You are currently viewing Sana’oin Zamani 10 Masu Saukin Yi ga Mazauna Kauye ko Karkara

Sana’oin Zamani 10 Masu Saukin Yi ga Mazauna Kauye ko Karkara

kananun sana'oin ga yan kauye

Ga wadanda suke zaune kauye yanayin kasuwancin su da kuma sana’oin da suke yi yana bambamta da birni ko kuma babban gari. saboda yanayin yadda mutane suke zaune a wadannan wuraren basu da yawa kuma yawancinsu ba yan boko bane sosai amma suna bukatar abubuwa kamar kowa.

A wannan post din na yau zamuyi dubi akan wasu muhimman sana’oin da ya kamata wanda yake zaune a irin wadannan wuraren su rika yinsu.

Wace Sana’oin Zamani Tafi Kamatar Kauye ko Karkara?

Akwai sana’oi da dama da ya kamace su, duk da dai su yawancinsu sunfi sabawa dana gargajiya to kai idan ka fahimci yanayin abubuwan zamani kuma kana cikinsu zaka samu kudi sosai, saboda suna bukatar abun ko kuma yaran su wayayyi wadanda suke son wani abun misali katin kira na gyaran abunda ya shafi waya.#

San a’oin da suke na zamani an fi samu da su saboda ba kowane a cikinsu yake da fahimtar su ba sai masu ilimi daga cikinsu don haka ga wasu guda goma wanda suke da amfani ake samun kudi da su ga wadanda suke zaune karkara.

Lissafinsu

  1. Saida Data da Kati
  2. Verselene
  3. Sabulu
  4. Gyaran waya
  5. Saida Layi da Yin rigistersa
  6. Abubuwan Computer
  7. Hoto
  8. Kahinta
  9. Tela
  10. Sana’ar Cajin Waya