Skip to content
Home » Karin Ni’ima ga Mata: Abincin da Ke Karin Ni’ima ga Mata

Karin Ni’ima ga Mata: Abincin da Ke Karin Ni’ima ga Mata

Karin ni;ma abu ne wadda kowace mace yakamata ta kula ta hanyar cin abinci ko kuma kula da wasu dabi’u wanda zai taimaka mata wajen inganta lafiyar jikinta. saboda yadda mata jikinsu yake saurin canzawa ba kamar maza ba.

A cikin wannan post din inshallahu zamuyi magana akan wasu muhimman nau.in abincion da ya kamata ta kula wanda zasu taimaka mata wajen samun ni’ima ko da ma inganta lafiyarta tare da abubuwan da da zata kula ko kuma yawan amfanin da su yau da kullun.

Abubuwan da ke Kara ma Mace Ni’ima

Kamar dai yadda na fadi a baya zamuyi kasa abun kusan fanoni inda ya kunshi fannin abinci, sai kuma fannin abubuwan hade hade na magunguna ko abunda zata rika sha sai kuma fannin halaye ma’ana abunda zata rika yi ko kuma ta kula da kanata domin kariya ko inganta lafiyar jikinta.

Fannin Abinci

Duk macen da ke son samun ni’ima to cin abinci mai gina jiki yana taimakawa kuma shine jigon tafiyar saboda sai jikin yana samun sinadarai da yake bukata wanda zai dan taimaka wajen sa ta kiba.

Cin abubuwa kamar masu protein kamara su wake, kwai, madara da sauransu yana taimaka ma mata sosai kuma kar ki ce baki da kudi a sai mai kudi aa a karamin abinci ma kamar su awara suna taimakawa saboda suna da waken suya a cikin su wanda protein ne shima.

To shiyasa a kowane hali kar ki bari kina takura kanki kina zama da yunwa matsala ce ga lafiyar jikinki sosai.

sai kuma wannin abun kulawa shin cin abinci safe da wuri wanda yake taimakama jikin dan adam duka namiji ne ko kuma mace yana inganta lafiya kuma masana nacewa masu kula da kalaci suna yinsa da wuri sun fi yawancin rayuwa ko kuma lafiya fiye da wadanda sai sun dade suke karyawa.

Amma a lokacin dare ba’a son ana cin abinci da yawa saboda illa yake ja a jikin mutum wani ma idan ya cika cikinsa ya kwanta cikin har baci yake to ana son cin abu marara nauyi a lokacin dare da safe a kalaci kuma mai nauyi mai sinadarai.

Karanta:Karin Kiba: Kunun Karin Kiba na Sabaya da Yadda Ake Yinsa

Fannin Magani

A fannin magani kuma akwaia abubuwan da suke gyara jiki na mace sosai su sa shi yayi kyau yayi sulbi kuma ya kara ni’ima a jikinta saboda wanda suka kunshi irin gGanyen gwanda, Lalle, Ganyen magarya da kuma irin Hulba.

Wadannan abubuwa ne da suke sa jikin ta yayi sheki yayi kyau sosai ya kuma kara mata lafiyar jiki musamman hulba duk macen da take son ta tsufa amma da kyan jikinta ko kuma nonon ta bai zube ba irin sosai dinnan alhali ba tsufa tayi ba to ta riki hulba.

Hulba abu ce wadda take inganta lafiyar mata kuma take kara masu ni’ma.

Lalle kuwa daman yana taimakawa wajen gyaran jiki da kuma tsotse cututtuka da ke addabar jikin idan mace na yawan amfani da shi tayi kunshi to yana taimakawa sosai kamar yadda mukayi bayanin Amfanin lalle guda biyar (5) ga Mata a post dinmu na da.

Sai kuma ganyen magarya wanda shima abune mai gayara fatar jikin mata sosai tare da taimakawa wajen inganta lafiyar jikinsu

Karanta:

Gyaran Gashi: Yadda ake wanke gashi da lalle ga mata

Magunguna 5 da ya Kamata su Kasance Tare da Kai a Kullun

Fannin Halaye

Daga nan kuma sai dayan fannin da nike son inyi bayani a kanshi wanda shine mu’amala ko halayenm da mace yakamata kula domin samun ni’ima a jikinta.

Daga cikinsu akwai kulawa da amfani da ruwan dumi a wajen tsarki. ana son mace ta kula da amfani da ruwan duma a wajen tsarki hakan yana taimaka mata wajen magance cututtukan kafin su kai ga wurin.

Saboda su bacteria idan ruwan sanyi ne sunfi saurin shiga wanda suna iya haifar mata da infection amma ruwan dumi cikin ikon Allah yana taimakwa wajen bata kariya.

daga nan kuma kuma sai kaucema yawan tashin hankali da kuma yin fara’a ga mutane hakan yana taimakama jikin dan adam sosai kuma yana kara lafiya kamar yadda masana suka tabbatar bama ga mata ba kawai har ma da mazan ana son mutum ya rika sakin fuska kamar yadda masana suka ce irin mutane masu fara’a sun fi tsawon rai.

Karanta: 

Amfanin Zuma 10 ga Jikin dan Adam

 Amfanin Ruwa Dumi 5 ga Lafiyar Jiki

Hanyoyin da ake bi Wajen Magance Cutar Diebities ciwon suga