Skip to content
Home » YADDA AKE GURASA

YADDA AKE GURASA

Gurasa  dai na daya daga cikin abinci da jinsin mutane da dama keyi saboda dadin ta da kuma  karbuwa datai ga mutane.

Kuma gurasa wani abincine wanda ake yinshi da fulawa kuma Kuma yana daukar mahadi dayawa misali: gurasa da kuli, suga, miya da sauransu.

Yau zamu koyi yadda ake gurasa kala biyu wadan da sune;

Kalolin:

1) gurasa zalla

2) gurasa da miyar anta

                                *

Yadda ake gurasa zalla

Idan za’ayi gurasa zalla ana bukatar kayan hadi kamar haka;

Kayan hadin:

  • Fulawa
  • Yis
  • Gishiri
  • Ruwa
Yadda ake hadawa

Zaki samu wurin ki mai yalwa na kwabi sai ki zuba fulawa, yis da gishiri aciki ki motsa, sannan kisa ruwa ki kwaba sosai, amma kar kisa ruwa dayawa  kiyi kamar kwabin fanke amma yafishi tauri.

Bayan kin gama sai ki rinka yago kwabin kina dan budawa kina sawa a tandenun gurasa, idan kuma oven ne sai ki jajjerashi acikin tire kisa ki rufe ki kunna wuta kadan kibarta taita gasuwa har takai yadda kike bukata sai ki kwashe.

                                *

Yadda ake gurasa da miyar anta

Uwargida kijaraba wannan girki kar kibari abaroki a baya dominko yanada dadi sosai musanman ma idan kika inganta girka miyarki.

Abubuwan da ake bukata sune;

Kayan hadin:

  • Fulawa
  • Nama
  • Anta
  • Magi/gishiri
  • Mai
  • Attarugu/albasa
  • Yis
  • Ruwa
  • Man ja
  • Kori/tayim
Yadda ake hadawa

Dafarko zaki wanke antarki  da nama ki tafasasu tare idan suka tafasa sai ki saukesu ki soyasu ki juye a gefe.

Sai kizo ki dauko fulawarki kisa mata yis da gishiri kadan sai ki sa ruwa ki kwaba kamar kwabin fanke amma yafishi tauri sai ki kaita a rana ta tashi, idan ta taso sai ki dauko frenfan dinki ki azashi a wuta kisa mai kadan kamar cokali daya sai ki dauko kwabin nan naki ki zuba kisa hannu ki bar bajeshi yayi fadi idan kasan yasoyu sai ki juya haka zaki tayi har kigama.

Bayan kin gama sai ki daura tukunyarki kisa mai, manja da albasa idan yasoyu sai kisa jajjagenki na tarugu sannan kisa magi, gishiri, kori, tayim da albasa kibarshi yasoyu har sai kinga mai yataso sama sai ki dauko nama da antarki dakika sulala ki zuba kimotse, sannan kikawo ruwan dakika tafasa naman ki ki zuba kadan ki kulle, sai ki bata tsawon minti shabiyar tadahu.