Yadda Ake Tura Sakon Email a cikin waya

Yadda Ake Tura Sakon Email a cikin waya

Assalamu alaikum To shidai Email kamar yadda kowa ya sani ana amfani da shi ne don a tura sako ko Kuma a amshi sako daga wani zuwa wami ta hanyar address, kar a manta kana tare da website din Hausawasite.com.ng.
     

Yadda Ake tura Sakon email address

     Kuma a zamanin yanxu mafi yawanci ana bukatar a sa Email wajen registration ne Koko wajen harkokin kasuwanci daban daban to a dalilin haka Yana da matukar amfani mutum ya San yadda zai iya tura Email address.

   Kafin ka tura Email address akwai bukatar ya kasance ka Bude Email address Dinka domin da shi ne zakai amfani ka tura ma wani, idan baa manta ba a baya mun koya yadda Ake Bude Email address inda mukai bayani sosai akan hakan ta hanyar kawo matakai da Kuma hotuna wanada suke koya hakan.

   To bayan ka bude sai ka je kayi install din wani application Wanda Ake cema Gmail inda idan ka dauko shi zaka Yi login din Email address din ka a cikin wayarka. Shima mun Yi bayanin a baya  kan yadda Ake login Email address a waya, yanzu zamu tai matakan rubuta Email din.

kar a manta ana tare da website din Hausawasite.com.ng ne wanda ta Al’ummar Hausa ce inda ake koyon abubuwa daban daban daga masana da dama a cikin harshen hausa musamman sana’oi don dogaro da kai  Domin kasancewa damu kana iya Rubuta Hausawa SIte a Google don samun sabbin rubuce – rubucenmu

Matakan da zaka bi don rubuta Email address Wanda Ake turawa zuwa wani

Mataki na farko ka je a playstore kayi download din Gmail app said kayi install din sa.

Yadda Ake install email app daga playstore

Ka bude app din Gmail din sai ka Danna wajen alamar alkalami a gefen damar ka a kasa Yana da jar kala sai ka latsa shi.

Zai bude maka waje kamar haka.

Rubutun Sakon email
To bayan ka Danna wajen zaka ga an bude maka wajen da zaka rubuta kungin Email din wato inda zaka rubuta Wanda zaka turamawa inda aka sa To  
Rubutun Email address
Daga nan Kuma sai ka je inda aka sa subject ka rubuta taken email address din bayan ka Yi haka sai ka je wajen compose Email ka rubuta duk abunda zaka rubuta in ka gama sai ka Danna kibiya daga dmsama shine wajen send.

Abubuwan da zaka iya aikawa ta hanyar sakon Email

  1. Rubutu
  2. Hotuna
  3. Bodiyoyi
  4. Litattafan PDF 
Da sauran filoli daban daban/ dan duka kana iya turawa. ta sakon imel.

Idan sakon ya jema wancen kawai abunda  zaiyi shin e ya sauke file din acikin wayarsa ko komputer zai sameshi

Kammalawa

Kamar dai yadda Mai karatu ya karanta mun Yi bayani gamsashe kan yadda Ake tura Sakon email address daga wani zuwa wani, idan akwai Wanda yake bukatar Karin bayani Yana iya comment a kasa muna fata zaa cigaba da kasancewa da wannan website ta Hausawasite.com.ng mungode.

This Post Has One Comment

  1. AKUSHI TV

    Allah ya kara basira, to amma tamayata anan itace, me ake bufi Taken email address sai najiku
    mungode

Comments are closed.