You are currently viewing Minene Abun zûmin(microscope)

Minene Abun zûmin(microscope)

Ayau zamuso sanin minene ake nufi da abun zumin(microscope), Wanda yahada da sanin  anfaninsa dakuma matakanda akebi domin anfani dashi.

To ayanzu kuma zamu shiga acikin darasin Wanda zamu fara sanin mi ake nufi da abun zumin?.

Mi ake nufi da abun zûmin(microscope)

BAYANI: abun zumin(microscope) wani abun anfanine wanda ake anfana dashi acikin laf(laboratory) domin duba kananun halittunda  baza’a iya ganinsu da ido ba. Halittun da suka kasance baza’a iya ganinsu da ido ba seta hangar  abun zumin to wadannan halittu ana kiransu da halittun abun zumin(microscopic organisms).

Idan aka duba mafi karancin halitta acikin halittu ta hanyar anfani da abun zumin, to za’a ga wannan halittar aciki ta kara girma Wanda har ana ganin dukkan tsarin halittarta kwaro-kwaro. Karantar abun zumin dakuma anfani dashi yana bamu dama wajen lura dakuma tantance yadda tsarin jikin kananun halittu yake.

Ire-iren abun zûmin

Akwai ire-iren abun zumin da dama Wa’yanda sune:

  • Fili abun zumin(compound microscope)
  • Haske abun zumin(light microscope)
  • Hannun gilas abun zumin(hand lens microscope)

Sashunan abun zûmin(microscope)

Abun zumin an hadashine da sashuna da dama, Wanda kowane sashe yake kunshe da anfaninsa, wadannan sashuna sune:

1. Tushe (the base)

2. Mataki (the stage)

3. Madubin sama (The plane mirror)

4. Mariki (handle)

5. (clips)

6. (condenser)

7. Abun madubi (the object lens)

8. Yankin madubin ido (the eye piece lenses)

9. Yankin juyawa (the rotary nasal piece)

Bayani akan sashunan