Uwargida dafarkode zaki tanadi kayan hadinki kamar haka:
Table of Contents
Kayan Hadin
- koda
- Koren tattasai
- Jan tattasai
- Manja
- Albasa
- Tarugu
- Gishiri
- Citta
- Karas
- Bell pepper
- Scotch bonet pepper
Yadda ake hadawa
Da farko dai zaki fara yin miyarki ki tabbata ta zama ready.
Shine idan kika kunna wuta sai ki fara zuba man ja a cikin kasko ko tukunya ba tare da albasa ba.
Daga nan sai ki zuba kodar ki yadda kike so yadan fara dahuwa, haka kamar tsawon minti ukku.
Sannan sai ki zuba karas, tattasai, albasa da citta ki motsa sannan kizuba Kayan kanshi ki rufeshi akalla tsawon minti uku tadahu kenan.

To yanxu kinkammala miya saura kuma moimoi (alala)
Yadda akeyi
Zaki sirfa wakenki sannan kiwankeshi yafita sosai , wato kifidda duk wannan dusar dake jikinsa.
Saiki zubashi a blender tare da albasa dakuma attarugu kimarkada.
Sannan kijuyeshi ki zuba manja, scotch bonnet pepper, da gishiri ki zuba aciki kimotsa.
Sai ki kukkulla aleda gwargwadon yadda kike bukata.
Zaki zuba ruwan zafi a tukunya yatafasa sannan ki zuba kullallar alalarki aciki ki kulleshi kamar tsawon minti ashirin ko talatin yadahu.
Author Profile
- IBRAHIM BUHARI Shahararren marubuci ne game da sana'oi, Digital Skills da sauransu shine kuma shugaban kamfanin HS Global Wato Shugaba a Wannan Website ta Hausawa Site
Latest entries
KasuwanciOctober 23, 2025Lambar TIN a Nigeria: Ma’ana, Amfani da Yadda Ake Mallakar ta
Kiwon LafiyaOctober 22, 2025Zogale: Sinadaran Sa da Amfanin Sa ga Lafiyar Jiki
Kiwon LafiyaOctober 21, 2025ZUMA: Amfanin Ta, Hanyoyin Samar Da Ita, Da Muhimmancin Ta Ga Lafiya
Kiwon LafiyaOctober 20, 2025Maganin Karfin Maza: Hanyoyin Gargajiya na Kara Kuzarin Maza





