Skip to content
Home » Yadda Ake Man Kwakwa(Coconut Oil)

Yadda Ake Man Kwakwa(Coconut Oil)

COCONUT OIL (MAN KWA-KWA)

Dafarko zaka samu kwakwa kamar wadda tafara lalacewa saboda tafi fidda mai sosai sai ka bare bawon a yanyankata ayi blending dinti sosai sai a taceta a fidda dissar

sai azuba ruwa a da aka tace cikin wata roba haka mai murfi sai a sa fridge idan yayi sanyi sosai zaka ga ruwan yayi kasa man kuma yayi sama sai ka kwashe man, idan kagama sai ka sai kazuba shi a tukunya kadan soyashi kamar 15 minutes sauran ruwan dake jikin shi zaya kone sai a sauke idan ya huce sai a zuba a container.

Amfanin Man Kwakwa

Man Kwakwa yana da amfani sosai a jikin mutum musamman ma a fannin gashi shiyasa ake yawan amfani dashi a man kitso.

Daga cikin manyan manyan amfaninsa sun kunshi

  • Yana kara sa gashi yayi sulbi
  • Yana sa kaurin gashi
  • Yana taimakawa gashi yazama yana da sulbi da damshi
  • Yana hana fata saurin bushe
  • Yana taimakawa wajen kara lafiyar zuciya
  • Yana taimawa wajen gyaran baki da kare cututtukan dasuka shafi baki

Kammalawa

Kamar yadda muka koya hada man kwakwa kana iya daukar shi a matsayin hanyar samun kuɗi babba wanda ana yawan bukatar shi.

Saboda ko masu hada irinsu sabulu man kitso da sauran su suna son su sashi.