Skip to content
Home » Abunda mutanen yanzu basu sani ba game da Buhari

Abunda mutanen yanzu basu sani ba game da Buhari

    

    Kamar yadda yawancin yan Nigeria suka sani shugaba Muhammadu Buhari ya nemi takarar mulkin Nigeria abaya wanda za’a ce kusan ba sau daya ba ba sau biyu ba indi jam’iyar (PDP) wanda take mulki a Nigeria tun a shekarar 1999 take kada shi amma duk da hakan bai sa shi ya kare ba wajen neman mulki a inda a shekarar 2015 Allah ya bashi nasarar hambarar da jam’iyyar (PDP) wadda take mulki a kasar.


      Shidai tsohon shugaban kasar Nigeria ne wanda ya mulki kasar tun lokacin mulkin soja wanda yake da shekara 76, inda yawancin yan Nigeria ke ganin sa a matsayin mai gaskiya wanda yake tsayayye .


     A shekarar 2015 ya sami hadin kai tare da kungiyar APC inda suka hada da niyyar kawo yan Nigeria canji wanda hakan ya kara ma jam’iyyar karfi da kuma kima a idanun yan Nigeria inda bayan an gama zaben ya samu nasarar kada shugaban da ke mulki a kasar wato Goodluck Jonathan.


 Na daka cikin abubuwan da yan Nigeria suka sa rai dama shi abun da shugaba muhammadu Buhari yayi koarin yi a lokacin mulkinsa da kuma abubuwan da suka faru  da shugaban  tun kafin  ya hau mulkin kasar har zuwa yau.
Al’amarin Rashin Lafiya na 2017.

     A lokacin da ya hau mulkin kasar Nigeria a shekarar 2017 ya samu rashin lafiya wadda ta jawo magan ganu a bakunan yan Nigeria.
     Ya dai yi jinyarsa ne a kasar ingila inda ya shafe kusan kwanaki 100 inda bayan ya gama wadannan kwanakin ne ya dawo gida a Nigeria ya cigaba da harkokin mulki.
Al’ amarin da ya faru na  yunkurin kisa

An kai farmaki ma shugaba muhammadu Buhari a  lokacin da suke wata tafiya da shi da jerin motocin da su ke raka shi a birnin kaduna inda, ba’a san ko suwa ne ne suka kai harin ba.e
 Amma a lokacin kasar Nigeria tana fama da hare haren wannan kungiyar mai suna Boko Haram, kafin shugaba Buhari ya hau mulkin kasar ya sha alwashin cewa zai yi iya kokarinshi na ganin ya kawo zaman lafiya a Nigeria.
   inda bayan ya hau masana dama sauran yan Nigeria sun jin jina mai kame da kokarin da yayi bayan hawan sa mulkin kasar kame da harkar tsaro musamman ma rikicin Boko Haram wanda ya addabi kasar a baya.
Sa rai da yan Nigeria sukai wajen samun sauyi.

      Yan kasar Nigeria  musanmanma talakawa a lokacin da shugaba muhammadu buhari ya hau a mulkin kasara Nigeria a shekarar 2015 sun sa ran samun chanji na harkokin kasar kamar su samun tsaro a kasar, yaki da cin hanci da rashawa ,da ma sauransu.
    
     Amman daga cikin wasu masu sharhi na kasar Nigeria suke ganin wai cewar ba wani abun da aka samu da tattalin arziki da abubuwan cigaba.
     Amma fa wasu daga cikin su sun jinjina ma shugaban ta fuskar tsaro musan man ma wannan rikin wanda ya dabaibaye kasa watau Boko Haram inda suke cewar ya taka rawar gani.
        
Yakin da shugaban yayi akan rashin da’a

      Shugaba Buhari yayi alkawarin gyara wasu daga banna da ta awku a Nigeria inda bayan da ya hau Mulkin kasar a wata zantawar da akai da shi ya ce bannar da akai a tsawon shekaru 16 tayi yawa kuma zasuyi kokarin rage tamusan man ma a fanin cin hanci da rashawa.
  To anan ya rage ma jama’a ga zaben 2019 nan yana zuwa kuma shugaba Buhari ya kara fitowa don koma wa wa’adin mulki akaro na Biyu to kowa  zai ci zabe tsakanin attiku da Buhari, idan akwai comment yi shi a comment section don muji ta bakin ka mai karatu.