaka dora ta a hosting bayan ka hada ta da domain sai ka cigaba da amfani da ita.

Inshallahu zamu yi bayanai akan wasu abubuwan da na ambata a sama nan gaba kada a cigaba da kasancewa da mu a Hausawasite.com.ng a koda yausshe.

Idan kana da tambaya kayi a kasa akwa wurin commen.