You are currently viewing Girkin Kifi: Yadda ake sarrafa kifi Hanyoyi da Dama

Girkin Kifi: Yadda ake sarrafa kifi Hanyoyi da Dama

To shide kifi wani dabba ne Wanda ake samunshi cikin ruwa Wanda yakasance kala daban- daban a duniya misali: cat fish (kifin Hausa), Titus da sauransu.

To ayau zamu koya maku yadda zaku sarrafa kifi ta hanya daban-daban domin samun dandano kala-kala masu dadi kuma ba tare da ansha wahalaba.

Hanyoyin da zamu koya

1) Dafuwa

2) Gashi

3) Soye

4) Dambu

Yadda ake dafaffen kifi (farfesu)

Idan zaki farfesun cat fish (kifi Hausa); ana bukatar ki tanadi Kayan hadi kamar haka:

Kayan hadi

 

 • Cat fish
 • Mai
 • Thyme
 • Rosemary
 • Citta/tafarnuwa
 • Albasa
 • Tattasai
 • Ruwa
 • Gishiri
 • Seasoning
 • Ganyen ugu
 • Spices

Yadda ake hadawa

Dafarko zaki fara yanka kifin ta kwance sannan kidafa ruwan zafi ki zuba mashi sai ki wanke yadda zai fita sosai.

Sannan ki daura tukunya ki zuba mai, thyme, rosemary, citta da tafarnuwa kimotsa.

sai kuma ki zuba kifin aciki ki motsa wato kidan soyashi na yan sakanni.

Sai ki kawo spices dinki ki zuba Kalan Wanda kike so sai kuma albasa da tattasai kidan juyashi sai ki rufe kamar minti biyar.

Sannan sai ki bude ki zuba ruwan zafi amma ruwan ba dayawa ba sosai sai kuma ki zuba gishiri da seasoning sannan ki kulleshi yada hu tsawon minti ashirin da biyar.

Bayan yadahu sai ki yaryada ganyen ugu Kadan aciki.

Yadda ake gasashshen kifi

Kayan da ake bukata ki tanada sune:

Kayan hadi

 • Cumin
 • Coriander
 • Fish masala
 • Paprika
 • Citta/tafarnuwa
 • Onion powder
 • Black pepper
 • Curry/thyme
 • White pepper
 • Mai
 • Seasoning
 • Lemun tsami

Yadda ake hadawa

Dafarko zaki fara tsaga saman kifin dawuka kamar tsaga uku ko hudu sannan shima tsakiya ki tsagashi kifidda duk wani dattin da Ke ciki sai ki wanke shi yafi ta Sosa.

Sannan sai ki kawo kayan hadinki duka wadanda muka lissafa ki cakudesu wuri daya ki matsa mai da lemun tsami ki motsa.

sai ki samu wuri mai yalwa ki shafe kifinki tas da wannan hadin tun daga ciki har waje. Sai kisanyashi cikin oven yagasu.

To idan kingama zaki iya cinshi da miyar source ko kuma da abunda kike ra’ayi.

karanta:

Yadda ake wainar alkama

Yadda ake ice-cream na kwakwa

Yadda ake soyayyen kifi

Yadda ake soya cat fish (kifin Hausa) shine zaki tanadi kayan hadi kamar haka:

Kayan hadi

 • Cat fish (kifin Hausa)
 • Albasa
 • Lemun tsami
 • Citta/tafarnuwa
 • Onion powder
 • Cumin
 • Seasoning
 • Back pepper
 • Curry/thyme
 • Clove powder

Yadda ake hadawa

To kunsan shi kifin Hausa idan aka wanke shi sosai yafi dadi.

wajen wanke kifin zaki fara dafa ruwan zafi sai ki yanka kifin ta kwance sana ki kwaranya mashi wannan ruwan zafin ki wanke shi dashi yadda zai fidda duk wani dattin dake jikinshi.

sannan sai ki juyeshi a wada taccen wuri ki zuba mashi duk wadannan spices din da muka lissafa tare da lemun tsami ki motsa sosai.

Sannan sai ki kulleshi ya dan gumu na minti biyar.

bayan ya gumu sana kisoya mai tareda albasa, sai ki zuba kifin aciki kina juyawa gefe-gefe harya soyu baki daya.

To shide soyayyen kifi zaki iya cinshi da tashshi ko kuma gishiri idan kina bukata.

 

Yadda ake dambun kifi

Ana bukatar ki tanadi kayan hadi kamar haka:

Kayan hadi

 • Kifi
 • Albasa
 • Seasoning
 • Black pepper
 • Citta/tafarnuwa
 • Ruwa
 • Mai
 • Markadadden cefane (mekauri)
 • Curry/thyme

Karanata:

Karin Ni’ima ga Mata: Abincin da Ke Karin Ni’ima ga Mata

Karin Kiba: Kunun Karin Kiba na Sabaya da Yadda Ake Yinsa

Yadda ake hadawa

Dafarko de zaki fara yanka kifin kana ki wanke shi yafi ta sosai.

Sai ki sa shi a tukunya ki zuba mashi albasa, seasoning, citta, black pepper dakuma ruwa kadan ki kulleshi ya sulala.

Bayan ya gama sai ki tsame shi cikin wuri ki fidda mashi duk kayar dake cikin shi, sai ki rarrabashi kananu sannan ki maidashi a tukunya kokuma kasko ki mammotsa shi ba tare da kinsa mashi komi ba na tsawon minti 5.

Sannan sai ki zuba mashi mai Kadan, markadadden cefane, curry dakuma thyme kicigaba da juyawa kina Dan tabawa.

Toh idan kika ji yayi waras-waras baya kama hannu alamar yasoyu kenan, saiki juye.